Abu 7 da bincike ya gano kan mutuwar matasa 33 masu haƙar zinare a Neja

Asalin hoton, Bago/X
Wani bincike da aka gudanar kan mutuwar mutane 33 da ake tsare da su a jihar Neja da ke Najeriya ya gano cewa sun mutu ne a wani abin da kwamitin binciken ya bayyana a matsayin mummunan yanayin cunkoson da za a iya kauce wa.
Kwamitin ya ce yanayin wanda ya samo asali daga cunkoson da ya yi tsanani a wajen tsarewar ya janyo rashin isasshiyar iska da kuma gazawar jami'ai wajen amsa ƙorafe-ƙorafen neman agaji da aka yi ta yi.
Shugaban kwamitin binciken ya ce shaidun da suka tattara daga binciken gawarwaki da na likitoci sun nuna cewa mutuwar ta samo asali ne daga matsananciyar matsalar numfashi sakamakon tsarewa ta dogon lokaci a wuri mara kyau, lamarin da zafin jiki mai tsanani da rashin ruwa a jiki suka ƙara munin al'amarin.
Ga jerin abubuwa 7 da binciken ya gano makwanni fiye da biyar bayan faruwar al'amarin.
Abubuwa 7 da binciken ya gano
- Shaidun da aka samu ba su goyi bayan ikirarin cewa mutuwar ta samo asali ne daga wata annoba ko barkewar cuta ba.
- An tsare maza 50 a cikin ɗaki guda mai faɗin kusan murabba'i mita 20, ba tare da ruwan famfo mai gudana ko bayan gida mai aiki ba, sannan kuma abinci, ruwan sha da iskar da ake buƙata ba su wadatar ba.
- An tsare manya da ƙananan yara a wuri ɗaya, yayin da wasu daga cikin waɗanda ake tsare da su suka wuce wa'adin tsarewar da doka ta tanada.
- Jami'ai sun yi biris da kiraye-kirayen neman agaji da aka yi ta yi, duk da cewa wani ma'aikacin lafiya ya nuna damuwa kan yanayin wurin tun da farko.
- Yanayin da aka tsare mutanen ya kai matsayin azabtarwa da wulaƙanci tare da tauye mutuncin ɗan Adam.
- Wuraren haƙar ma'adinan suna da lasisi na doka, sannan samamen da aka kai an gudanar da shi ne ba tare da sahalalliyar takardar umarnin aiki ba, kuma ba tare da kyakkyawan shiri ko tuntuɓar Sashen Jami'an Kula da Ma'adinai ba.
- An share tare da gyara wurin da aka tsare mutanen kafin masu bincike su isa, lamarin da ya haifar da damuwa kan yiwuwar lalata ko ɓoye shaidu.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce duk wanda aka samu da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Ya ce jami'an da aka kama da laifi za a dakatar da su daga aiki, sannan za a miƙa rahoton binciken ga babban lauyan tarayya domin ɗaukar matakan shari'a da suka dace.
A watan Satumba ne dai Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakke kuma sahihin bincike, game da mutuwar mutanen da ake zargin suna hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.
Hakan ya sa gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti mai mutum 10 domin binciken.
Kwamitin, wanda tsohon mataimakin daraktan DSS, Jonathan Kure, ke jagoranta, an ba shi wa'adin makonni biyu domin kammala bincikensa da gabatar da rahoto.
Sai dai kuma kwamitin ya nemi ƙarin lokaci bayan ƙarewar wa'adin da aka ɗeba masa.
























