Me ya sa Kannywood ba ta samun tagomashi a taron karrama ƴan fim na Afirka?

Asalin hoton, Amal Umar/IG
An gudanar da taron karrama jaruman fina-finan Afirka na shekara ta 2026, inda ranar Asabar 9 ga watan Mayu manyan taurari da masana harkar fim suka taru domin bikin ranar karramawar.
Taron mai suna Africa Magic Viewers' Choice Awards (AMVCA), shi ne mafi ɗaukar hankali a harkar nishaɗi a nahiyar Afirka, wanda kamfanin Africa Magic ke ɗaukar nauyi duk shekara.
An gudanar da taron ne a otel ɗin Eko Hotels and Suites da ke jihar Legas, kuma jarumai gwaraza ne suka taru, inda wasu suke karba kyauta, wasu kuma suka halarta domin taya abokan sana'arsu murna.
A mafi yawan lokaci masana'antar fim ta Najeriya, wadda ake wa laƙabi da Nollywood ce ke mamaye bikin, inda jarumanta da finafinata ke lashe kyaututtuka masu yawa.
Sai dai a cikin masana'antar fim ta Najeriya akwai wani ɓangare da ake ganin ba ya taka rawar da ta dace da shi a lokacin bikin - Kannywood - wato masana'antar fim ta arewacin Najeriya wadda ke haɗa finafinai a mafi yawan lokaci da harshen Hausa.
Duk da cewa miliyoyin mutane a ƙasashen Afirka ta yamma da kuma duniya ne ke kallon finafinan Kannywood a kowace rana, amma tauraruwa ɗaya ce tal daga masana'antar sunanta ya fito cikin ɗaya daga cikin ajujuwan karramawa a bikin na wannan shekara.
Amal Umar - sunanta ya fito ne ƙarƙashin ajin mai taimaka wa babbar tauraruwa (Best supporting actress) bisa rawar da ta taka a wani fim ɗin turanci mai taken 'The Herd', wanda a ƙarshe tauraruwa Linda Ejiofor ta lashe.
To amma me ya sa ake barin Kannywood a baya a bikin bayar da kyaututtukan na AMVCA?
Kannywoood a AMVCA

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A baya fina-finan Kannywood sun samu kyaututtuka a bikin na AMVCA, sai dai yawanci suna lashe kyautar da aka ware domin fina-finan Hausa ne.
Dr Muhsin Ibrahim, malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus, ya bayyana cewa "akwai matsaloli da yawa da masana'antar Kannywood ke fuskanta a cikin gida da waje, amma abin da ya sa Kannywood ba ta samun tagomashi a bikin bayar da kyaututtuka na AMVCA, matsala ce ta waje, ba ta cikin gida ba".
Mushin wanda ya daɗe yana bincike da nazari kan fina-finai, musamman Kannywood ya ce ƴan masa'antar sun gaza wajen haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen samun nasarar da ake magana.
"Ya kamata a ce suna samun haɗin gwiwa da masu shirya fina-finai na kudancin Najeriya, saboda su ne suka fi ƙarfi a dukkan irin waɗannan shirye-shirye na ƙasa. Har yanzu ana yi wa Kannywood kallon fina-finan yankin Arewa kaɗai," in ji shi.
Ya ce ya yi tsammanin akwai manyan jarumai a Kannywood da ya kamata a ce sun shige gaba wajen rage giɓin da ke tsakanin fina-finan Kannywood da na Kudancin Najeriya.
"Sai dai har yanzu gaskiya babu wata nasara da ake iya gani a zahiri. Kuma matuƙar ba a yi hakan ba, ba za a riƙa ganin ƴan arewa a irin waɗannan lamura ba," in ji Dr Mushin.
A game da abubuwan da masana'antar ya kamata ta yi domin samun cigaba da take buƙatar, Dr Mushin ya ce akwai buƙatar masu ruwa da tsaki na Kannywood su ƙara zama tare da jawo ƴan kudancin su yi aiki tare.
"Ba ƴan Kannywood ba ne kawai ya kamata su gyara. Su ma ƴan Kudancin Najeriya ɗin da masu shirya irin waɗannan manyan kyaututtukan su fahimci yanayin fina-finan Hausa."
Ya ce duk ƙoƙarin da ƴan Kannywood za su yi domin su samu karɓuwa, ba za su samu yadda suke so ba sai sun samu taimakon ƴan kudu.
"Ya kamata su fahimci cewa akwai yanayi da al'adun Kannywood. Ba dole ba ne sai an yi rungume-rugume da sumbata ba ne fim zai yi kyau. Ba kowane irin fim da suka yi ba ne za mu iya yi. Amma idan aka fahimci juna, sai a samu ƙarin tagomashi," in ji shi.
Wani abu da ke jan hankali shi ne yadda kyautar ke ɗaukar hankali, lamarin da ya sa wasu ke tambayar shin mene ne amfanin karramawar?
A game da wannan, Dr Mushin ya ce duk da cewa akwai masu shirya tarukan karrama fina-finai da sukan bayar da kuɗi, yawanci kawai ana yi domin nuna bajinta da ƙwanji a duniyar fim.
"Kuma a duniya ne baki ɗaya ake irin waɗannan karramawar. Akwai karramawar Oscars da sauran su. Sannan kuma ko nan gaba idan mutum yana samun irin waɗannan kyaututtukan, mai fim ɗin zai riƙa samun masu zuba jari da haɗin gwiwa da sauran su," in ji Muhsin.
Bikin bana
Karramawar ta bana ita ce ta 12, kuma jarumar fin ɗin kudancin Najeriya mai tashe, Linda Ejiofor ce ta fi samun tagomashi, inda ta lashe gwarzuwar jaruma, sannan ta lashe jaruma mai bi. Ga waɗanda suka lashe kyautar a bana:
- Gwarzon jarum – Uzor Arukwe.
- Gwarzuwar jaruma – Linda Ejiofor.
- Jarumi mai taimakon babban jarumi – Bucci Franklin.
- Jaruma mai taimakon babban jaruma – Linda Ejiofor
- Gwarzon fim – My Father's Shadow.
- Gwarzon darakta – Akinola Davies Jr. for My Father's Shadow.
Kannywood a baya

Asalin hoton, Africamagic/IG
A baya akwai kyauta ta musamman da aka ware kan fina-finai da aka yi amfani da yaren gida, inda ake ware kyaututtuka ga kowane harshe irin su Hausa da Swahili da Yarbanci da Ibo da sauran su.
Sai dai yanzu an koma bayar da kyautar ta fina-finan gida kan yankunan Afirka, inda a yankin Afirka ta Yamma da Najeriya, fim ɗin Lisabi: A Legend Is Born ya lashe kambun na bana.
A shekarar 2023, fim ɗin Aisha, na Abubakar Bashir Maishadda ya samu kyautar a ɓangaren Hausa.
A shekarar 2018, fim ɗin Mansoor na Ali Nuhu ya lashe kyautar, inda shi ma ya lashe kambun gwarzon fim ɗin Hausa.
A taron na shekarar 2025 ne fim ɗin Hausa na 'Mai Martaba' ya samu shiga cikin fina-finan gida na Afirka ta Yamma da AMVCA ya ware, amma bai lashe kambun ba daga baya. Sannan fim ɗin ne ya wakilci Najeriya a taron karrama fina-finai da jarumai na duniya wato Oscars.








