Ko dakatar da ƴan fim na iya gyara masana'antar Kannywood?

Asalin hoton, IG/Multiple
Masana'antar Kannywood ta daɗe tana fuskantar ƙalubale daga cikin gida da kuma waje, waɗanda sukan yi cikas ga harkokinta, har wasu lokutan takan tsaya cak.
Amma daga cikin manyan ƙalubalen da suka ɗaga hankali masana'antar akwai rigingimun ciki, musamman tsakanin hukumar tace fina-finai - wadda a baya-bayan nan take ƙarƙashin shugabancin ɗan fim - da wasu jarumai.
A zamanin tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ne aka ƙirƙiri hukumar tace fina-finai domin sanya ido kan yadda masana'antar take gudanar da harkokinta, musamman fina-finai da bidiyo.
A zamanin, da Malam Abubakar Rabo ke shugabantar hukumar, an yi ta kai ruwa-rana tare da kiraye-kiraye daga masana'antar da a mayar da shugabancin hukumar a ƙarƙashin kulawar ƴayan masana'antar.
Sai dai daga zamanin Isma'ila Na'Abba Afakallah zuwa yanzu da Abba El-Mustapha yake shugabantar hukumar, an dakatar da ƴan fim da mawaƙa da dama, ciki har da waɗanda aka tura gidan kaso.
An daɗe ana kallon dokoki na addini da al'ada a matsayin wasu daga cikin turakun da ke yin cikas ga cigaban masana'antar fim ɗin ta Kannywoon.
A yanzu da ake tattaunawa kan dakatar da jaruma Amina Uba da Adam Garba, BBC ta yi duba shin ko dakatarwar na tasiri wajen gyara ɗabi'un ƴan masana'antar?

Asalin hoton, Amina Uba Hassan/Adam Garba/FB
Shin dakatarwar na tasiri?
Dr Muhsin Ibrahim malami ne a Jami'ar Cologne da ke Jamus, ya ce ayyukan hukumar tace fina-finan za su yi tasirin da ake buƙata ne kawai idan ta samu haɗin kan masu ruwa da tsaki a masana'antar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce dama ita hukumar tana dakatar da jarumai ne ko sauran masu shirya fim ta hanya biyu:
- Ko dai don a hukunta su bisa saɓa doka
- Ko kuma don wasu su shiga taitayinsu
Sai dai ya ce rashin haɗin kan da masana'antar ke fama da su yana kawo tsaiko ga ayyukan hukumar.
"Amma saboda rashin ƙarfin ƙungiyoyin masana'antar Kannywood, da kuma haɗin kansu ana samun ɓaraka sosai, musamman bayan hukumar ta dakatar da ɗan fim," in ji shi.
Ya ce idan forudusa yana ganin ya isa, sai ya saka ɗan fim ɗin da hukumar ta dakatar saboda ya san ya isa.
"Idan forodusan yana ganin babu abin da za a yi masa, ya san ba za hukunta shi ba saboda don ya karya dokar. Wannan ne ya sa sau tari za ka ga dakatarwar ba ta da wani tasiri," in ji Mushin.
Muhsin ya ƙara da cewa hukumar tana buƙatar haɗin kai sosai daga masu shirya fim domin a samu abin da ake so.
Ya ƙara da cewa abin da ya fi dacewa shi ne duk ɗan fim da aka datakar kada a saka shi a wani fim.
"Idan kuwa aka saka shi a fim, to ya kamata a ci tarar wanda ya shirya fim ɗin kuɗi mai yawa ko shi ma a dakatar da shi."
Masanin harkokin fina-finan ya ce idan ba haka aka fara yi ba, "wannan dakatarwar ba ta da muhimmanci."
Muhsin ya yi misali da yanayin bambanci da kuma hurumin da hukuma take da ita, inda ya ce zai yi wahala ta yi hukunta waɗanda ba ƴan Kano ba idan ba an samu hadin kan masu shirya fim ba.
"Misali idan aka dakatar da mutum a Kano, kamar yadda aka yi na Amina Uba da Adamu Garba. Ka ga duk ba ƴan Kano ba ne, an dakatar da su, kuma yanzu yawancin fina-finain Kannywood a wasu jihohin irin su Gombe da Kaduna da Jigawa da Abuja ake yi," in ji shi.
Ya ce tunda ba ƴan Kano ba ne, don hukumar ta yi a kansu, babu wani tasiri da hakan zai yi.
"Amma yanzu yawancin manyan masu shirya fina-finan ƴan Kano ne. Don haka idan za a samu haɗin kansu, kuma ga shi shugaban hukumar ɗan cikinsu ne, sai ka ga dakatarwar na tasiri sosai," in ji Muhsin.
Rabilu Musa Ibro
Rikicin farko da ya fara jan hankali shi ne na marigayi Rabilu Musa Ɗan Ibro da hukumar fim.
A fim ɗin Rabilu mai suna 'Ƙara'in Ibro' hukumar ta kama tare da ɗaure furodusan fim ɗin, Ibrahim Bauni na shekara 10, sannan aka dakatar da mai kasuwancin fim ɗin mai suna Shazali Kamfa, amma ba a haɗa da Ibro ba.
Sai dai an sake kama shi a fim mai suna 'Ibro a loko' tare da abokinsa, Lawal Ƙaura, inda aka zarge su shirya fim ba tare da rajista ba.
Adam A. Zango
Wata dakatarwar da aka yi da ta yamutsa hazo ita ce ta jarumi Adam A. Zango, lamarin da ya sanar da komawa jihar Kaduna da gudanar da fina-finai.
Sai dai ya sake jan hankali a lokacin Adam A. Zango ya fito a wani bidiyo da Rahama Sadau ta wallafa a Instagram yana cewa zai shiga jihar domin kallon fim ɗin 'Mati A Zazzau'.
Bayan fitar da bidiyon ne aka ruwaito shugaban hukumar tace fina-finai na wancan lokacin, Isma'ila Na'abba Afakallah, yana cewa da zarar jarumin ya shiga Kano domin aiwatar da wani da ya shafi fim za su kama shi, amma idan kallon fim kawai zai je, babu ruwansu da shi.
Rahama Sadau
A shekarar 2016 jaruma Rahama Sadau ta fito a waƙar Hip-hop tare da mawaƙi Classiq mai suna "I Love You".
Waƙar ta tayar da ƙura matuƙa, lamarin da ya sa hukumar ta dakatar da jarumar daga taka rawa a masana'antar.
Hukumar ta saba ƙa'idoji ta hanyar sanya tufafi masu bayyana jiki da sauran laifuka, inda aka dakatar da ita tsawon shekara ɗaya.
Sanusi Oscar
A watan Agusta na 2019, Hukumar ta gurfanar da daraktan fina-finai Sanusi Oscar a gaban kotu saboda ya "saba ka'idojin gudanar da sana'arsa a Kano, inda ya saki wata waka wadda akwai baɗala a ciki", kamar yadda shugaban hukumar Isma'ila Na'abba Afakallahu ya shaida wa BBC.
Oscar ya musanta zargin kuma alkali Aminu Fagge na kotun majistare da ke Kano ya bayar da belinsa bisa sharuda biyu — wajibi ne mutum biyu su tsaya masa kuma daya daga cikinsu ya zama dan uwansa na jini, tare da haramcin magana da kowacce irin kafar yada labarai
Naziru Sarkin Waka
A watan Satumba na 2019, rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta kama fitaccen mawakin nan Naziru M. Ahmed, wanda aka fi sani Naziru Sarkin Waka "saboda kalaman batanci" da ya yi a cikin wasu wakokinsa.
Hukumar tace fina-finan, wadda ta bayar da umarnin kama shi, ta kara da cewa ana tuhumar mawakin da gudanar da dakin yin waka, wato sutudiyo, a gidansa, zargin da Naziru M. Ahmed ya musanta.
Naziru shi ne Sarkin Wakar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, mutumin da ya dade yana kai ruwa rana tsakaninsa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje lamarin da ya kai ga raba shi da sarauta, kafain daga baya aka mayar da shi.
Shi ma kotun Majistare a birnin Kano ta bayar da belin sa da sharuda wadanda suka hada da bayar da kudi naira dubu 500, da mika fasfo dinsa na tafiye-tafiye, da kuma gabatar da mutane uku da za su tsaya masa, wadanda dole su kasance ma'aikatan gwamnatin jihar Kano da kuma dagacin yankin da yake zaune.
Sauran jaruman da aka taɓa dakatarwa sun haɗa da:
- Nafisat Abdullahi
- Sani Musa Danja
- Samha M. Inuwa
- Sadiq Zazzaɓi








