KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 27/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 27/10/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima
  • Dattijuwa

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar

  1. Kungiyar Ansaru ta ɗauki alhakin kashe Sheikh Yahaya Masussuka

    mai dauke da bindiga

    Ƙungiyar Ansaru, wadda ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda, ta ɗauki alhakin kisan fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Yahaya Masussuka, saboda a cewarta ya kauce wa koyarwar Musulunci.

    A cikin wani saƙo da masanin tsaro Dr Bulama Bukarti ya fitar a shafinsa na X, ya ce ƙungiyar ta fitar da wani saƙon murya, inda ta ce ta kai harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Talata.

    To sai dai rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin.

    Ansaru ta zargi Sheikh Yahaya Masussuka da abin da ta kira "saba wa addinin Musulunci", amma ba ta bayyana takamaiman abin da take zarginsa da aikatawa ba.

    Ƙungiyar ta kuma soki koyarwar marigayin ta inganta tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban da kuma zaman lafiya tsakanin al'umma, tana mai nuni da cewa wannan ne ya sa ta kai masa hari.

    Ansaru ta balle daga Boko Haram ne a shekarar 2012 bayan saɓani da tsohon shugaban kungiyar, Abubakar Shekau.

    Tun daga lokacin ƙungiyar ke gudanar da ayyukanta galibi a arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihohin Zamfara, Kaduna da Nijar.

  2. Nijar ta zargi Chadi da haɗa kai da Faransa wajen kai mata hari ta sama

    Tiani

    Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta zargi maƙwabciyarta Chadi da kai wani mummunan harin jirgin yaƙi maras matuƙi ƙasarta,tare da goyon bayan Faransa.

    A cikin wata sanarwa da aka watsa a gidan talabijin na ƙasa a daren Litinin, gwamnatin Nijar ta ce wani jirgin yaƙi maras matuƙi da ya taso daga ƙasar Chadi ya kai hari wani ƙauye a yankin Agadez da ke arewacin ƙasar a ƙarshen mako, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu da dama.

    Nijar ta ce tana da ƙarin hujjojin da ke ƙarfafa zargin da take yi kan inda harin ya fito, sai dai ba ta bayyana waɗannan hujjojin ga jama'a ba.

    Gwamnatin ta ce ta buɗe cikakken bincike kan lamarin tare da shirye-shiryen kai ƙara a kotunan ƙasa da ƙasa.

    Haka kuma ta ce za ta gayyaci jakadan Chadi domin miƙa ƙorafi kan abin da ta kira keta ƴancin iyakokin ƙasarta.

    Ya zuwa yanzu dai ƙasashen Chadi da Faransa ba su fitar da wata sanarwa kan waɗannan zarge-zargen ba.

    Wannan zargi na zuwa ne a lokacin da dangantaka ke ci gaba da yin tsami tsakanin Nijar da Faransa tun bayan juyin mulkin sojin da ya kifar da gwamnatin farar hula a watan Yulin shekarar 2023, wanda ya kawo gwamnatin mulkin soja mai ci a halin yanzu.

  3. Adadin waɗanda suka kamu da cutar Ebola a Kongo ya zarta 10,000

    ebola

    Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) ya haura 10,000, a cewar sabon rahoton kididdigar annobar da hukumomin lafiya na ƙasar suka fitar.

    Rahoton, wanda Cibiyar Kula da Lafiyar Jama'a ta Ƙasa (INSP) ta wallafa, ya nuna cewa an samu sabbin mutum 96 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Jihar North Kivu ce ta fi yawan sabbin masu kamuwa da cutar inda ta ke da mutum 58, sai lardin Ituri mai mutum 32, yayin da yankin Tshopo ke da mutum shida.

    Sabbin alkaluman sun nuna cewa jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a yayin annobar Ebola ta 17 da ƙasar ke fuskanta yanzu ta kai 10,060.

    Mahukuntan lafiya sun ce mutum 4,887 sun mutu bayan kamuwa da cutar nau'in Bundibugyo, yayin da marasa lafiya 2,684 suka warke.

    Haka kuma an sallami 14 a ranar 25 ga Oktoba bayan gwaje-gwaje biyu da aka yi musu sun tabbatar ba su ɗauke da cutar.

    Hukumomin lafiya sun ce alƙaluman na nuna muhimmancin gano masu ɗauke da cutar da wuri tare da tabbatar da bin ƙa'idojin jana'iza cikin aminci domin daƙile yaɗuwar cutar.

    Ko da yake North Kivu ce ta fi samun sabbin masu kamuwa da cutar a wannan lokaci, har yanzu Ituri ce yankin da annobar ta fi yi wa illa, inda take da kusan kashi 72 cikin ɗari na dukkan waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar tun bayan fara barkewar annobar.

  4. Za a gudanar da cikakken bincike kan kisan Sheikh Yahaya Masussuka - Gwamnan Katsina

    Radda

    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana alhini kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, wanda ya bayyana a matsayin malami mai daraja kuma mai fafutukar wanzar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mabiya addinai daban-daban.

    A cikin saƙon ta'aziyyar da ya fitar a shafinsa na X, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, da alummar musulmi, da duk waɗanda wannan rashi ya shafa.

    Gwamnan ya kuma tabbatar wa al'ummar jihar Katsina cewa za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano waɗanda ke da hannu a mutuwar malamin, tare da gurfanar da su gaban shari'a.

    Ya kuma yi kira ga alummar jihar da su kwantar da hankalinsu, su ba jami'an tsaro cikakken haɗin kai yayin gudanar da bincike, tare da kiyaye zaman lafiya a wannan lokaci na alhini.

    Gwamnan ya kuma yi wa mamacin addu'ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, ya sanya shi a Aljannatul Firdausi.

  5. Harin jirgi maras matuƙi ya hallaka mutum sama da 20 a Sudan

    Rahotanni daga Sudan sun ce wani harin jirgin sama maras matuƙi da aka kai birnin Nyala na jihar Darfur ta Kudu ya kashe mutum 21 tare da jikkata wasu mutum 40.

    Shaidu sun bayyanawa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP) cewa an kai harin ne da yammacin ranar Litinin kan wata kasuwa da ke arewacin birnin, wadda ke ƙarkashin ikon dakarun rundunar RSF.

    Ɓangarorin biyu da ke fafatawa a yaƙin basasar Sudan na yawan kai wa juna hare-hare ta amfani da jirage marasa matuƙa.

    Haka kuma akwai rahotannin da ke cewa rundunar RSF ta sake kai hari kan kayayyakin samar da wutar lantarki da ke kusa da babban birnin ƙasar, Khartoum.

  6. DSS ta gurfanar da wani magoyin bayan Atiku kan yaɗa wasiƙar bogi kan Tinubu

    DSS

    Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Najeriya, DSS, ta gurfanar da wani da aka bayyana a matsayin magoyin bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bisa zargin yaɗa wata wasiƙar bogi da aka danganta ga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

    A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X, ya ce mutumin mai suna Mubarak Abdullahi, wanda aka fi sani da Sardaunan Samari, na fuskantar shari'a a jihar Kaduna kan zarginsa da wallafa takardar a shafinsa na Facebook, wanda ya ce Tinubun ya aikewa shugaban Amurka Donald Trump, tare da rubuta saƙon "Atiku is coming".

    Rahotanni sun ce an kama Mubarak ne a ranar 28 ga watan Satumba, kuma yayin bincike ya amince cewa shi ne ya wallafa takardar, tare da neman afuwa kan abin da ya aikata.

    Sai dai DSS ta ce neman afuwar bai wadatar ba, inda ta gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare, wadda ta ba da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Kaduna har zuwa ci gaba da shari'ar.

    Hukumar ta kuma shigar da tuhume-tuhume guda uku a kansa a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, waɗanda suka haɗa da laifukan da suka shafi amfani da yanar gizo wajen aikata laifi da kuma ɓata suna.

    Sai dai BBC ba ta samu wani bayani daga hukumar DSS game da batun ba.

  7. Aljeriya za ta tura sojojinta Nijar a karon farko cikin sama da shekaru 50

    jirgin soji

    Aljeriya ta amince da tura sojojinta Nijar, a karon farko da za ta tura dakarunta wata ƙasa tun bayan aika sojoji Masar a lokacin yaƙin Larabawa da Isra'ila a shekarar 1973.

    Matakin ya biyo bayan ziyarar da ministan tsaron Nijar ya kai Algiers, yayin da Nijar ke neman ƙarin goyon baya wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, kuma wasu daga cikinsu na da alaƙa da al-Qaeda.

    Aljeriya na da muhimman muradun tattalin arziki a Nijar, ciki har da wani shirin samar da bututun iskar gas da zai rika jigilar iskar gas daga Najeriya ta cikin Nijar zuwa Aljeriya.

    Ana sa ran sojojin za su taimaka wajen kare kayayyakin samar da makamashi da ke arewacin Nijar kusa da iyakar Libya.

    Tura sojojin na zuwa ne yayin da ƙasashen biyu ke ƙoƙarin inganta alaƙarsu bayan takaddamar diflomasiyya da ta kunno kai a shekarar 2025, lokacin da Nijar ta janye jakadanta daga Algiers.

    Majalisar dattawan Aljeriya ta gudanar da zama na musamman a ranar Lahadi domin kaɗa ƙuri'a kan amincewa da shirin.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa sanatoci 148 daga cikin 174 ne suka amince da ƙudirin, kafin daga bisani majalisar wakilai ta mara baya.

    Sai dai har yanzu ba a bayyana lokacin da za a tura sojojin ba ko kuma adadin dakarun da za a aika.

    Wannan mataki zai zama karo na farko da Aljeriya za ta yi amfani da tanadin kundin tsarin mulkinta na shekarar 2020 da ya ba ta damar tura sojoji ƙasashen waje, lamarin da ke nuna babban sauyi a manufofinta na tsawon lokaci kan ƙin tura dakarunta zuwa ƙasashen waje.

    "Ba wai za mu tura sojoji ba ne domin su yi yaƙi a Nijar ba, illa domin su kare muhimman kayayyakin tattalin arziki," in ji Sanata Belkacem Boulghiti na Algeria ga manema labarai bayan kaɗa ƙuri'ar.

  8. Sojojin Najeriya sun hallaka mayaƙan ISWAP 16 a Tafkin Chadi

    Sojoji

    Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa Maso Gabas, wato Operation HADIN KAI (OPHK), ta ce ta kashe mayaƙan da ake zargin 'yan ƙungiyar ISWAP ne guda 16 a wasu hare-haren haɗin gwiwa ta sama da aka kai kan wurare uku da ake zargin maboyar 'yan ta'adda ne a yankin Tunbunma da ke Kudancin Tafkin Chadi.

    Mukaddashin Jami'in Yaɗa Labaran Soja, Kyaftin Mohammed Goni, wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ya ce an kai harin ne tsakanin ƙarfe 1:00 na dare zuwa 2:00 na dare a ranar 26 ga Oktoba, 2026, inda aka yi amfani da makamai ta sama da ta ƙasa wajen kai hare-haren.

    Rundunar ta ce farmakin, wanda aka gudanar bayan samun bayanan sirri da suka nuna kasancewar wasu manyan jagorori da mayaƙan ƙungiyar a wuraren, wani ɓangare ne na ci gaba da matsin lamba kan gungun 'yan ta'adda a yankin Tafkin Chadi, kamar yadda gidan talibijin na Channels ya ruwaito.

    Ta kuma jaddada cewa babu wata mafaka ga 'yan ta'adda, saboda a cewar ta har yanzu ta na da ƙudurin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, ta hanyar amfani da bayanan sirri wajen gudanar da ayyukan ta na yaƙi da 'yan ta'adda a Arewa Maso Gabashin Najeriya.

    Haka kuma ta yi kira ga jama'a da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin tallafa wa ayyukan yaƙi da ta'addanci.

  9. An fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Rasha da Ukraine a birnin Oleshky

    An fara aiwatar da wata yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Rasha da Ukraine a birnin Oleshky, wanda ke ƙarkashin ikon Rasha.

    Wannan tsagaita wuta na da nufin ba da damar kai kayan agaji da kuma fitar da fararen hula daga yankin.

    Wakilin BBC ya ce a makon da ya gabata ne uwargidan shugaban Amurka Donald Trump, Melania ta sanar da yarjejeniyar wadda ta shafi yankin kaɗai, yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa a sauran sassan ƙasar.

    Oleshky dai yana kan gaɓar kudancin kogin Dnipro, kuma mazauna yankin da suka rage suna fuskantar matsanancin ƙarancin abinci da sauran kayayyakin buƙata na yau da kullum.

  10. Za a iya ayyana ƙarshen Ebola nan da watan Disamba - Gwamnatin Najeriya

    Ministan Lafiya

    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na iya ayyana ƙarshen annobar Ebola nan da ranar 7 ga Disamba, 2026, idan ba a sake tabbatar da mai ɗauke da cutar ba, ko wanda ake zargi da kamuwa ita, sannan kuma ƙasar ta cika sharuɗɗan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gindaya.

    Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama'a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

    Ya ce hakan zai dogara ne kan sakamakon bibiyar waɗanda suka yi hulɗa da masu cutar da kuma cikar wa'adin kwanaki 42 ba tare da samun mai cutar ba, da Cibiyar Yaƙi da Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) tare da WHO za su jira.

    Sai dai Pate ya jaddada cewa wannan ranar ta wucin gadi ce, kuma za ta iya sauyawa idan aka sake gano wani sabon mai cutar.

    Bisa ƙa'idojin WHO, ana iya ayyana cewa annoba ta kawo ƙarshe bayan cikar kwanaki 42 a jere ba tare da samun wani sabon mai cutar ba, tare da cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata domin tabbatar da cewa an daƙile yaɗuwar cutar.

  11. An buɗe rumfunan zaɓe a babban zaɓen Isra'ila

    Isra'ila

    An fara buɗe rumfunan zaɓe a babban zaɓen Isra'ila na farko tun bayan hare-haren da ƙungiyar Hamas ta kai hari a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023.

    Firaminista Benjamin Netanyahu na neman tsawaita wa'adinsa a kan karagar mulki, bayan shekara uku na yaƙi a fagage daban-daban.

    Babban ɗan takarar jam'iyyar adawa shi ne tsohon kwamandan soji, Gadi Eisenkot.

    Wakiliyar BBC ta ce muhimman batutuwan da suka mamaye zaɓen sun haɗa da ɗaukar alhakin gazawar tsaron da ya haifar ta hare-haren 7 ga watan Oktoba, da yadda ake gudanar da yaƙe-yaƙe a yankin, da kuma matsayin Isra'ila a idon duniya.

  12. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar ranar Talata.

    A yau ma za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta kamar Fesbuk da X da Instagram, sannan ku ziyarci shafinmu na YouTube domin kallon bidiyo.