Ko Kwankwaso zai raba ƙuri'ar Atiku a jihohin Arewa?

Asalin hoton, Atiku Abubakar/Facebook
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, ɗaya daga cikin tambayoyin da ke janyo ce-ce-ku-ce a siyasar Najeriya ita ce ko jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, zai iya raba wa Atiku Abubakar ƙuri'un Arewacin ƙasar ganin cewa dukansu ƴan yankin ne kuma suka da tasiri.
A zaɓen 2023, Atiku Abubakar na PDP da Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP sun yi gogayya wajen neman goyon bayan masu kaɗa ƙuri'a a jihohin Arewa.
Duk da cewa Atiku ya yi nasara a wasu manyan jihohin yankin, Kwankwaso ya samu tagomashi musamman a jihar Kano, inda ya samu gagarumar nasara tare da nuna cewa har yanzu yana da babban tasiri a cikin siyasar yankin ta hanyar tafiyar Kwankwasiyya.
Masana siyasa na ganin cewa ƙarfin Kwankwaso a Kano da wasu sassan Arewa maso Yamma na iya rage wa Atiku yawan ƙuri'un da zai samu idan suka sake fafatawa a zaɓe guda. Kano dai na cikin jihohin da suka fi yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya, lamarin da ke sa duk ɗan takarar da ya samu rinjaye a jihar ya samu wata muhimmiyar fa'ida.
Sai dai wasu na ganin tasirin Kwankwaso bai wuce wasu sassan Arewa ba, yayin da Atiku ke da magoya baya a jihohi da dama na Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da wasu sassan Arewa maso Yamma.
Hakan ne ya sa ake muhawara kan ko Kwankwaso zai iya ɗauke wa Atiku ƙuri'u masu yawa ko kuma zai fi tasiri ne a Kano da jihohin da ke makwabtaka da ita.
Abokan tafiyar siyasa da suka raba gari
Dangantakar siyasa tsakanin Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso ta daɗe, domin sun shafe sama da shekara 30 suna gwagwarmayar siyasa, lamarin da ya sa ake tunanin ya kamata su kasance makusantan juna a siyasa.
Duk da cewa a wasu lokuta sun kasance a jam'iyyu daban-daban ko kuma sun kara da juna a zaɓe, asalinsu na siyasa ya samo asali ne daga tafiya guda ƙarƙashin marigayi Shehu Musa Yar'Adua.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A zamanin mulkin soji na Janar Ibrahim Babangida ne da aka fara shirye-shiryen komawa dimokuraɗiyya ta Jamhuriya ta uku, Shehu Musa Yar'Adua ya kafa ƙungiyar siyasa ta People's Front of Nigeria, wadda ta kasance ɗaya daga cikin ƙungiyoyin siyasa mafi ƙarfi a wancan lokaci.
Atiku da Kwankwaso dukkansu sun kasance cikin fitattun mambobin wannan ƙungiya tare da wasu ƴan siyasa, waɗanda yawancinsu daga baya suka mamaye siyasar Najeriya.
A lokacin an samu cikas saboda gwamnati ta ƙi yi wa People's Front rajista a matsayin jam'iyyar siyasa, wanda hakan ya sa mambobinta da dama suka shiga jam'iyyar SDP domin shiga zaɓen 1992.
A zaɓen shekarar 1992, Kwankwaso ya lashe kujerar majalisar wakilai, inda ya zama mataimakin shugaban majalisar. A gefe guda kuma, Atiku ya fara da takarar gwamna sannan daga baya ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa na SDP a shekarar 1993, inda ya fafata takarar fitar da gwani, amma Abiola ya doke shi.
Bayan rushewar Jamhuriya ta uku sakamakon soke zaɓen da ya yi fice da zaɓen 12 ga Yuni, Atiku da Kwankwaso sun ci gaba da kasancewa cikin tsarin siyasar da ya samo asali daga People's Front. Daga baya suka shiga People's Democratic Movement (PDM), wata ƙungiya da ta taka muhimmiyar rawa wajen fafutukar dawo da mulkin dimokuraɗiyya.
Da aka dawo mulkin farar hula a shekarar 1999, su biyun suka kasance cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar PDP.
A zaɓen na 1999, Atiku da Kwankwanso sai suka tsaya takarar kujerar gwamna, inda Atiku lashe zaɓen gwamna jihar Adamawa, shi kuma Kwankwanso ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.
Sai dai shi Atiku bai yi gwama ba, saboda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na lokacin, Olusegun Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa., yayin da Kwankwaso ya zama Gwamnan Jihar Kano.
Atiku ya yi shekara takwas a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, shi kuma Kwankwanso ya yi shekara huɗu a gwamna, aka kayar da shi, amma daga bisani ya zama ministan tsaro. Amma dukkansu suna PDP tare.
Za su iya zama wuri ɗaya?
Doka Kabiru Sa'id Sufi, masanin siyasa ne, kuma mai sharhi kan harkokin siyasar Najeriya ya ce akwai abubuwa biyu muhimmai a suke tsaiko wajen zaman ƴansiyasar guda biyu a inuwa ɗaya.
"Na farko dai duk da kasancewar idan aka duba tarihi ƴan gidan siyasar gida ɗaya ne wato gidan fadama kuma ƴan taɓo ne, amma da aka shiga mulkin Obasanjo, sai su Kwankwaso da wasu ministoci irin su Nasir El-Rufai suka zama na hannun daman Obasanjo a lokacin a Atiku da Obaanjo suna takun-saƙa."
Masanin siyasar ya ƙara da cewa abu na biyu mai muhimmanci shi ne dukkan ƴan siyasar biyu yanzu burinsu ɗaya ne.
''Yanzu dukansu burinsu zama shugaban ƙasa ne, shi ya sa yake da wahala su haɗu a waje ɗaya, har gara Kwankwaso ma zai iya zama mataimakin shugaban ƙasa."
'Za a raba ƙuri'a'
Masanin harkokin siyasa daga Kano, Kabiru Sufi, ya ce tasirin Rabiu Musa Kwankwaso a jihar Kano na iya kawo wa Atiku Abubakar ƙalubale a zaɓen shugaban ƙasa, musamman idan aka yi la'akari da ƙarfin da Kwankwaso ke da shi a jihar.
A wata tattaunawa, Kabiru Sufi ya bayyana cewa rarrabuwar ƙuri'u a Kano na iya yin tasiri ga sakamakon zaɓen.
"Ba shakka Kwankwaso zai kawo wa Atiku tangarɗa, musamman a Kano. Sannan zai iya faruwa idan ya samu ƴan takara masu ƙarfi a wasu jihohi, kamar yadda ya samu a Taraba a zaɓen baya," in ji shi.
Sai dai ya ce dabarar da ta fi dacewa ga Atiku ba wai mayar da hankali kan samun nasarar lashe duk jihohin ba ne, illa dai neman ƙuri'un da za su taimaka su cicciɗa shi.
"Abin da Atiku ya fi kamata ya mayar da hankali a kai shi ne samun ƙuri'un da lissafi zai kai masa ga nasara a jihohi daban-daban. Kamar yadda Tinubu ma yake yi, akwai jihohin da kashi 25 cikin ɗari kawai yake buƙata. Shi ma Atiku ya kamata ya bi irin wannan tsari," in ji Kabiru Sufi.
Masanin ya kuma yi hasashen cewa za a ga gagarumar rarrabuwar ƙuri'u a Kano saboda ƙarfin manyan jam'iyyun siyasa da ke fafatawa a jihar.
"Lallai za a raba ƙuri'un Kano sosai saboda yadda siyasar jihar ta kasu. Kwankwaso na da babban tasiri wajen jawo ƙuri'u, sannan gwamnatin jihar ta APC ta sha alwashin tabbatar da cewa jam'iyyar ta yi nasara a jihar. Haka kuma Atiku ya sauya salon yadda yake tunkarar masu zaɓe a Kano," in ji shi.
A cewarsa, wannan yanayi na nuna cewa Kano za ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da za su iya taka muhimmiyar rawa wajen tantance sakamakon zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.


























