Mourinho ya sanya wa Madrid sharaɗi, Newcastle da Chelsea na son Nunez

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na tattaunawa da wakilin Jose Mourinho kan yuwuwar nada kociyan na Benfica mai shekara 63 a matsayin kociyan kungiyar.(Athletic)
Rahotanni sun ce Mourinho wanda ya kasance tsohon kociyan Chelsea da Manchester United, wanda kuma Real ta tuntube shi kai tsaye ya bukaci a ba shi cikakken iko da kuma dama sosai wajen saye da sayar da 'yan wasa. (Sky Germany)
Newcastle da Chelsea na son tsohon dan wasan Liverpool Darwin Nunez, inda ake ganin dan wasan mai kai hari dan kasar Uruguay mai shekara 26 kila zai bar kundiyarsa ta Al-Hilal ta Saudiyya. (Daily Star)
Arsenal, da Liverpool, da Bayern Munich, da kuma Barcelona dukkaninsu na sha'awar dan wasan gaba na gefe na Paris St-Germain da Faransa Bradley Barcola. (Mundo Deportivo)
Atletico Madrid na dab da cimma yarjejeniya a cinikin dan wasan tsakiya na Wolves Joao Gomes, na Brazil mai shekara 25, a kan kudin da ya kai fam miliyan 39. (Givemesport)
Inter Milan na shirin watsi da bukatar mai tsaron ragar Tottenham Guglielmo Vicario, dan Italiya mai shekara 29, domin ta mayar da hankali wajen karfafa wasu bangarorin kungiyar. (Corriere dello Sport)
Har yanzu Leeds ce kan gaba a kungiyoyin da ke son sayen dan wasan Juventus mai kai hari Lois Openda a bazaran nan duk da sha'awar dan wasan na tawagar Belgium mai shekara 26 da kungiyar Coventry City ke yi. (Football Insider)
Newcastle za ta yi wa sashen nemo mata 'yan wasa garambawul inda za ta nada masu farauto mata 'yan wasa da za su rika leka kasashen yankin Balkan wato na kudu maso gabashin Turai - Albania, da Bosnia da Herzegovina, Bulgaria, da Croatia, da Girka, da Kosovo, da Montenegro, da Macedonia ta Arewa, da Romania, da Serbia, da kuma Slovenia. Shi kuwa tsohon mai kai hari na kungiyar Shola Ameobi zai bar aikinsa na mai kul da bayarwa ko aro 'yan wasa a kungiyar. (The i)











