Kamfanoni 21 da kotu ta ce suna harkoki ba bisa ƙa'ida ba a Najeriya

Federal High Court
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, ta samu kamfanoni 21 da laifin gudanar da harkokin zuba jari ba tare da lasisin Hukumar Kula da Kasuwannin Hannun Jari ta Najeriya, SEC ba.

Mai shari'a Anyalewa Onoja-Alapa ce ta yanke hukuncin, bayan da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, ta gurfanar da kamfanonin a gaban kotun.

Kotun ta ci tarar kowane kamfani Naira miliyan 30, wanda ya sa jimillar tarar ta kai Naira miliyan 630.

Haka kuma, an umarci kowanne daga cikinsu ya biya ƙarin Naira 200,000 kan kowace rana da aka tabbatar ya aikata laifin.

Waɗanne kamfanoni ne?

Ga jerin kamfanonin 21 da kotun ta samu da laifin:

1. Ngwuoke Daniels Technologies

2. Credio Banco Ltd

3. Digital Company Ltd

4. Co Request Capital Nigeria Ltd

5. Mega Drop Quality Stores Ltd

6. Norland Global Ltd

7. Oxford International

8. Creative Agriculture Cooperative

9. Qnet Nigeria Ltd

10. Qnet Professional Skill Academy Ltd

11. Mastermind Energy & Agro Nigeria Ltd

12. Atus West Africa Investment Company

13. Eatrich360 Farms

14. Matag Agro General Services

15. Viables X Agribusiness Ltd

16. Kwakol Markets Ltd

17. Light Shade International Ltd

18. Value Growth Ltd

19. B12 Synergy Nigeria Ltd

20. Phresh Farm Ltd

21. Omega Pro Global Resources.

Me ake tuhumar kamfanonin da shi?

EFCC ta gurfanar da kamfanonin ne kan tuhume-tuhume da suka shafi gudanar da harkokin hada-hadar kuɗi ba tare da lasisin da doka ta tanada ba.

Hukumar ta ce laifin ya saɓa wa Sashe na 57(1) na Dokar Banks and Other Financial Institutions Act, 2020, kuma hukuncinsa yana ƙarƙashin Sashe na 57(5)(a) na dokar.

A ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen, EFCC ta ce Mega Drop Quality Stores Limited, duk da cewa an yi wa kamfanin rajista a Hukumar Rijistar Kamfanoni ta Najeriya, CAC, ya gudanar da harkokin kula da zuba jarin kuɗi tare da tallata irin wannan sana'a ba tare da ingantaccen lasisi daga SEC ba.

An gabatar da makamancin wannan tuhuma kan Ngwuoke Daniels Technologies, inda aka zarge shi da tallatawa da kuma gudanar da harkokin kula da zuba jari ba tare da lasisin SEC ba.

Yadda shari'ar ta gudana

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An gurfanar da kamfanonin a gaban kotun a ranakun 15 da 16 ga Satumba 2026 daga sashen EFCC na Abuja.

Babu wakilan kamfanonin da suka halarci kotun lokacin da aka karanta tuhume-tuhumen.

Bisa buƙatar lauyan EFCC, Nasir Umar, kotun ta shigar da ƙarar "ba su amsa laifi ba" a madadin kamfanonin, sannan aka fara sauraron shari'ar.

A yayin shari'ar, masu gabatar da ƙara sun dogara da shaidu da takardun da ke cikin bayanan shari'ar, ciki har da rahotannin sirri, bayanan jami'an bincike, takardun bincike da amsoshin da aka samu daga CAC da SEC.

Bayan gabatar da shaidun, Mai shari'a Anyalewa Onoja-Alapa ta samu kamfanonin da laifin tare da yanke musu hukuncin tarar Naira miliyan 30 kowannensu.

A cewar EFCC, binciken ya biyo bayan wasu bayanan sirri da hukumar ta samu waɗanda suka alaƙanta kamfanonin da zargin damfarar masu zuba jari da kuma gudanar da harkokin zuba jari ba tare da lasisi ba.

Hukumar ta ce ta gayyaci masu kamfanonin domin yi musu tambayoyi a 22 ga Disamba 2022, sannan ta sake gayyatar su a 12 ga Janairu 2023, amma ba su zo ba.

EFCC ta ce daga bisani sun ci gaba da kaucewa ganawa da jami'an binciken na tsawon lokaci, lamarin da ya kai ga gurfanar da kamfanonin a kotu.

Zamba da safarar mutane da sunan QNET

Dubban mutane a faɗin Afirka ta Yamma suna faɗawa cikin wata zamba ta safarar mutane, wadda aka fi sani da sunan QNET.

An kafa QNET a Hong Kong, amma asali kamfani ne na halal da ke harkar kayayyakin lafiya. Kamfanin yana bai wa mutane damar yin rajista domin sayen kayayyakinsa da kuma sayar da su ta yanar gizo.

Sai dai tsarin kasuwancin kamfanin ya fuskanci suka daga wasu ɓangarori. A Afirka ta Yamma kuwa, wasu ƙungiyoyin masu aikata laifuka suna amfani da sunan QNET a matsayin kafar kasuwancin bayan fage.

Masu safarar mutane suna farautar mutane ne ta hanyar yi musu alƙawarin samun guraben aiki a kasashe kamar Amurka da Canada da Dubai da wasu ƙasashen Turai.

Suna neman waɗanda aka yaudara su biya maƙudan kuɗaɗe da ake bayyana su a matsayin kuɗin gudanar da harkokin aiki ko wasu kuɗaɗen gudanarwa kafin su fara aikin.

Bayan sun biya kuɗin, sau da yawa ana safarar su zuwa wata ƙasa maƙwabciya. Daga nan sai a faɗa musu cewa ba za su iya tafiya zuwa ƙasashen da aka yi musu alƙawari ba har sai sun shigo da wasu mutane cikin wannan tsarin.

Amma ko da sun shawo kan ƴan uwansu da abokansu suka shigo cikin tsarin, ayyukan da aka yi musu alƙawari ba sa samuwa a lokuta da dama.

A baya kamfanin QNET ya ƙaddamar da wani gangamin wayar da kan jama'a a faɗin yankin, inda a cikin kamfanin ya riƙa gangamin mai taken "QNET Against Scams", wato "QNET na yaƙi da Zamba."

Kamfanin ya kuma yi watsi da zarge-zargen da ake yi masa na cewa yana da alaƙa da safarar mutane.