Abu huɗu da suka sauƙaƙa rayuwar ƴan Najeriya bayan ƴancin kai

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A ranar 1 ga Oktoba na shekarar 1960 ce Najeriya ta samu ƴancin kai daga hannun turawan Birtaniya bayan kwashe shekaru ƙasar da ƴan ƙasar suna ƙarƙashin mulkin mallaka.
A duk ranar ta 1 ga watan Oktoba, ana guganar da bukukuwa a faɗin ƙasar domin tunawa da ranar.
A lokuta da dama, a kan tattaunawa abubuwa da dama da suka shafi cigaban ƙasa ko ma akasin, duk da cewa ana yawan mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi komawa baya da ƴan ƙasar suke ganin tana fuskanta.
Sai dai kamar masu iya magana ke cewa a cikin ido ake tsawurya, daga wancan lokaci zuwa yanzu, rayuwar ƴan Najeriya ta sauya a ɓangaorin rayuwar ta yau da kullum.
A yau, bayan fiye da shekara 60, fasaha ta kawo sauye-sauye da dama da suka sa rayuwa ta yi sauƙin gudanarwa.
BBC ta yi nazari tare da rairayo wasu ɓangarorin rayuwar ƴan Najeriya da za a iya cewa an samu cigaba tare da samun sauƙin gudanar da su.
Harkar sadarwa

Asalin hoton, Getty Images
Daga muhimman ɓangarorin da aka samu matuƙar sauyi a Najeriya akwai batun sadarwa.
Kafin samun ƴancin kai, sadarwa na cikin abubuwa da suka fi wahala a Najeriya. A lokacin an fi ta'allaƙa da wayoyin tarho da ake tangaraho, kuma sun fi yawa a ofisoshi da ma'aikatun gwamnati da manyan birane.
A wani rahoton babban bankin Najeriya, a shekarar 1960, Najeriya tana da kusan layukan waya 18,724 ne kacal, a lokacin da da aka ƙiyasta akwai kusan miliyan 40 a ƙasar, sannan kuma yawancin musayar waya na lokacin na amfani da tsarin hannu ne, inda ma'aikaci ke taimakawa wajen haɗa kira.
Wannan ya sa a lokacin aƙalla mutum 12,128 na ƴan ƙasar ne suke amfani da wayar tarho guda ɗaya.
Yawanci a lokacin an fi amfani da aike wajen isar da saƙo, sannan ake amfani da ofishin saƙon ofishi na kar ta kwana.
Najeriya a yau yanayin ya sauya sosai. Wayar hannu ta zama wani ɓangare na rayuwar yau da kullum. Mutum zai iya kira, aika saƙon WhatsApp, yin wayar bidiyo da aika hoto ko amfani da intanet, sannan saƙo ya isa cikin ƴan daƙiƙa.
Abin da wannan ya nuna sadarwa ta sauya daga kasancewa abu mai wuya da tsada zuwa kasancewa abu mai sauri kuma kusa da kowa, musamman ga mutanen da ke da wayar hannu da damar intanet da sauran su.
Hada-hadar kuɗi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kafin lokacin ƴancin kai, tsarin banki yana nan amma bai kai yadda yake yau ba, don haka sai ya kasance hada-hadar kuɗi na da wahalar gaske, musamman a tsakanin masu ƙaramin ƙarfi.
Rahoton CBN a watan Disamban shekarar 1960 ya nuna yadda a lokacin da ake tunanin an samu gagarumar cigaba, inda a lokacin aka ce adadin rassan bankuna ya ƙaru daga 44 zuwa 200, yayin da ajiyar bankuna ta kai kusan fam miliyan 70.
Duk da wannan ci gaba, yawancin harkokin yau da kullum sun dogara ne kan tsabar kuɗi. Yawanci ana hada-hada ne ta hanyar zuwa da tsadar kuɗi hannu da hannu, musamman zuwa kasuwanci da sauran hada-hadar yau da kullum.
Sai dai duk da haka a lokacin, waɗanda suke da asusun bankin ma suna fuskantar wahala wajen hada-hada da bankunan, kasancewar a lokacin babu ATM, babu manhajar bankuna a wayoyin salula ballanta POS, waɗanda duk suka sauƙaƙa hada-hadar kuɗi a yanzu.
Najeriya a yau, mutum zai iya yin abubuwa da dama ba tare da shiga banki ba. Misali: Tura kuɗi daga waya zuwa wani asusu. Biyan kuɗin wutar lantarki ko wasu kuɗaɗe ta intanet. Amfani da ATM d POS da sauran su.
Wannan sauyi ya sa hada-hadar kuɗi ta zama mafi sauri kuma ya buɗe damar shiga tsarin kuɗi ga mutane da yawa.
Sufuri

Asalin hoton, Getty Images
A lokacin ƴancin kai, jirgin ƙasa, motoci, jiragen ruwa da sauran hanyoyin sufuri su ne manyan hanyoyin sufurin mutane da kayayyaki daga wani waje zuwa wani wajen, musamman mai nisa.
Layin dogo ya kasance muhimmin ɓangare na tattalin arzikin ƙasar. An gina shi musamman domin haɗa yankunan cikin gida da tashoshin jiragen ruwa da kuma jigilar kayayyaki kamar kayan amfanin gona.
Wani rahoton bankin duniya na watan Janairun 1964 ya nuna cewa a shekarar 1960 akwai kusan motoci 58,000, yayin da hanyar mota ta kasance muhimmin ɓangare na jigilar kayayyaki a faɗin ƙasar.
Rahoton ya ƙara da cewa daga cikin motocin akwai na safa guda 28,000, sannan a lokacin kimanin mil 45,500 kawai na tituna a ƙasar, sannan daga ciki, mil 7,700 ne kawai akwai kwalta.
Haka kuma akwai ƙoƙarin da aka fara a lokacin na tsawaita layin dogon ƙasar daga mil 2,180.
A yau, hanyoyin sufuri sun fi yawa kuma kusan yawanci na zamani ne, sannan mutane suna amfani da: Motoci da bas-bas domin sufuri da babura da kekuna a wasu wurare.
Sannan jiragen ƙasa na zamani suna aiki, bayan kuma jiragen sama da na ruwa da suke aiki a ɓangarorin ƙasar da dama.
Misali, a shekarun baya, tafiya a jirgin ƙasa suna kwanaki a hanya a tafiyar da ake yin sa'o'i kaɗan a yanzu.
Daga cikin manyan hanyoyin jiragen ƙasa da suke jan hankali a Najeriya akwai layin jirgin ƙasa na Abuja–Kaduna da Lagos–Ibadan.
Sannan a yanzu an samu sabuwar manhajar sufuri, inda mutum zai iya amfani da wayarsa wajen neman mota ya yi amfani da taswira, motar ta gano wurin da yake, sannan direba ya zo ya ɗauke shi, sannan su je wajen za su je, ko kuwa ba su san wajen ba.
Sai dai a ɓangaren sufuri ma har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin duk da ci gaban, Najeriya har yanzu tana fuskantar matsaloli kamar cunkoson ababen hawa, lalacewar wasu tituna da tsadar sufuri.
Wani rahoton bankin duniya ya bayyana cewa tituna ne ke ɗaukar babban kaso na zirga-zirgar ƙasar, yayin da bukatar inganta wasu hanyoyin sufuri da haɗa su da juna ta ci gaba da kasancewa muhimmiyar magana.
Noma

Asalin hoton, Getty Images
Noma yana ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan tattalin arzikin Najeriya a lokacin samun ƴancin kai.
A wancan lokaci, Najeriya ta shahara wajen samar da gyada, koko, dabino, auduga, roba da sauran amfanin gona.
A farkon shekarun 1960, kayayyakin noma sun kasance babban ɓangare na abubuwan da Najeriya ke fitarwa zuwa ƙasashen waje.
Misali: Arewa ta shahara wajen gyaɗa da auduga, yammacin Najeriya ta shahara wajen koko, sannan yankunan Kudu sun shahara wajen dabino da kwakwar mai da sauran su.
A wancan lokaci, yawancin manoma suna amfani da kayan aikin gargajiya wanen noma, inda aikin ya fi dogaro da ƙarfin mutum da dabba, maimakon manyan injuna na noma.
A Najeriya a yanzu, harkokin noma sun bunƙasa, musamman a ɓangaren kasuwancin ababen noma.
Yanzu akwai matasa har ma da mata da suka ɗauki harkokin noma a matsayin sana'arsu, inda har ake nazartarsa a jami'o'i.
Haka kuma yanzu an samu cigaba da sauƙin noma, inda ake amfani da taraktoci da sauran injinan noma da fasaha wajen ban-ruwa da inganta iri da takin zamani da amfani da fasaha wajen binciken yanayin kasuwanci.
Haka kuma akwai noma da ake iya amfani da fasaha wajen noma ɗimbin amfanin gona a ƙaramar gona, maimakon wahalar da ake sha a baya wajen noma manyan gonaki.



























