Ƙasashe sun yi kakkausar suka kan harin Houthi a Madina

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashe da dama sun yi kakkausar suka kan harin da 'yan Houthi suka kai wata tashar rarraba wutar lantarki a birnin Madina na Saudiyya.
Turkiyya da Pakistan sun yi allahwadai da harin, tare da bayyana goyon bayansu ga Saudiyya.
Haka kuma, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Bahrain, Kuwait, Jordan, Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da Ƙungiyar Haɗin Kan Musulunci sun yi tur da harin, suna mai bayyana kai hari a Madina a matsayin "keta ƴancin Saudiyya ƙarara."
Mai magana da yawun rundunar ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta, Turki al-Maliki, ya ce harin ya lalata tashar rarraba wutar lantarki ta birnin.
Ya ce "Bincike da shaidun da hukumomin da abin ya shafa suka tattara, bayan nazarin abin da ya faru da kuma ɓurɓushin jirgin mara matuƙi da aka yi amfani da shi, sun tabbatar da hannun 'yan Houthi wajen tsarawa da aiwatar da wannan hari."
Al-Maliki ya ce harin ya sa ɗaya daga cikin na'urorin sauya ƙarfin wutar lantarki daina aiki, amma hakan bai haifar da katsewar wutar lantarki mai yawa ba.
Ya ƙara da cewa tashar tana samar da wutar lantarki ga Masallacin Annabi SAW, yana mai bayyana harin a matsayin "ci gaba da yunƙurin mayaƙai na kai hari kan Masallatai Masu Alfarma Biyu."

















