Matar da aka yi wa allurar kisa sau biyu amma ba ta mutu ba

..
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

An garzaya da wata fursuna da ke jiran hukuncin kisa a jihar Tennessee ta Amurka, Christa Pike, zuwa asibiti bayan yunkurin zartar mata da hukuncin kisa ta hanyar allura ya ci tura, lamarin da ya haifar da sabon ce-ce-ku-ce kan yadda ake aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar.

Lauyoyinta sun yi gaggawar neman kotu ta dakatar da hukuncin a daidai lokacin da jami'ai ke ƙoƙarin aiwatar da shi, bayan da Pike ta suma amma zuciyarta ta ci gaba da bugawa.

An kai ta asibiti domin kula da lafiyarta bayan an yi mata allurai biyu na sinadarin pentobarbital, maganin da ake amfani da shi wajen aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar allura.

An samu matsala yayin aiwatar da hukuncin

..

An yanke wa Pike hukuncin kisa ne a shekarar 1996 bayan an same ta da laifin kashe wata budurwa mai suna Colleen Slemmer, mai shekara 19.

Sai dai lokacin da aka yi ƙoƙarin aiwatar da hukuncin a gidan yarin Riverbend da ke birnin Nashville, abubuwa ba su tafi yadda aka tsara ba.

A cewar lauyoyinta, bayan an yi mata allurai biyu na pentobarbital, Pike ta rasa hayyacinta, amma zuciyarta ta ci gaba da bugawa, har ma ana jin tana minshari.

Nan take lauyoyinta suka garzaya kotu suna neman a dakatar da hukuncin tare da umartar jami'an lafiya su ba ta kulawar gaggawa.

Wani alkalin tarayya, Clifton Corker, ya ce tuni ma'aikatan lafiya suka fara ba Pike kulawar da lauyoyinta suka nema.

Daga bisani kuma aka garzaya da ita asibiti, inda lauyanta ya ce likitoci na ƙoƙarin ceton rayuwarta.

Tambayoyi kan tasirin maganin

Wani ƙwararren likita da lauyoyinta suka ɗauka ya bayyana cewa mai yiyuwa ne adadin maganin da ya shiga jikinta bai isa ya katse numfashi da aikin zuciyarta gaba ɗaya ba.

Lamarin ya sa aka fara tambayar ko an yi amfani da maganin yadda ya kamata, da kuma ko tsarin aiwatar da hukuncin ya samu matsala.

Gwamna ya ba da umarnin bincike

Bayan faruwar lamarin, gwamnan jihar Tennessee, Bill Lee, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa domin gano abin da ya faru.

Ya kuma sanar da cewa ba za a ci gaba da aiwatar da sauran hukuncin kisa da aka shirya yi a jihar kafin ƙarshen shekara ba har sai an kammala binciken.

Sai dai hukumar kula da gidajen yarin Tennessee ta ce tana goyon bayan dukkan matakan da jami'anta suka ɗauka yayin yunkurin aiwatar da hukuncin.

Ba shi ne karo na farko ba

Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun matsala wajen aiwatar da hukuncin kisa a Tennessee ba.

A watan Mayu, an dakatar da hukuncin kisa kan wani fursuna mai suna Tony Carruthers bayan jami'ai sun kasa samun jijiyar da za su yi masa allurar kisa.

Shari'ar da ta dauki lokaci mai tsawo

..
Bayanan hoto, An yi wa Colleen Slemmer azabtarwa tare da kashe ta a mummunan yanayi a kisan da aka yi mata a shekarar 1995

An shafe shekaru ana ta fafatawar shari'a kan hukuncin Pike.

Kotun Kolin Amurka ta yi watsi da bukatun da lauyoyinta suka gabatar na dakatar da hukuncin, duk da hujjojin da suka gabatar.

Lauyoyin sun kuma yi ikirarin cewa lokacin da aka yanke mata hukuncin kisa, ba a yi cikakken nazari kan irin cin zarafin da ta fuskanta tun tana yarinya ba.

Pike tana da shekara 18 lokacin da ita da saurayinta na lokacin suka kashe Colleen Slemmer bayan sun haɗu a wani sansanin horas da matasa.

Mahaifiyar mamaciyar, May Martinez, wadda ta shafe shekaru tana jiran ganin an aiwatar da hukuncin, ta bayyana abin da ya faru a matsayin lamari mai matuƙar rikitarwa.

Tun bayan dawo da hukuncin kisa a Amurka a shekarar 1976, mata 18 kacal aka zartar wa hukuncin kisa, idan aka kwatanta da maza sama da 1,600 da aka kashe a ƙarƙashin irin wannan hukunci.