''Ba a yi adalci in aka ce matsalar tsaro ta taɓarɓare a mulkin Tinubu ba''

Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, ASOROK VILLA

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da 'yan Najeriya da dama ke ci gaba da kokawa kan matsalar tsaron da ake fama da ita a kasar a shekaru uku na farko na mulkin shugaba Tinubu, fadar shugaban kasar ta dage cewa lallai ana samun nasara a kokarin yaki da matsalar.

A cewar wani mai magana da yawun shugaba Tinubu Abdulaziz Abdulaziz, duk da cewa da gaske ana samun garkuwa da mutane, to amma lamarin bai kai yadda aka gani kafin hawansa karagar mulki a shekarar 2023 ba.

A cewarsa ''Bana jin an yi adalci idan aka ce matsalar tsaro na tabarbarewa a mulkin Tinubu, watakila dai a ce tana kara fadada, mun sani ba ma jin dadi, kuma ba wai muna watsi da halin da wadanda suke cikin matsalar suke bane, gwamnati ba ta jin dadi, amma idan ka duba abun da aka saba samu a baya, tsananin abun, ka ji an ce an shiga gari daya an sace mutum dari biyu, an je nan gari an kashe mutum 50 lokaci daya, ko ka ji an an tashi gari an watsa shi, yanzu ana samun irin haka jifa-jifa, amma ba irin manyan hare haren da za ka ji an ce an sace ko an kashe mutane da yawa kamar yadda take faruwa a baya ba''.

Ya ce hatta satar mutanen da ake samu a yanzu sai dai a sace kalilan amma ba wai da yawa kamar yadda ake samu a baya ba.

''A yanzu sai dai ka ji an saci yara 26, nan an saci yara 42, ba shakka ko mutum daya aka sace abu ne na takaici, amma ka tuna an saci yara 300 a baya an shiga da su daji, an dauki mutane dari biyu da wani abu a jirgin kasa wata da watanni ba a iya gano su ba, amma a wannan gwamnatin ba yadda za ka ji an ce an sace yara ba a yi kokari cikin kankanin lokaci an ceto su ba'' inji shi.

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce duk da ƙoƙarin jami'an tsaro, har yanzu akwai buƙatar ƙarin matakai domin dawo da cikakken zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

A gefe guda kuma, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa tattalin arziƙin Nijeriya na nuna alamun farfaɗowa a hankali sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin ta aiwatar tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023.

A cewar gwamnati, matakan da aka ɗauka sun taimaka wajen ceto ƙasar daga matsananciyar matsalar tattalin arziƙi da ka iya jefa ta cikin durƙushewa, duk da cewa miliyoyin 'yan Najeriya sun fuskanci tsadar rayuwa da matsin tattalin arziƙi a cikin shekaru ukun da suka gabata.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shi dai shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya cika shekara uku a kan mulki a ƙarshen watan Mayu, ya fara mulkinsa da wasu manyan sauye-sauye da suka haɗa da cire tallafin man fetur da kuma sassauta tsarin canjin kuɗi ta yadda darajar naira za ta rinƙa ƙayyadewa bisa ga yanayin kasuwa.

Sai dai Abdulaziz Abdulaziz, ya ce shugaba Tinubu ya yi abun da ba a taba yi ba a Najeriya wajen daukar matakan da suka zama wajibi duk da cewa za su haifar da radadi na dan wani lokaci.

''Masana da ma wasu gwamnatocin baya sun sha cewa lallai idan ana son ci gaba dole ne a tsayar da tallafin man fetur din nan, maimakon a rika bayar da tallafi a kan abun da ana kone shi kuma gobe sai an koma an sha, gara abayar da tallafi a harkar samar da tattalin arziki mai dorewa''.

Ya ce a yanzu, ana amfani da tallafin da ake bayarwa na man fetur wajen bayar da tallafi ga harkar noma, da tallafin karatun dalibai da sauran muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar jama'a kai tsaye.

Cire tallafin man fetur da ya haifar da tashin farashin fetur daga ƙasa da naira 200 kan kowace lita zuwa sama da 1000. Haka kuma, sauyin tsarin canjin kuɗi ya janyo faduwar darajar naira, lamarin da ya ƙara tsadar kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Masana tattalin arziƙi sun bayyana cewa waɗannan matakai sun kasance masu wahala amma suna daga cikin gyare-gyaren da ake ganin sun zama wajibi domin rage nauyin da ke kan baitul malin gwamnati da kuma ƙarfafa zuba jari.

Sai dai masu suka suna ganin cewa gwamnati ta kasa samar da isassun matakan kariya ga talakawa kafin aiwatar da sauye-sauyen, wanda ya sa dubban iyalai suka shiga cikin mawuyacin hali.

Duk da ikirarin gwamnati na samun ci gaba, 'yan Nijeriya da dama na ci gaba da kokawa kan hauhawar farashin kayayyaki, tsadar sufuri da kuma raguwar ƙarfin sayen kayan masarufi.

Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a sassan ƙasar, yayin da albashin ma'aikata da kuɗaɗen shiga na yawancin gidaje suka kasa tafiya daidai da hauhawar farashin da ake fuskanta.

To sai dai jami'an gwamnatin tarayya sun dage cewa sauye-sauyen da aka fara aiwatarwa suna buƙatar lokaci kafin amfaninsu ya bayyana sosai ga talakawa. Sun ce alamomin da ake gani a wasu fannoni na tattalin arziƙi na nuna cewa ƙasar na kan hanyar samun daidaito da bunƙasa.

Sai dai jama'a da kungiyoyin farar hula na ci gaba da kira ga gwamnati da ta ɗauki ƙarin matakan rage raɗaɗin tsadar rayuwa tare da magance matsalar tsaro da rashin aikin yi.

Yayin da Shugaba Tinubu ya shiga shekararsa ta huɗu a mulki, idanuwan 'yan Nijeriya na ci gaba da kallon ko sauye-sauyen da gwamnatin ta fara za su haifar da sauƙin rayuwa da ci gaban da ake fata ga al'ummar ƙasar.