Me ya sauya tun bayan da Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya?

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, Ton Molina/Getty Images)

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shafe shekara uku a kan mulki, kuma ƴan Najeriya na ta tsokaci kan abubuwan da shugaban ya yi tun bayan da ya kama mulki.

Tinubu shi ne shugaban ƙasa na biyar tun bayan komawar Najeriya ta farkin dimokuraɗiyya a shekarar ta 1999 - bayan ya lashe zaɓe a shekarar 2023.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne aka rantsar da Tinubu, to amma ana ci gaba da muhawara kan ko Tinubu ya yi wani abin a zo a gani tun daga wancan lokaci.

Ƴan Najeriya da dama na kokawa kan abubuwa da yawa, wanda ya haɗa da rashin tsaro da rashin aikin yi da tsadar man fetur da zubewar darajar naira da yunwa da ma wasu abubuwan da dama.

Sai dai a lokacin wani jawabi da ya yi wa al'ummar Najeriya na cika shekara uku da hawa kan mulki, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta kawo ci gaba a fannoni da dama.

Sai dai ya faɗi cewa har yanzu gwamnatinsa ba ta kammala warware matsalolin da ƙasar ke fama da su ba.

Shugaba Tinubu ya ce har yanzu abinci na da rahusa, kuma ya ce tattalin arziƙin Najeriya ya haɓɓaka fiye da yanda ya iske shi a shekarar 2023.

  • Farashin abinci
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƴan Najeriya ba su wasa da harkar abinci, domin wajibi ne ɗan'adam ya ci abinci, kuma farashin abinci a kasuwa shi ne zai tantance abin da mutum zai iya ci.

Mun duba yadda farashin wasu kayan abinci yake kafin Tinubu ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2023, da kuma farashin da ake samun su a wannan shekara ta 2026, shekara uku bayan ya hau mulki.

A shekarar 2023, akan sayar da doya ɗaya a wasu wuraren na Najeriya kan farashin naira 800 kacal, amma ya zuwa cikin shekara ta 2024 doya ɗaya ta kai kimanin naira 3,000.

Kuma har yanzu a ashekarar 2026 farashin doya ya ƙi saukowa, inda yanzu ake sayar da lafiyayyar doya ɗaya kan naira 5,000 a wasu wauraren.

Garin kwaki, ɗaya daga cikin abinci mafi farin jini a Najeriya, farashin robar fenti a 2023 na kamawa ne kimanin naira 500, amma yanzu ya haura naira 2,000 a wasu wuraren.

Yanzu farashin robar fenti ta shinkafa a kasuwa na kamawa ne daga naira 7,000 zuwa 8,000.

Tashin farashi na daga cikin abubuwan da Tinubu ya sha alwashin magancewa a lokacin yaƙin neman zaɓensa na 2023, amma yanzu bayan shekara uku, a bayyane take cewa farashin abubuwa da dama sun yi tashin gwauron zabo ne, maimakon sauka.

  • Tsaro

A lokacin bikin rantsar da Tinubu a 2023, shugaban ya ce tsaro zai zama babban abin da gwamnatinsa za ta sanya a gaba.

Ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali sosai wajen bunƙasa yawan jami'an tsaro da horas da su da kuma inganta albashinsu.

Shekara uku bayan haka, Najeriya na ci gaba da fama da matsanancin matsalar tsaro - abin da ya haɗa da garkuwa da mutane, a gida ko a kan hanya ko a makaranta ko kuma wuraren ibada - da kuma matsalar hare-haren Boko Haram.

Ga matsalar rikicin manoma da makiyaya, lamarin da ya kai ga cewa Amurka ta ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta bayan zargin muzguna wa kiristoci.

  • Tallafin man fetur

A halin yanzu farashin man fetur sai ɗagawa yake yi a Najerya, inda a wasu wurare ake sayar da man fetur ɗin kan naira 1,350 a kan lita ɗaya.

Shugaban Tinubu na ci gaba da tutiya da matakinsa na cire tallafin man fetur, inda yake iƙirarin cewa tallafin ya fi amfanar masu kuɗi a kan talaka.

"Ba za mu iya bayar da hujjar ƙarin kuɗin da ake narkarwa a harkar tallafi ba," in ji Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2026.

To amma bayan cire tallafin man fetur ɗin, abin da ake gani shi ne tamkar nauyin ya koma ne kan mutanen da ke sayen fetur ɗin na yau da kullum.

Duk da irin alƙawarin da aka sha yi, har yanzu Najeriya ba ta da wata nagartacciyar matatan man fetur ta gwamnati da ke aiki.

Me ƴan Najeriya ke cewa?

BBC ta tuntuɓi wasu ƴan Najeriya don jin mene ne ra'ayinsu game da gwamnatin Tinubu tun bayan da ya karɓi mulki.

Bashar Abubakar, mazaunin cikin birnin Zazzau ya ce "a gaskiya mulkin Tinubu ya ƙara jefa mu cikin matsala, ya yi alƙawari da yawa, kuma mun yi masa kyakkyawan zato saboda mun yi tunanin cewa shi ƙwararre ne, to amma abin ya ƙi gyaruwa, na rasa daga ina matsalar take."

Shi kuwa Godspoer Olorunsanumi cewa ya yi abubuwa da dama sun sauya a cikin shekara uku ta mulkin Tinubu.

"Tattalin arziƙinmu ya ɗan samu sauyi kadan daga yadda yake a baya. Muna sa ran za a samu ci gaba a nan gaba, to amma mutane na cikin wahala saboda tashin farashi.

Ya ƙara da cewa Tinubu ya kawo shirye-shiryen bunƙasa ƙasa ta hanyar fara ayyukan tituna a ɓangarorin ƙasa da dama..

"A ɓangaren ilimi, an rage samun yaje-yajen aikin malaman jami'o'i, ina ganin muna kan hanya mai kyawu."

Sai dai ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro a cikin ƙasar yana tayar da hankali, amma yana sa ran za a samu sauƙi.

David Toluwase ya ce ya ga alamar sauyi a ɓangaren tattalin arziƙi a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

"Ƙasar ta samu muhimman sauye-sauye a ɓangaren tattalin arziƙi wanda ya sanya aka samu sauƙi a fannin canjin kuɗi, sai dai hakan na haifar da tashin farashin kaya a tsakanin al'umma.'

David ya ce ya kamata a ce manufofin Tinubu su kawo sassauci ga al'umma to amma babu tsari mai kyau na walwala.

Ya ce duk da Najeriya ta ɗan samu ci gaba ta wasu fannonin amma rashin tsaro babban matsala ce, kuma yana lalacewa.

David ya ce kasancewar ƴan Najeriya na cikin fargaba game da rayukansu, ya kamata Tinubu ya ɗauki mataki a wannan ɓangare.

Shi kuma Olaleye Komolafe ya koka ne kan taɓarɓarewar walwalar al'umma sanadiyyar cire tallafin man fetur.

"Wannan shi ne wani abin kirki guda ɗaya tilo da talaka ke amfana da shi daga gwamnati. Cire shi ya karya hanyar samun abin rayuwa na al'umma saboda haka kusan komai ya sauya tun daga wancan lokacin."

A yanzu mutane sun talauce fiye da yadda suke a shekarar 2023."

Ya kuma yi tsokaci kan mataslaar tsaro wadda ta yi sanadiyyar rayukan mutane da dama a ƙarƙashin wannan gwamnati.

Wani mai sharhi kan harkokin yau da kullum Ayobami Akinola ya ce babban abin da ya fi addabar ƴan Najeriya a ƙarƙashin wannan gwamnati shi ne matsalar tsaro.

Ya ce rashin tsaro na ƙaruwa. Wannan a cewarsa ya ƙara a kan sauran matsalolin da ƴan Najeriya ke fama da su, kuma wajibi ne Tinubu ya magance shi.

"Mutane ba su buƙatar a ba su bayanin abin da ke faruwa a bayan fage, abin da suke so shi ne su ga alamar cewa gwamnati na aiki, su ga cewa akwai matakai da ake ɗauka, kuma a riƙa ɗaukar matakai a lokacin da ya kamata kuma a riƙa hukunta masu laifi."

Mutumin ya yi nuni da abin da ya faru a baya-bayan nan, inda aka sace ɗalibai a wata makaranta da ke jihar Oyo, haka nan ma an sace wasu a jihar Borno.

"Ba matsalar jami'an tsaro ba ne. Matsalar ita ce yadda aka tsara harkar tsaron ƙasar, ya fi mayar da hankali kan wani abu daban."

Dukkanin waɗannan ra'ayoyin da ƴan Najeriya suka bayyana na nuna cewa ƙarara, gwamnatin Tinubu na da tarin matsaloli a gabanta da suka kamata ta magance - kuma yayin da ake tunkarar babban zaɓen ƙasar na 2027, ƴan Najeriya za su fi son su ga an ɗauki mataki a aikace, maimakon alƙawari a baki.