Asibitin da mata ke haihuwa a kan tabarma a jihar Sokoto

Asibiti
Bayanan hoto, Badawa Primary Health Care
    • Marubuci, Abubakar Maccido
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Al'ummar Badawa, wani ƙauye da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Boɗinga ta jihar Sokoto na cikin wani yanayin da ya tilasta su yin kira ga hukumominsu da su kai musu dauki ta hanyar gyara musu asibitinsu wanda ya kwashe shekaru cikin mummunan hali.

Mazauna garin dai sun ce asibitin ya lalace ce bayan wata guguwa da ta yi awon gaba da wani ɓangare na asibitin shekaru 10 da suka gabata.

Kuma tun wannan lokacin ne al'ummar garin suka ce aka yi banza da asibitin ba tare da samun gyara ba duk kuwa da ƙorafi da suka yi wa hukumomin lafiya.

Wani mazaunin garin na Badawa ya shaida wa BBC cewa " da dama da cikin ɗakunan ba su da rufi, katangun sun tsage sannan wasu sassan asibitin ne kawai ake amfani da su wajen kula da marasa lafiya."

Ya kuma ƙara da cewa hakan ya sa samun kulawar lafiya ya zama abu mai matuƙar wahala ga al'ummar yankin musamman marasa lafiya.

Mazauna garin sun ce dubban marasa lafiya na ziyartar asibitin a kowane wata.

"Baya ga al'ummar garin Badawa, marasa lafiya daga ƙauyuka masu maƙwabtaka na zuwa asibitin domin neman lafiya kasancewarsa asibiti mafi kusa da su," in ji wani mazaunin garin.

Duk da yawan mutanen da ke ziyartar asibitin, mutanen garin da Bodinga sun ce likitoci biyu ne kawai suke ganin marasa lafiya.

Bugu da ƙari, mazauna garin sun ce ana kula da marasa lafiya ne a kan tabarma kasancewar babu gadaje a asibitin.

Mutanen sun ce al'amarin ya fi shafar mata masu ciki da ke buƙatar kulawa ta musamman a lokacin haihuwa wani abun da ya fi ci musu tuwo a ƙwarya.

Mata da dama a kan tabarmar suka haihu.

Tarin takardu
Bayanan hoto, One of di rooms wia dem dey treat patients
wani daki da rufinsa ya lalace

"Wannan asibitin ya daɗe da lalacewa. Lokacin da aka fara gina wani sabon sashen sai mutane suka fara murnar cewa za a gyara asibitin to amma har kawo yanzu ba su gyara ba. Asibitin ya kwashe shekaru 10 da lalacewa," in ji Rabi wata unguwar zoma da ke taimakon mata a lokacin haihuwa.

"A duk lokacin da mata masu ciki suka zo musamman waɗanda suke naƙuda muna kai su ɗakin da yake da ragowar rufi. Sai mu shimfida musu tabarma a ƙasa tunda babu gado. To yaya za mu yi tunda babu gado?

Rabi ta ce ta taimaka wa mata fiye da guda biyar da suka haihu a wannan yanayi a asibitin.

"A yanzu na karɓi haihuwar mata kamar biyar. Kullum muna ƙorafi ga hukumomi kuma jami'an gwamnati na zuwa nan domin ganewa idanunsu halin da asibitin ke ciki. Suna kawo mana tabarmi da wasu kayan aikin asibiti."

Bandaki lalatacce
Bayanan hoto, Di health facility toilet
Gini lalatacce

Lokacin da wakilin BBC ya nemi shiga cikin ginin domin ganewa idanunsu halin da asibitin ke ciki to amma wani ma'aikacin asibitin ya hana hakan duk da cewa wakilin ya samu wasu hotunan ginin.

Martanin gwamnatin Sokoto

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To sai dai kwamishinan lafiya na jihar Sokoto, Kaftin Farouk Umar Abubakar ya ce a yanzu haka sun gyara asibitocin da ke karkara 160 kuma suna ci gaba da gyaran sauran.

"Muna da asibitoci 240 kuma yanzu mun gyara 160. Za mu ci gaba da gyaran sauran ciki har da Badau wanda ya lalace tun 2015. Ba ma shi kaɗai ba da dama daga cikin asibitocin na karkara haka suke kuma za mu gyara su a tsanake."

Muna da kasafi na ci gaba da gyaran su har da wannan asibitin a wannan shekarar da muke ciki kuma in Allah ya so za a gyara ta a kuma inganta ta...duk asibitocin namu da muka gyara sai mun saka musu solar da borehole domin a samu wuta da ruwa ba tare da yankewa ba," in ji Kaftin Farouk.

Dangane kuma da sauran manyan asibitoci a faɗin jihar, kwamishinan ya ce:

"Muna da manyan asibitoci 25 a jihar Sokoto kuma daga cikinsu mun gyara 15. Yanzu kuma gwamna ya amince da a gyara sauran...yanzu a kowane lokaci majalisar zartarwa ta zauna za a ji labarin bada iznin gyaran sauran asibitocin."

Tsohon gini lalatacce
Ginin asibiti