Yadda wasu 'yan APC ke zargin gwamnoni da wawushe fom na takara

APC

Asalin hoton, APC NIGERIA

Bayanan hoto, APC
Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fara shirye-shiryen tunkarar zaben 2027, batun mallakar fom din takara na neman haifar da rudani a jam'iyyar.

Wasu yan jam'iyyar ta APC sun zargi gwamnoni da shugabannin jam'iyyar da son zuciya ta hanyar wawushe fom din takarar a matakai da dama domin raba su ga wadanda suke so.

Tun dai lokacin da jam'iyyar APC ta fara sayar da fom din takara, wasu yan jam'iyyar suka fara korafi da nuna damuwa kan zargin da suke ana fifita wasu, wani abu da wasu ke hangen zai iya yaga jam'iyyar.

Hon Musa Aliyu Khalid, jigo a jam'iyyar APC a jihar Kaduna ya shaida wa BBC Hausa cewa dole ne jam'iyya ta ba wa kowa dama ya sayi fom din takara ba wai a ba wa gwamnoni su sanya wadanda suke so ba.

''Ka ga yanzu yadda ake tafiya wa'yansu suna zuwa ne a ce shugaban jama'iyya ya ce, wasu su ce gwamnoni, wasu su ce wane ya ce, to ka ga duk wannan bai kamata ba, ya kamata a ce an ba wa kowa dama sannan a yi zaben cikin gida wanda ya fi goyon bayan jama'a ya samu.

Haka ma tsohon kakakin majalisar jiha a Kaduna Hon Yusuf Ibrahim Zailani wandake cikin masu nuna damuwa game da abun da ke faruwa, ya yi gargadin cewa hakan na iya kawowa APC koma baya.

A cewarsa ''Mu dai mun san cewa shugaban kasa Tinubu na cikin wadanda suka tabbatar da dimukradiyya a Najeriya, kuma shi dan siyasa ne wanda da mai jama'a ya ke mu'amula, kuma na san ba wanda zai zare masa ido, don haka in har za a yi abun da ya ce to masu jama'a ne za su samu''

Ya kara da cewa ''Akwai kura inda aka ce za a rubuta dan takara wanda bai da mutane, shi ya samuke kira ga shugabanni su ji tsoron Allah a bar mutane su zabi abun da suke so.

''Muna kokarin ganin an tabbatar da adalci''

Nentawe Yilwatda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban jam'iyyar APC Nentawe Yilwatda
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To sai shugabancin jam'iyyar APC ya ce an shimfida tsari na tabbatar da adalci.

Bala Ibrahim, daraktan watsa labarai na jam'iyyar APCn na kasa ya ce magana ce ta ana gudun son zuciya, don haka duk wanda ke da sha'awa zai bi ka'idojin jama'iyya da kuma na hukumar zabe.

''Duk wanda yake da sha'awa kuma ya cika ka'ida za a fafata da shi, idan an samu maslaha shikenan, inda kuma ba a samu ba za a je a yi zabe kato bayan kato, in ya so wanda duk ya ci, to farin jikinsa ne ya sa, ba wai soyayyar wani gwamna ko wani uban gida ba'' INJI SHI.

Dama dai masu sharhi dai sun dade suna hasashen cewa yadda APC ta cika ta batse za ta iya fuskantar kalulabe musamman idan an zo gabar tsayar da yantakara.

Dama dai a Najeriya an jima ana zargin gwamnoni da saye foma-foman takara na jama'iyyunsu ba wai kawa a APC kadai ba, domin bayar da su ga wadanda suke so su yi takarar mukamai daban-daban a lokacin zabe, wani abu da ke yawan haifar da rigingimu,.