Me ya sa yawancin mutanen da ke tara ƙwanji ke mutuwa da wuri?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Stephanie Rodrigues
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
A farkon wannan watan, Mailson Araújo ya wallafa hotonsa a ɗakin motsa jiki kamar yadda ya saba, inda yake nuna irin ƙaƙƙarfan jikinsa da ya sa ya zama fitaccen mai gina jiki da kuma yana da tasiri a kafafen sada zumunta, inda yake da dubban mabiya.
Ya sanya da jajayen kaya, yana nuna manyan damatsen hannayensa irin na jaruman fina-finai.
Sai dai cikin sa'o'i kaɗan bayan wallafa hoton, Araújo ɗan ƙasar Brazil mai shekara 35 ya rasu bayan rashin lafiya a gidansa da ke jihar Bahia a arewa maso gabashin ƙasar.
Har yanzu ba a tabbatar da musabbabin mutuwarsa ba, amma Araújo na cikin jerin masu tara ƙwanji da suka yi mutuwar ba-zata a ƴan shekarun nan.
A ƙarshen watan Mayu ma, Gabriel Ganley, ɗaya daga cikin fitattun matasa masu gina jiki a Brazil, ya rasu yana da shekara 22 sakamakon bugun zuciya fara-ɗaya. A bara kuma wasu masu gina jiki biyu ƴan Brazil masu shekaru 30 da 40 sun mutu sakamakon matsalolin zuciya, inda ɗaya daga cikinsu ya rasu a lokacin wata gasa.
Irin waɗannan mutuwar ba a yi Brazil kaɗai take faruwa ba.
A Amurka, Dallas McCarver ya rasu a shekarar 2017 yana da shekara 26, yayin da wani fitaccen mai gina jiki a Jamus, Jo Lindner, shi ma ya mutu a shekarar 2023 yana da shekara 30.
Hakan ya sa ake ta tambaya: me ya sa wasu masu gina jiki, waɗanda ake ganin suna cikin ƙoshin lafiya da ƙarfin jiki, ke mutuwa kwatsam tun sunamatsakaitan?
Me ya sa wasu masu gina jiki ke mutuwa da wuri?

Asalin hoton, Maddie Meyer/Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani bincike da aka wallafa a shekarar 2025 ya yi nazari kan haɗarin da ke tattare da yawan gina jiki da tara ƙwanji, inda masu bincike suka bibiyi kusan masu gina jiki 20,000, waɗanda suka haɗa da ƙwararru da masu farawa, da suka shiga gasar da hukumar kula da wasan ta shirya tsakanin shekarun 2005 zuwa 2020.
Binciken, wanda aka wallafa a mujallar European Heart Journal, ya gano cewa ƙwararrun masu gina jiki sun fi fuskantar haɗarin mutuwa ta farat-ɗaya sakamakon bugun zuciya – fiye da waɗanda suke farawa - wato lokacin da zuciya ke daina bugawa ba zato ba tsammani.
Irin wannan mutuwa ta farat-ɗaya ba kasafai take faruwa ga matasa masu ƙoshin lafiya ba, kuma galibi tana da alaƙa da wata matsalar zuciya.
Binciken ya gano mutum 121 da suka mutu, inda 46 da aka tabbatar sun mutu ne sakamakon bugun zuciya.
Waɗanda suka mutu suna da matsakaitan shekarun da ba su wuce 45 ba, amma daga cikin ƴan wasa, akwai waɗanda ba su wuce shekaru 34 ba.
Jagoran binciken, Dakta Marco Vecchiato na Jami'ar Padova da ke Italiya, ya ce akwai abubuwa da dama da ka iya taimakawa wajen haddasa waɗannan mace-macen.
"Daga ciki akwai yawaitar amfani da magungunan ƙara ƙarfi da gina tsoka, rage nauyi cikin gaggawa kafin gasa da kuma tsananin atisayen ɗaga nauyi" in ji shi.
Wani bincike da masu nazari daga Denmark suka wallafa a mujallar Circulation a 2025 ya bibiyi maza 1,189 da aka sani suna amfani da sinadaran anabolic steroids, tare da kwatanta su da kusan maza 60,000 daga cikin al'umma tsawon shekara 11.
Binciken ya nuna cewa masu amfani da waɗannan sinadarai sun fi sauran mutane kusan kamuwa da cutar cardiomyopathy, wadda ke raunana tsokar zuciya. Haka kuma suna cikin haɗarin bugun zuciya.
Baya ga sauran matsalolin lafiya kamar raguwar yawan maniyyi da matsalar rashin ƙarfin mazakuta, sinadarin anabolic steroids na iya ƙara hawan jini, sa kitse ya taru a jijiyoyin jini, da kuma sauya bugunn zuciyar mutum.
Masu binciken sun kuma duba sakamakon gwaje-gwajen gawarwakin wasu daga cikin masu gina jiki da suka mutu.
A lokuta da dama, an gano cewa zukatansu sun yi girma fiye da kima, tare da ƙara kaurin tsokar da ke tura jini daga zuciya, abin da ke ƙara haɗarin bugun zuciya ba daidai ba.
A wasu lokutan kuma, gwaje-gwajen sinadarai da rahotannin jama'a sun nuna alamun amfani da anabolic steroids, duk da cewa ba kasafai ake binciken irin waɗannan sinadarai a gwajin gawa ba.
Sakamakon gwajin gawar wasu matasa masu gina jiki da suka mutu sun sha nuna cewa zukatansu sun yi girma fiye da yadda ya kamata.
Ɗaya daga cikin shahararrun misalan shi ne ɗan wasan gina jiki na Amurka Dallas McCarver, wanda ya rasu a shekarar 2017 yana da shekara 26. Gwajin gawarsa ya nuna cewa zuciyarsa tana da nauyin gram 833, fiye da ninki biyu na nauyin da ake sa ran zuciyar namiji za ta kasance da shi.

Asalin hoton, Bispo & Zago, 2024, Arquivos Brasileiros de Cardiologia (CC BY)
Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2022 kan sakamakon gwajin gawar wasu masu gina jiki a Amurka ya gano cewa, zukatansu sun fi girman yadda ya kamata ya ya kasance da kusan kashi 74%, kuma kauran tsokar zuciya ya ƙar da kashi 125%.
A wani bincike na daban kuma, masu bincike sun duba rahotannin gwajin gawa daga Italiya da Sifaniya da suka shafi masu gina jiki da ake alaƙanta su da amfani da sinadaran anabolic steroids.
A lokuta da dama, an gano cewa matasa masu shekaru tsakanin 20 zuwa 29 suna da manyan zukata, kaurin tsokar zuciya mai da kuma toshewar jijiyoyin zuciya.
A wani rahoto, wani mai gina jiki ɗan shekara 24 ya samu toshewar fiye da kashi 75% a manyan jijiyoyin zuciyarsa, duk da cewa babu tarihin cututtukan zuciya a gidansu.
"Zuciya tsoka ce kamar kowace tsoka a jiki.," in ji likitan wasanni, Clayton Macedo
"A kullum idan na ga girman damtsen hannun mara lafiya, zan iya hasashen girman zuciyarsa, saboda tana girma ne tare da sauran tsokokin jiki."
Masana sun ce motsa jiki da ɗaga nauyi ba tare da amfani da sinadaran ƙara ƙarfi ba na iya sa zuciya ta ɗan ƙaru, kuma hakan wata dabi'ar ƴan wasa ce.
Sai dai shugaban ƙungiyar likitocin zuciya ta Brazil a jihar Bahia, Luiz Eduardo Fonteles Ritt, ya ce idan aka haɗa amfani da anabolic steroids da yawan atisayen ɗaga nauyi, zuciya na iya girma, har ta fara rasa ƙarfin bugawa yadda ya kamata.
"Hakan na iya haifar da gazawar zuciya, kuma daga baya ya kai ga matakin da ba za a iya ɗaukar mataki ba," in ji shi.
Sai dai Ritt ya yi gargaɗin cewa ba a kowane lokaci kaurin zuciya ke da alaƙa da amfani da sinadaran ƙara ƙarfi ba.
"Akwai wani yanayi da ba a iya tabbatar da musabbabinsa kai tsaye. Wataƙila cutar zuciya ce ta gado, ko kuma ta samo asali ne daga amfani da sinadaran ƙara ƙarfi, ko kuma yawan atisaye ko kuma ma haɗuwar dukkan waɗannan abubuwa uku."
Amfani da sinadaran ƙara ƙarfi na da haɗari

Asalin hoton, Rodrigo Góes
Tsohon ɗan wasan gina jiki, Rodrigo Góes, ya shaida wa BBC cewa ya riƙa shiga gasar ba tare da amfani da sinadaran ƙara ƙarfi ba har sai da ya kai shekara 30, kafin daga bisani ya fara amfani da anabolic steroids bisa kulawar likita.
Haka na nufin amfani da waɗannan sinadarai na tsawon wasu makonni, sannan a dakata domin bai wa jiki damar murmurewa kafin a sake komawa amfani da su.
"Suna da tasiri a jiki sosai," in ji shi.
"Kana girma cikin sauri fiye da yadda yake a ɗabi'ance. Jiki kuma na ƙara sirancewa, yayin da tsokoki ke murmurewa cikin gaggawa. Shi ya sa mutane da yawa ke fadawa tarkonsu."

Asalin hoton, Rodrigo Góes
Sai dai ya ce duk da cewa duk da ba ya amfani da sinadaran sosai kuma yana yi ne a ƙarƙashin kulawar likita, ya fuskanci matsaloli da suka haɗa da zubar gashi, damuwa, rashin barci da kuma yawan zufa da dare.
Amma ya ce matsalar da ta fi addabarsa ita ce ta yawan tunani.
"Ban taɓa jin daɗin yadda nake yawan yi wa kaina allura ba. A wani lokaci ina ji kamar ni mai shaye-shaye ne. Da wuya a faɗi haka, amma ina ji cewa ina aikata abin da bai dace ba."
A yanzu Góes na wayar da kan jama'a kan haɗarin amfani da sinadaran ƙara ƙarfi
"Babu wata hanya mai aminci ta amfani da anabolic steroids. Abin da likitoci za su iya yi kawai shi ne rage illolin da suke haifarwa, amma ba za su hana waɗannan illolin faruwa gaba ɗaya ba."
Me ya sa aka kasa gano adadin mutuwar da ke da alaƙa da sinadaran?
Ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke tattare da amfani da sinadaran ƙara ƙarfi shi ne cewa ƙasashe da dama ba sa da cikakkun tsare-tsaren bibiyar mace-macen da sinadaran ke haddasawa.
A Brazil, babu alƙaluma a hukumance da ke nuna yawan mutanen da suka mutu sakamakon amfani da anabolic steroids. Haka kuma wasu ƙasashe da dama ba sa rubuta amfani da sinadaaran a matsayin dalilin mutuwa.
A maimakon haka, galibi ana bayyana dalilin mutuwa ne bisa matsalar da ta bayyana kai tsaye, kamar bugun zuciya, shanyewar jiki ko cutar da ke raunana tsokar zuciya, ba tare da la'akari da tasirin magungunan ƙara ƙarfi ba.
Masu binciken gawarwaki sun ce amfani da sinadan kan yi tasiri ba tare da an gano shi ba, saboda waɗannan sinadarai suna kama da sinadaran da jiki ke samarwa, lamarin da ke sa gano su bayan mutuwa yake da wahala.
Saboda waɗannan dalilai, masana sun ce yana da wahala a iya tantance ainihin adadin mutuwar da amfani da magungunan ƙara ƙarfi ya haddasa.
"Ina samunn irin waɗannan bayanai a kullum. in ji Macedo.
"Zan iya kallon damtsen hannun mutum kuma in fahimci abin da ke faruwa. Abin takaici, idan na ga irin waɗannan manyan tsokoki, sau da yawa nakan fahimci cewa zuciyar mutumin ta riga ta samu matsala ko kuma tana fara fuskantar matsala. Sau da yawa, sakamakon yana bayyana ne daga baya."
Ƙarin rahotanni daga Luis Barrucho











