Mun sa hannu kan takardar sadaukar da biyu bisa uku na dukiyar mahaifinmu - Halima Ɗangote

Asalin hoton, Getty Images
Attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, na shirin ba da kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa ga ayyukan jin ƙai a matsayin wani ɓangare na tsarin gadon dukiyarsa, kamar yadda ƴarsa, Halima Dangote, ta bayyana.
Halima, wadda ke cikin amintattun mambobin Gidauniyar Aliko Dangote, ta bayyana hakan ne a wata hira da kafar watsa labarai ta Bloomberg a ranar Talata.
Ta ce Dangote ya samu amincewar iyalansa kan ware kashi 33 na dukiyarsa domin ayyukan jin ƙai.
Arzikin attajirin dai ya kai dala biliyan 35.1, wanda ke nufin idan har wannan adadin ya ci gaba da kasancewa haka, kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa zai kai kusan dala biliyan 11.7.
Da take bayyana dalilin wannan mataki, Halima ta ce mahaifinta yana kallon ayyukan jin ƙai a matsayin ginshiƙin abin da zai bari a bayansa, kuma ya haɗa hakan cikin tsarin yadda za a gudanar da dukiyarsa bayan rasuwarsa.
A cewarta, "ya riga ya tsara komai ta yadda muka fi mayar da hankali kan harkokin lafiya da ilimi. A zahiri ya ba da kashi 25 ga gidauniyar. Idan ka duba lamarin, akwai tsarin da Shari'ar Musulunci ta tanada, idan ka yi nazari za ka ga ana nufin ya ware kashi 33 na duk abin da zai bari a matsayin gado ke nan ga ya zama waƙafi ga gidauniyarsa.
"Hakan yana nuna irin muhimmancin da yake bai wa ayyukan jin ƙai, domin yana son su ci gaba daga tsara zuwa tsara.
"Saboda haka, taimakon al'umma wani ɓangare na abin da muka fahimci muhimmancinsa. Mun yi imani cewa nasarar kasuwancinmu tana da alaƙa da irin taimakon al'umma da muke yi. Wannan ne ya sa kyautar da wannan kashi 33 ɗin yake da matuƙar muhimmanci."

Asalin hoton, X/Dangote
Halima ta ƙara da cewa wannan ya sa mahaifin nasu ya buƙace ta da sauran ƴanuwanta biyu su saka hannu.
"Da ni da ƴan'uwana biyu da mahaifiyarsa mun saka hannu a yarjejeniyar ta kyautar da kashi 33 ɗin domin ayyukan jin ƙai," in ji ta a tattaunawar.
A wata tattaunawar kuma Mariya Dangote, wadda ita ƴa ce ga attajirin ta bayyana cewa rukunin kamfanonin na yunƙurin sayar da hannun jarin ɓangaren siminti na kamfanin a kasuwar hannun jarin London.
Ta ce sun muhimmantar da kasuwar hannun jarin London ce sama da ta Dubai saboda a cewarta ta London ta fi dacewa da kasuwancinsu.
"Mun gwada kasuwannin hannun jari da dama, amma sai muka fahimci cewa, sai muka fahimci zai fi kyau mu je ta London," in ji Mariya a wata tattaunar daban da kafar Bloomberg.
Dukiyar Aliko Dangote
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haifa Aliko Mohammad Dangote ne a ranar 10 ga Afrilun 1957, a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.
Dangote ne shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote (Dangote Group) da Matatar Dangote.
Ya zuwa Mayun 2026, Dangote wanda ɗan asalin jihar Kano ne, shi ne mutum na 62 mafi arziki a duniya, amma shi ne baƙin fata mafi arziki a duniya sannan kuma mutum mafi arziki a Afirka, inda mujallar Bloomberg ta ƙiyasta dukiyarsa ta haura dala biliyan 36.8.
A shekarar 1977, Dangote ya kafa rukunin kamfanonin, wanda ya fara kasuwancin saye da sayar da kayayyaki, musamman shigo da sukari, gishiri da kayayyakin abinci.
Daga bisani, a shekarar 1981, ya kafa Dangote Nigeria Limited da kuma Blue Star Services, waɗanda suka riƙa shigo da shinkafa da kuma albarkatun masana'antu kamar ƙarafa.
Bayan kasuwancinsa ya bunƙasa ne Dangote ya kafa Dangote Cement, wanda ya shiga harkar siminti, sannan daga baya da ya ƙara gawurta sai ya assasa matatarsa ta mai, wadda ta ƙara jan hankalin duniya.
A shekarar 2011, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya karrama shi da lambar girmamawa ta ƙasa ta GCON.
Haka kuma, a shekarar 2014, mujallar Time ta saka sunansa cikin jerin mutane 100 mafi tasiri a duniya.











