Spurs za ta kashe Fam Miliyan 125 kan Gibbs, United na harin Mesloub

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham Hotspur ta shirya siyen ɗan wasan Notthingham Forest Morgan Gibbs-White kan fam miliyan 125 a watan January mai zuwan, bayan da da kusa daukar dan wasan a kakar siyen dan wasan a 2025. (Football Insider)
Manchester United na harin ɗan wasan Lens Mezian Mesloub, a yunƙurinsu na ƙara ƙarfin ƙungiyar da matasa masu hazaƙa. (Teamtalk)
United na son ci gaba da riƙe ɗan wasan Ingila JJ Gabriel, da ake ta danganta shi da komawa Real Madrid ko Bercelona, yayin da Chelsea ita ma ta shiga sahum masu zawarci ɗan wasan. (Teamtalk)
Manchester United na sa ido kan Antonio Conte, a mastayin wanda zai maye gurbin Michael Carrick, inda har baa sami wani ci gaba ba kan yadda ya ke tafi da ƙungiyar. (Hard Tackle)
Ac Milan da Juventus su ma na harin Conte da ke jirin tayin d aya kwnata masa, kafin ya bar Napoli a kakar wasannin nan. (Calciomercato - in Italian)
Atletico Madrid sun sabunta aniyarsu na son ɗaukar ɗan wasan Bayer Leverkusen, ibrahim Maza, a yunƙurinsu na karfafa ƴan wasan tsakiyar ƙungiyar. (Goal)
Liverpool, da Manchester City, da Fulham, da Tottenham na cikin ƙungiyoyin da ke buga Firimiya da ke sa ido kan dan wasan Venezula da Real Sociedad Jon Aramburu. (Teamtalk)
Liverpool ta fara tattaunawa da Monaco kan Lamine Camara, 22, don ganin sun siye shi nan da watan Janairu. (Caughtoffside)
Arsenal na son ɗan wasan Borussia Dortmund Maximilian Beier. (Teamtalk)
Newcastle na gogayya da Barcelona kan ɗan wasan Djurgarden Bo Hegland, 22. (Football Insider)










