Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 20/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji

Rahoto kai-tsaye

Daga Isiyaku Muhammed da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Tattalin arzikin Iran na fuskantar ƙalubale saboda yaƙi da takunkumi

    Iran

    Asalin hoton, IRNA

    Sabbin alƙaluman gwamnati daga Iran sun nuna cewa tattalin arzikin ƙasar na ci gaba da fuskantar ƙalubale sakamakon yaƙin da take yi da Amurka da kuma takunkuman tattalin arziki da aka ƙaƙaba mata.

    Bisa ga bayanan, yawan kuɗaɗen da ƙasar ke samarwa a cikin gida (GDP) ya ragu da sama da kashi 10 cikin 100 idan aka kwatanta da na bara.

    Haka kuma, kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa ƙasashen waje sun ragu da fiye da kashi ɗaya bisa uku, yayin da Amurka ke ci gaba da matsa mata lamba ta hanyar takunkuman tattalin arziki.

    Kazalika, hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ta ƙaru sosai, inda ta kai aƙalla kashi 70 cikin 100, lamarin da ke ƙara tsananta wa al'ummar ƙasar matsin rayuwa.

    Masana na ganin waɗannan alamu na nuna irin girman tasirin yaƙi da takunkuman da ke addabar tattalin arzikin Iran.

  2. Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Atiku/X

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa bai halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) ba karo na uku a jere.

    A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Lahadi, Atiku ya ce rashin halartar taron sau uku a jere abu ne da ya saɓa ƙa'ida, wanda hakan na iya yin tasiri ga hulɗar Najeriya da ƙasashen duniya..

    Ya ce akwai buƙatar fadar shugaban ƙasa ta fayyace ko akwai wani abin da ke hana Tinubu zuwa Amurka, domin "ƴan Najeriya na da haƙƙin sanin dalilin rashin halartar taron sau uku a jere".

    Ya bayyana cewa taron UNGA na ɗaya daga cikin muhimman wuraren da shugabannin ƙasashe ke tattauna batutuwan tsaro, kasuwanci da ci gaba tare da neman jari da haɗin gwiwa da sauran ƙasashe.

    A cewarsa, duk da cewa Shettima na iya wakiltar Najeriya, amma bai kamata hakan ya maye gurbin kasancewar shugaban ƙasa da kansa ba.

    Atiku ya kuma yi zargin cewa wataƙila ko tsohuwar shari'ar "ƙwace kadarori" da gwamnatin Amurka ta taɓa gudanarwa kan wasu kuɗaɗe da ake dangantawa da Tinubu a shekarun 1990, "dalilin da ke sanya shugaban ƙasar gujewa halartar tarukan a ƙasar Amurka".

    Ya kuma ɗiga ayar tambaya kan rahotannin da ke cewa an tanadar wa Tinubu kujera kusa da Shugaban Amurka Donald Trump a taron, amma daga ƙarshe ya ƙi halarta.

    Tinubu bai halarci zaman Majalisar Ɗinkin Duniya na shekarun 2024, 2025 da 2026 ba, inda a kowanne lokaci yake tura Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilce shi.

  3. Tinubu ya tura Shettima ya wakilci Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka

    Kashin Shettima

    Asalin hoton, Kashin Shettima

    Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi da jagorantar tawagar Najeriya zuwa babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 81 da za a yi a birnin New York na ƙasar Amurka.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shettima ya bayyana cewa tawagar za ta haɗa da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati.

    An shirya gudanar da muhawarar babban taron na UNGA daga ranar 22 zuwa 28 ga Satumban 2026.

    Ana sa ran Najeriya za ta yi amfani da taron wajen bayyana matsayinta kan muhimman batutuwan duniya da suka shafi tsaro, ci gaba da tattalin arziki.

  4. Iran ta sanar da harbo jirgin leƙen asiri mara matuƙi a Mashigar Hormuz

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Iran ta ce dakarun kare sararin samaniyarta sun harbo wani jirgin leƙen asiri na zamani mara matuƙi mai suna Orbiter a mashigar Hormuz.

    A wata sanarwa da sashen hulɗa da jama'a na rundunar ya fitar ranar Lahadi, sojojin sun ce an harbo jirgin ne da misalin ƙarfe 6:30 na yamma agogon ƙasar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun kare sararin samaniyar Iran ne suka kai harin a yankin kudu maso gabashin ƙasar, inda suka lalata jirgin gaba ɗaya.

    Sai dai sanarwar ba ta bayyana ƙasar da jirgin ya fito ko kuma wanda yake gudanar da shi ba.

    Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa da jigilar man fetur a duniya.

  5. Ƴan Houthi sun amince ba za su kai hari kan Amurka ba - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce mayaƙan Houthis na Yemen sun amince cewa ba za su kai hare-hare kan Amurka ba.

    Kafar yaɗa labarai ta Fox News ya rawaito Trump yana cewa Amurka na ci gaba da tuntuɓar Houthi, kuma ƙungiyar ta amince ba za ta yi faɗa da Amurka ba.

    Rahotannin Reuters sun ce wakilan ɓangarorin biyu sun kuma gana a birnin Muscat a kwanakin baya-bayan nan, yayin da Houthi suka bayyana cewa ba za su kai hare-hare kan jiragen ruwa na Amurka ba.

    Houthi, waɗanda ke samun goyon bayan Iran, na ci gaba da yaƙi da Saudiyya, ɗaya daga cikin manyan abokan hulɗar Amurka a yankin.

    A watan Mayun 2025, Amurka da Houthi sun cimma yarjejeniyar tsagaita kai wa juna hari ta hanyar sasancin ƙasar Oman.

  6. APC ta ƙalubalanci Atiku ya yi bayani dalla-dalla kan yadda zai dawo da tallafin mai

    Tinubu da Atiku

    Asalin hoton, FB/Multiple

    Jam’iyyar APC ta buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi cikakken bayani kan yadda yake shirin aiwatar da abin da ya kira "tallafin samar da man fetur a matatun cikin gida domin rage farashin fetur".

    A cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Dele Alake, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce akwai ayar tambaya game da shirin Atiku a tsarin doka da tattalin arziki da ya kamata ya amsa.

    APC ta ce ya kamata ɗantakarar jam'iyyar adawa ta ADCn ya bayyana yadda shirin zai yi aiki ƙarƙashin Dokar Man Fetur (PIA), da kuma yadda zai tabbatar da rage farashin fetur ga masu amfani.

    Jam’iyyar ta kuma buƙaci ya bayyana kuɗin da za a kashe wajen aiwatar da shirin, daga inda kuɗaɗen za su fito, da hanyoyin da za a bi wajen hana karkatar da tallafin ko safarar mai zuwa ƙasashe maƙwabta.

    APC ta ce Atiku ya taɓa sukar tsarin tallafin fetur a baya tare da alƙawarin kawo ƙarshensa, don haka ya kamata ya yi bayanin dalilin da ya sa yanzu yake goyon bayan dawo da wani nau’in tallafi.

    Jam’iyyar ta ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fi mayar da hankali kan samar da hanyoyin sufuri masu amfani da iskar gas da lantarki, maimakon komawa tsarin tallafin fetur.

    A cewar APC, har sai Atiku ya gabatar da cikakken bayani dalla-dalla kan yadda shirinsa zai yi aiki da kuma kuɗin da zai laƙume za ta fahimta, domin yanzu alƙawari ne kawai ya yi da bai fayyace yadda za a aiwatar da shi ba.

  7. Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma'adinai 37 da suka rasu Neja

    Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC ta buƙaci a tabbatar da adalci tare da biyan diyya ga iyalan masu haƙar ma'adinai 37 da suka mutu yayin da suke tsare a hannun hukumar tsaro da kare fararen hula ta Najeriya, NSCDC, a Jihar Neja.

    A wata sanarwa da shugaban MURIC na jihar Kano, Malam Hassan Sani Indabawa, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce ta damu da yadda mutanen suka mutu bayan kama su a wani samame da aka kai kan masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

    MURIC ta ce idan zarge-zarge da ake yi wa hukumomin sun tabbata, hakan na nuna rashin ƙwarewa da rashin mutunta rayuwar ɗan'adam daga jami'an.

    Ƙungiyar ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yarjejeniyoyin kare haƙƙin bil'adama na duniya sun tanadi kare rayuwa da mutuncin mutanen da ke hannun jami'an tsaro.

    Ta kuma nuna damuwa kan abin da ta kira yawaitar zarge-zargen take haƙƙin bil'adama da ake dangantawa da wasu jami'an NSCDC a sassan ƙasar.

    A ƙarshe, ƙungiyar ta buƙaci a tabbatar da adalci ga mamatan tare da biyan diyya ga iyalansu.

  8. An kashe ƴar jarida da ta shiga takarar zaɓen ƙananan hukumomi a Peru

    Peru

    Asalin hoton, Getty Images

    An kashe wata yar jarida kuma yar takara a zaben kananan hukumomi a kasar Peru yayin da ta ke gudanar da yakin neman zabe.

    Wani mutum da ba a san ko wanene ba ya bindige Susy Aponte Polo, mai shekaru 44, a wata kasuwa da ke garin Caraz a yankin Ancash da ke gabar teku.

    Wakilin BBC ya ce: Sa'o'i kadan kafin lokacin, ta wallafa cewa ta samu sakonnin barazanar kisa daga wasu mutane da ke tsare a gidan yari, amma ba ta yi wani karin bayani kan barazanar ba.

    Yayin yakin neman zabenta gabanin zaben da za a yi a wata mai zuwa, ta yi zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka shafi 'yan takara daga jam'iyyar masu hamayya da ita, da kuma jami'an 'yan sandan yankin.

  9. Rasha ta ce harin jirgi mara matuƙi ya yi ajalin mutum biyu a Moscow

    Putin

    Asalin hoton, AFP

    Kafofin yaɗa labaran gwamnatin Rasha sun bayar da rahoton cewa mutum biyu sun mutu sakamakon hare-haren jiragen sama marasa matuƙa na Ukraine a birnin Moscow.

    Rahotannin sun ce an kuma kai hari kan matatar mai da ke babban birnin kasar.

    Hare-haren sun faru ne a jajibirin zaben majalisar dokokin Rasha.

    Magajin garin Moscow ya ce hare-haren sun lalata wasu sassan matatar man fetur ta Moscow, tare da dakatar da zirga-zirgar sama na jirage sama da 30.

    Ya kuma ce an kai hare-haren ne da nufin yin tasiri kan zaben.

    Hare-haren sun ci gaba duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a makon da ya gabata Rasha da Ukraine sun amince da cewa ba za su rika kai wa wuraren samar da mai na juna hari ba.

    An cimma wannan yarjejeniya ne a daidai lokacin da duniya ke fuskantar matsalar man fetur da makamashi.

  10. 'Babu wanda zai iya kare abin da aka aikata a Gaza'

    Waka

    Asalin hoton, Getty Images

    Sharaharren mawaƙi ɗan Birtaniya Ed Sheeran ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin bala'i mai tsanani inda ya ce babu wata hujjar da za a bayar domin kare abubuwan da aka aikata a yankin.

    Sheeran ya yi wannan jawabi ne kafin fara wasansa na farko tun bayan da aka cire mawakin rap Macklemore daga jerin masu rakiyarsa a rangadin wasannin da yake yi a Amurka, sakamakon kalamansa na nuna goyon baya ga Falasɗinawa yayin da ya ke kan dandamalin wasa.

    Sheeran ya ce: "Abin da ke faruwa a Gaza ba ƙaramin bala'i ba ne kuma ba za a iya kare shi ba, ina baƙin cikin abubuwan da ake yi da ke haddasa mutuwar fararen hula, musammamn kananan yara," in ji shi.

    Bayan cire Macklemore daga jerin masu wasa a wannan rangadin, dukkan wadanda ke taya Sheeran wasa sun janye.

  11. Atisaye 4 da ke taimakawa wajen ƙarfafa wuyan hannu

    Hannu

    Asalin hoton, Getty Images

    Rayuwar yau da kullum tana matuƙar ɗaura wa wuyan hannayenmu nauyi.

    A wajena, ya fara ne da ɗan ƙaramin ciwo. A cikin watannin bazara, sai ciwon ya ƙaru da sauri har ya zama ya yi tsanani a hannuna, sannan yana bazuwa zuwa tafin hannun hagu a duk lokacin da na buga ƙwallon tenis, ko ma lokacin da na yi ƙoƙarin buɗe ƙofa.

    A lokacin ina da shekara 18, kuma wasan tenis wani muhimmin ɓangare ne na rayuwata.

  12. Saudiyya ta tabbatar da harin mayaƙan Houthi a Riyadh

    Houthi

    Asalin hoton, Getty Images

    Saudiyya ta tabbatar da cewa mayaƙan Houthi na Yemen sun yi yunƙurin kai hari kan birnin Riyadh, babban birnin kasar, da makami mai linzami.

    Wannan shi ne harin farko da aka kai kan Riyadh tun bayan tsanantar faɗa da ake yi tsakanin Saudiyya da mayaƙan Houthi.

    A baya, mayaƙan Houthi sun yi amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa wajen kai hare-hare kan wasu wurare masu matukar muhimmanci a Riyadh.

    Sai dai Saudi Arabiya ta ce ta “kawar da makamin mai linzamin tare da lalata shi” kafin ya isa inda aka nufa.

    Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito cewa wasu mazauna Riyadh sun ji karar fashewa, daga bisani kuma suka ga wani hayaki na tashi kusa da filin jirgin saman birnin.

    Mayaƙan Houthi dai na iko da wani babban ɓangare na Yemen, kuma a baya-bayan nan sun ƙwace wasu biranen bakin teku da ke kusa da mashigin Bab al-Mandab da wasu tsibiransa.

    A ranar Asabar, Amurka ta yi gargaɗin cewa rikicin tsakanin Saudiyya da mayaƙan Houthi, waɗanda Iran ke marawa baya, na iya “tsananta cikin gaggawa.”

  13. 'Ana samun ƙaruwar miyagun ƙwayoyi a Scotland'

    Hukumar kula da magunguna ta nahiyar Turai ta bayyana cewa, ana ci gaba da samun bullar sabbin miyagun kwayoyi masu matukar karfi a Scotland, lamarin da ke kawo cikas ga kokarin rage yawan mace-macen da ke da alaka da ta'ammali da miyagun kwayoyi.

    Hukumar ta ce an samu karuwar yaduwar wasu nau'ukan kwayoyi cikin a Scotland, wadanda karfinsu zai iya ninka na hodar iblis kusan sau dari.

    Wakilin BBC ya ce Scotland ce ƙasar da ta fi samun yawan mace-mace masu alaka da miyagun ƙwayoyi a Turai - kuma masana kimiyya da ma'aikatan agaji da 'yan sanda sun ce kwararar sabbin kwayoyi na ƙara ta'azzara lamarin.

  14. Dole Amurka ta kasance a gaban China a fasahar AI - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai kafa hukumar kula da fasahar AI, sannan ya naɗa sabon mai ba da shawara kan harkokin da suka shafi fasahar don daidaita ɓangaren.

    A saƙon da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya ce ba zai hana ci gaban fasahar AI ba, yana mai jaddada cewa dole ne Amurka ta ci gaba da shigewa gaban China a bunƙasa fasahar.

    Wannan matakin ya biyo bayan damuwar da shugabannin masana'antar da ma'aikata da dama ke nunawa cewa fasahar AI barazana ce ga bil'adama.

    Wannnan naɗi dai shi zai zama na biyu da Shugaba Trump zai yi - bayan ɗan kasuwa David Sacks ya sauka daga irin wannan muƙamin a watan Maris.

  15. Iran ta sake aika sharuɗɗan kawo ƙarshen yaƙi ga Amurka

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Mohammad Baqer Qalibaf ya soki masu ra'ayin da ke ƙoƙarin jefa ƙasar cikin “yaƙin da babu raar ƙarewa.” Sannan ya kuma tabbatar da cewa Iran ta aika da saƙonni da kuma sharuɗanta ga Amurka ta hannun masu shiga tsakani.

    A wani jawabi gabanin zaman majalisar dokokin Iran, shugaban majalisar ya ce wasu “suna magana ne kan yaƙi amma ba su da wani tsari ko hanyar da za a kawo ƙarshensa.”

    Ya ce irin wannan ra'ayi, ta hanyar ƙin amincewa da duk wata mu'amala ko diflomasiyya ba tare da yin la'akari da yiwuwar abubuwan da za su iya faruwa ba, “a zahiri yana jefa ƙasar cikin tsananin yaƙi da ba shi da iyaka.”

    “Dole ne mu yi yaƙi, amma a gefe kuma mu riƙa shiga tattaunawa,” in ji shi.

    Mista Qalibaf ya kuma jaddada cewa: “An isar da saƙonni tare da bayyana sharuɗɗanmu ga ɗaya ɓangaren ta hannun masu shiga tsakani.”

    Ya ce matuƙar ba a cika sharuɗɗan da Iran ta gindaya ba, “ba za a koma kan tsarin shawarwarin da aka yi a baya ba, kuma ba za a bude mashigar Hormuz ba.”

    A jiya, Mohsen Rezaei, sakataren Majalisar Tsaron Iran, ya sanar da cewa Tehran ta isar da sharuɗɗunta na tattaunawa ga Amurka ta hannun masu shiga tsakani daga Qatar da Pakistan.

    Ya ce yanzu Iran na “jiran martanin Shugaba Trump.”

  16. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya.

    Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo da kuma yin muhawara.

    Ku kasance tare da mu.