Hanyoyin da AI zai shafi zaɓen Najeriya na 2027

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Yayin da Najeriya ke shirin babban zaben shekarar 2027, wata sabuwar barazana ta fara ɗaukar hankalin hukumomi da masana: Ƙirƙirarriyar basira (AI) da yadda za a iya amfani da ita wajen yaɗa bayanan ƙarya, sauya hotuna da bidiyo, ko ma kwaikwayon muryar ƴan siyasa.
A kwanaki baya ne shugaban INEC Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya ce sahihancin zaɓe bai dogara da na'urorin fasaha kamar BVAS da takardun sakamako kaɗai ba, inda ya ce har da yadda ƴan Najeriya ke fahimtar bayanan da suka shafi zaɓe da kuma yadda suke amincewa da su.
A wani jawabi da aka gabatar a madadinsa a taron shekara-shekara na 13 na Ƙungiyar masana sadarwa da ƙwararrun masu hulɗa da jama'a ta Najeriya a kwanakin baya, ya ce ya kamata a shigar fasahar sadarwa cikin harkokin gudanar da zaɓen ƙasar.
Ya kuma yi gargadin cewa ƙirƙirarriyar basira da ake amfani da ita wajen samar da bayanan ƙarya na iya zama babbar barazana ga sahihancin zaɓe.
A cewarsa, sabuwar AI ta sauƙaƙa samar da bidiyoyi, muryoyi da hotuna na bogi, tare da kara wahalar gano abin da yake na gaskiya.
Amupitan ya ce matsalar ba ta tsaya ga ƙirƙirar bayanan ƙarya kai tsaye ba, domin ana iya amfani da dabarun kwamfuta wajen aika saƙonni daban-daban ga wasu rukunin masu kaɗa ƙuri'a.
Shin AI zai iya sata ko canza sakamakon zabe?
Wannan na daga cikin tambayoyin da ke yawan tasowa yayin da ake magana kan tasirin AI a zaɓen 2027.
Sai dai Malam Muhammad Ubale Kiru, malami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma masani kan fasahar AI da tsaron yanar gizo, ya ce akwai buƙatar a bambanta tsakanin fasahar AI da za ta yi kutse kai-tsaye cikin tsarin zaɓe, da kuma fasahar AI da za a yi amfani da ita wajen tasiri kan tunanin masu kaɗa ƙuri'a.
A cewarsa, babu wata hujja a halin yanzu da ke nuna cewa fasahar AI da kanta za ta iya shiga cikin tsarin INEC ta canza sakamakon ƙuri'un da aka tattara.
Amma ya ce babbar barazanar da ake iya gani ita ce amfani da AI wajen samar da bayanan ƙarya kafin zaɓe da lokacin zaɓe, musamman a kafafen sada zumunta.
"A yanzu haka fasahar AI ba ta da damar yin kutse don lalata sakamakon zaɓe a tsarin INEC. Amma akwai tabbacin cewa za ta iya tasiri kan abin da zai faru kafin ma a shiga zaɓen."
Abin da aka gani a zaɓen 2023
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ba sabon abu ba ne a Najeriya a yi amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba yayin siyasa.
Rahotanni sun nuna cewa a lokacin zaɓen 2023 an yaɗa bayanan ƙarya da kuma wasu abubuwan da aka ƙirƙira ta hanyar AI domin tasiri kan ra'ayin jama'a.
Malam Kiru ya ce wannan na nuna irin barazanar da Najeriya za ta iya fuskanta yayin da fasahar AI ke kara samun saukin amfani.
"Ƙirƙirar bayanan ƙarya na daga cikin abubuwan da wannan fasaha za ta iya samarwa. Kuma yana da matuƙar wahala wani lokaci ka gane gaskiyar abin da aka ƙirƙira da abin da yake na gaske."
A cewarsa, matsalar na iya ƙara muni a lokacin zaɓe saboda saurin yaɗa bayanai a kafafen sada zumunta.
A watan Mayun 2026, wani sautin da ya yi kama da muryar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaɗu a kafafen sada zumunta.
Bincike ya nuna cewa an yi amfani da wani bidiyon shugaban ƙasar da aka samu a baya, sannan aka yi amfani da fasahar AI wajen sauya muryar.
Wannan misali ya nuna yadda za a iya ɗaukar ainihin hoton ɗan siyasa a haɗa shi da muryar bogi, sannan a samar da wani abu da zai yi wa mai kallo ko mai sauraro kama da gaskiya.
Raba kan al'umma
A cewar Malam Kiru, barazanar AI ba ta tsaya ga ƙirƙirar labarin ƙarya kai tsaye ba.
Ana iya amfani da bayanan da aka tattara game da mutane wajen aika musu da saƙonni daban-daban bisa ga abubuwan da suke so, matsalolinsu ko irin abubuwan da suke yawan kallo a kafafen sada zumunta.
Wannan dabara na iya sa ƙungiyoyin siyasa su aika sakonni daban-daban ga kungiyoyin masu kada kuri'a daban-daban.
"Wata dabara ce ta rarraba jama'a ta hanyar amfani da bayanan sirri domin tura musu saƙonni na musamman da suka dace da buƙatunsu da ɗabi'unsu ko ra'ayoyinsu."
A cewarsa, hakan na iya ba ƴansiyasa damar isar da saƙonni daban-daban ga rukunin masu kaɗa ƙuri'a daban-daban.
"Mutum ɗaya zai iya ganin wani saƙo, yayin da wani rukuni na mutane suka ga wani saƙo daban, duk da cewa suna magana ne a kan ɗan takara ɗaya."
Haɗarin bidiyon bogi
Babban abin da ya bambanta AI da wasu hanyoyin yaɗa labaran ƙarya shi ne sauƙin samar da abubuwan da suke kama da gaskiya.
Ana iya samar da muryar bogi da ta yi kama da ta ɗan siyasa, bidiyon bogi da ke nuna mutum yana faɗin abin da bai faɗa ba, ko hoton da aka ƙirƙira wanda bai taɓa faruwa ba.
Malam Kiru ya ce wannan na iya zama matsala musamman idan mutane suka fara yarda da abin da suka gani ko suka ji ba tare da tantance shi ba.
"A yau AI na iya ƙirƙirar bayanai masu kamanceceniya da gaskiya ta yadda ba za ka gane cewa ƙarya ba ce sai an yi maka cikakken bayani ko bincike."
Taimakon AI ga INEC
Sai dai duk da waɗannan barazana, AI ba fasaha ce da za a yi amfani da ita wajen cutar da tsarin zaɓe kadai ba, domin ana iya amfani da ita wajen taimaka wa masu kaɗa ƙuri'a samun sahihan bayanai cikin sauki.
Misali, za a iya amfani da AI wajen amsa tambayoyin masu kaɗa ƙuri'a game da yadda ake yin rajistar zaɓe, abubuwan da ake buƙata a ranar zaɓe, yadda ake amfani da BVAS da kuma ƙa'idojin zaɓe.
Malam Kiru ya ce akwai kuma damar amfani da AI wajen taimakawa wajen tantance bayanan da ake zargin karya ne.
"Fasahar AI za ta iya zama abin dogaro ga hukumar zaɓe da al'umma baki ɗaya wajen samar da bayanai da kuma taimakawa wajen tantance bayanan gaskiya."
Sai dai ya ce bai kamata a bar fasahar AI ita kaɗai ta yanke hukunci kan abin da yake gaskiya ko ƙarya ba.
"Har yanzu mutum yana da muhimmiyar rawa, saboda akwai wasu abubuwa da AI ba za ta iya fahimta yadda ɗan Adam yake fahimta ba, musamman mahallin magana da yanayin al'umma."
Me ya kamata a yi kafin 2027?
A cewar Malam Kiru, akwai buƙatar gwamnati, INEC, kamfanonin kafafen sada zumunta, masana fasaha da kafafen yaɗa labarai su fara shiri tun kafin lokacin zaɓe.
Daga cikin abubuwan da ake buƙata akwai wayar da kan jama'a kan yadda ake gane abubuwan da aka ƙirƙira da AI, inganta tsarin tantance bayanai, da kuma samar da hanyoyin da hukumomin zaɓe za su iya fitar da sahihin bayani cikin gaggawa idan bayanan ƙarya suka fara yaduwa.
Haka kuma akwai buƙatar dokoki da ƙa'idoji da za su fayyace yadda ake amfani da AI a harkokin siyasa tare da kare ƴancin faɗin albarkacin baki.
Masanin ya ce fasahar AI ba ita ce matsalar ba, yadda mutane za su yi amfani da ita ne.
A ƙarshe, Malam Kiru ya ce bai kamata a riƙa kallon AI a matsayin wata fasaha da kanta ke da niyyar cutar da al'umma ba.
"Fasahar AI ba ita ce matsalar wannan al'umma ba. Mutane ne matsalar. Fasahar ba ta da ikon cutarwa da kanta sai abin da mutane suka koya mata ko suka umarce ta da ta yi."
A cewarsa, ya zama wajibi gwamnati ta samar da dokoki da ƙa'idojin amfani da fasahar tare da tabbatar da cewa ana ɗaukar matakan da suka dace daga ɓangaren masu ƙirƙira da masu amfani da ita.










