Mece ce makomar Fubara,bayan janyewa daga zaɓen fitar da gwani na gwamnoni?

.

Asalin hoton, Facebook/Fubara

Bayanan hoto, '
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana janyewa daga zaɓen fidda gwani na ƴan takarar gwamna a jam'iyyar APC .

Sanarwar ta sa na zuwa ne yayin da jam'iyyar APC mai mulki ke shirin gudanar zaɓen fidda gwani na yan takarar gwamna a ranar 21 ga watan Mayu.

A cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar da kansa, ya ce zai goyi bayan duk wanda ya zama ɗan takarar jam'iyyar.

''Bayan tunani mai zurfi tare da tattaunawa da ƴan uwa da abokan arziki, na yanke shawarar ficewa daga zaɓen fidda gwani na gwamnonin jam'iyyar APC. Na yi haka ne da zuciya ɗaya tare da goyon bayan duk wanda ya fito a matsayin ɗan takarar babbar jam'iyyarmu," in ji shi.

Gwamnan ya ce jihar Ribas ta fi kowane mutum muhimanci, yana mai jaddada cewa a wannan mawuyacin lokaci, ya zama dole zaman lafiya da kwanciyar hankali da haɗin kan jihar su gabaci buƙatun ƙashin kai.

Ya ce shirun da ya yi a lokacin da ya k fuskantar matsin lamba a ƴan watannin nan bai kamata a ɗauke shi a matsayin tsoro ba.

''A fahimci a fili cewa na janye daga shiga zaɓen gwamnan jihar Ribas mai zuwa ba don rauni ko tsoro ko miƙa wuya ba, sai don yaƙini da sadaukarwa domin jihar Ribas ta samu ci gaba cikin zaman lafiya da haɗin kai." Inji shi.

Sai dai wasu na ganin cewa janyewar Fubara ta na da nasaba da rikicin da suke yi da mutumin da ya gaji mulki daga wurinsa , Nyesome Wike.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ficewar gwamnan na zuwa ne bayan ɗaya daga cikin ƴan takarar gwamnan a jihar Gombe Malam Isa Ali Pantami ya sanar da janyewa daga shiga zaɓen saboda a cewarsa an shirya yin maguɗi.

Malam Bala Ibrahim, wanda shi ne daraktan watsa labarai na jama'iyyar APC, ya shaidawa BBC cewa tun farko jam'iyyarsu ta hango wasu matsaloli kuma tuni ta ɗauki matakin shawo kansu

''Jam'iyya ta yi iya ƙoƙarinta domin ganin cewa an yi zaɓuɓɓukan nan lami lafiya ba tare da yamutsi ko hayaniya ba, akwai ƴan matsaloli waɗanda aka hanga, akwai ƙoƙarin da jam'iyya ta yi na ganin cewa an yi maganinsu''

''Abinda ake son a gani shi ne a yi wa jama'a adalci ta yadda ba za'a samu rarrabuwar kawuna ba tun da yake ana bai wa maslaha fifiko''

''Dama inda ba a samu maslaha ba ne shi ne ake maganar ayi ƙato bayan ƙato amma muna fata kowane idan aka yi da ƙarshe dai za a yi ƙoƙari a ga an ƙarfafa ƙarfin wannan tsintsiya ta yadda za ta yi sharar da ake buƙata'' in ji shi