Yadda zaɓen fitar da gwani na kujerar sanatoci na APC ya bar baya da ƙura

Asalin hoton, APC/X
A Najeriya, ana ci gaba da jayayya tare da nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaɓukan fidda gwani na jam'iyyar APC mai mulki a kasar da aka gudanar a ranar Litinin.
An gudanar da zaɓen fidda gwani na sanatoci ne a jihohi daban-daban, inda wasu wuraren aka tabbatar da su kasancewar an cimma maslaha, to sai dai wannan tsari da APCin ta yi ga alama ya bar baya da ƙura.
Sanatoci da dama ne wadanda ke kan kujerunsu suka rasa tikitin takarar neman koma a jihohi daban-daban na Najeriya, a zaben fidda gwani na jam'iyyar APCin da aka kammala a ranar Litinin.
Cikinsu akwai Sanata Ned Nwoko wanda Ifeanyi Okowa ya kayar da shi a jihar Delta.
Sai kuma Sanata Danjuma Goje da ya rasa tikitin inda aka ayyana DCP Muhammad Ahmed mai ritaya a matsayin wanda zai yi wa APC takarar a Gombe ta tsakiya.
Jihohi da dama dai, tsarin maslaha suka ɗauka, inda kuma tuni suka tabbatar da ƴan takarar, ciki har da jihar Kano da Jigawa da Yobe sai kuma Katsina kodayake an yi zaɓen a mazaɓa daya, abin da ya sa da dama ke korafin cewa ɗauki ɗora kawai aka yi ba maslaha ba.
Yusuf Bala Ikara ɗan takarar majalisar dattawa ne a jihar Kaduna, wanda ke cikin wa ɗanda ba su gamsu da yadda aka yi zaɓen ba:
''A guna dantakara ba a yi zabe ba. An rubuta wanda ake so a rubuta a wasu gurare da suka je suka boye kansu, suka yi abin da suka yi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
''Amma zabe bai gudana ba. Ka'idar zabe ita ce za a zo a tara mutane, malaman zabe su fito da kayan zabe, a kirga wane ya samu kaza wane ya samu kaza amma wannan ba haka aka yi ba.
''Ni da nake takara ma ban yi zabe ba, ban ga kayan zabe ba, ban ga malaman zabe ba. Haka ma jama'a kashi casa'in ko casa'in da takwas bisa dari ba su ga masu zabe ba. Za mu duba abin da ya dace na doka mu dauka.''
A jihar Zamfara kuwa a ranar Talatar nan ne ake sa-ran za a gudanar da zaɓen fitar da gwanin na sanatoci, to sai dai tuni wasu suka yi fatali da tsarin da za a fitar da 'yan takarar.
To amma Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya ce sun yi amfani da tsarin da APC ta bayar ne na yin maslaha amma ba kakaba 'yan takara suka yi ba.
Rahotanni na cewa tsarin maslaha da jam'iyyar APC ta ɗauka wajen fitar da ƴan takarar sanatan zai iya yi mata lahani saboda yadda ake ci gaba da samun korafi a wurare da dama, to sai dai bayanai na cewa jam'iyyar na cewa wannan tsari shi ne take ganin hanyar da zai rage mata ruɗani da rigingimu.









