'Maganar Trump cewa mashigar Hormuz ta Amurka ce shaci-faɗi ce'

Asalin hoton, Getty Images
Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa wani jami'in Fadar White House ya ce kalaman Donald Trump na cewa mashigar Hormuz ta Amurka ce shaci-faɗi ce, ba wata manufa ta hukuma ba.
Trump ya bayyana a ranar Juma'a cewa mashigar Hormuz mallakin Amurka ce.
Sai dai kalaman nasa sun jawo martani daga Iran, inda mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar, Kazem Gharibabadi, ya ce mashigar Hormuz "ta Iran ce, kuma zai ci gaba da kasancewa hakan.


















