Ƙalubale 7 da INEC za ta iya fuskanta a zaɓen Najeriya na 2027

Ana tantance wata mata

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da ya rage saura ƙasa da wata takwas a gudanar babban zaɓen Najeriya na 2027, hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta duƙufa don ganin ta shirya babban aikin a ƙasar da ta fi kowace yawan jama'a a Afirka.

Tuni dai jam'iyyun siyasar ƙasar suka fara gudanar da zaɓukan fitar da gwani a shirye-shiryensu tunkarar zaɓen na 2027.

A duk lokacin da aka gudanar da zaɓuka a Najeriya, akan fsukanci ƙalubale nan da can a harkar gudanar da zaɓukan.

Ƙungiyoyin da ke sanya idanu kan zaɓukan na cikin gida da na waje kan fitar da rahotonnin matsaloli da nasarorin da aka samu a lokacin zaɓukan.

Awwal Musa Rafsanjani, shugaban gamayyar ƙungiyoyin da ke sanya idanu a zaɓukan Najeriya, Transition Mornitoring Groups (TMG), ya bayyana wa BBC wasu daga cikin ƙalubalen da hukumar INEC ɗin za ta fukanta a zaɓen na 2027.

Matsalar Tsaro

matsalar tsaro

Asalin hoton, @HQNigerianArmy

Matsalar tsaro na ɗaya daga cikin matsalolin da aka saba fuskanta a zaɓukan Najeriya na baya-bayan nan.

Wasu yankuna da dama na arewacin ƙasar da kudanci kan fuskanci matsalolin tsaro ta yadda a wasu lokutan ma ba a iya gudanar da zaɓukan a yankunan.

Awwal Musa Rafsajani ya ce matsalar za ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da zaɓen 2027 zai fuskanta.

''Wannan matsalar yanzu tana nan a Najeriya, kuma ba ta yadda za a yi zaɓe cikin tsoro, fargaba da rashin kwanciyar hankali, dole ne jami'an tsaro da hukumar INEC da mutanen gari su haɗa kai don ganin an samu sauƙin matsalar'', in ji shi shugaban na TMG.

Rashin ƙwarin gwiwa da INEC

Shugaban INEC

Asalin hoton, INEC/X

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rafsanjani ya ce wani babban abu da zai zama ƙalubale ga zaɓen na 2027 shi ne raunin da imani da hukumar zaɓen a zukatan wasu ƴanƙasar.

Tun bayan naɗin shugaban hukumar zaɓen a 2025, wasu ƴan ƙasar da dama da suka haɗa da ɓangarorin addini da na siyasa sun riƙa ƙorafi da suka sabon shugaban.

Wasu ma sun riƙa kiraye-kirayen tsige shi saboda a cewarsu sun yanke ƙauna daga gare shi.

Majalisar ƙoli kan harkokin Shari'ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta bayyana shi a matsayin barazana ga amincin tsarin dimokraɗiyyar Najeriya. saboda zargin da take yi masa game da fifita wani addini.

Ita ma jam'iyyar adawa ta ADC a nata ɓangare ta yi kira ga shugaban na INEC ya yi gaggawar sauka daga muƙaminsa ko kuma gwamnati ta cire shi, saboda zargin da take yi cewa ba zai yi mata adalci ba.

Sai dai a lokuta da dama hukumar ta INEC ta sha musanta zarge-zargen.

Rafsanjani ya ce wannan babbar matsalar ce ga zaɓn na 2027.

''Wasu ƴan ƙasar da dama ba su yi imani ko amincewa da shugaban INEC ɗin ba, suna ganin ba zai yi musu adalci a zaɓen ba, wannan kaɗai ƙalubale ga hukumar'', in ji shi.

Ƙarancin kayan aikin zaɓe

Na'urorin zaɓe

Asalin hoton, INEC

A duk lokacin da aka yi zaɓe a Najeriya, ɗaya daga cikin matsalolin da masu sanya idanu kan zaɓen ke bayyanawa cikin ƙalubalen da aka samu shi ne rashin wadatattun kayan aikin zaɓe, da rashin isar su cibiyoyin zaɓe a kan lokaci.

Ko a zaɓen an 2027 ma akwai yiwuwar a fuskanci wannan matsala kamar yadda shugaban gamayyar ƙungiyoyin sanya idanu kan zaɓen ya bayyana.

''Wannan zai shafi babbar na'urar da ake son yin amfani da ita a babban zaɓen mai zuwa'', in ji shugaban na TMG.

A zaɓen 2023 da ya gabata an riƙa samun matsalolin amfani da na'urorin Card Readers wajen tattance masu kaɗa ƙuri'a.

Ƙaruwar labaran ƙarya

Rafsanjani ya ce yaɗuwar labaran ƙarya tsakanin ƴan Najeriya na daga cikin abubuwan da za su iya zama ƙalubale ga sahihancin zaɓen na 2027.

''Akwai masu yaɗa labaran ƙarya da dama a shafukan sada zuunta da ke haifar da kokwanto game da yadda za a tafiyar da zaɓen ƙasar mai zuwa'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa ɗaya daga irin labaran ƙaryar da ake yaɗawa game da zaɓen shi ne masu cewa ''APC ce ta naɗa shugaban INEC domin ya yi mata aiki''.

Sayen ƙuri'a

Wata na ƙirga katunan zaɓe

Asalin hoton, Getty Images

Sayen ƙuri'a na ɗaya daga cikin matsalolin da ke janyo wa dimokraɗiyya koma-baya.

Matsala ce da ta jima a tsarin zaɓukan Najeriya, inda ƴansiyasa ke amfani da dabaru daban-daban wajen yaudarar masu kaɗa zaɓe domin su kaɗa musu ƙuri'a.

Rafsanjani ya ce bisa dukkan alamu matsalar za ta faru a zaɓen na 2027, saboda an fara ganin hakan a zaɓukan fitar da gwani.

''Idan ka duba ɗaya daga cikin zaɓukan fitar da gwanin da aka gudanar a baya-bayan nan, an ga bidiyoyin wasu mata daga wata jiha a arewa da suke bayyanawa da bakinsu cewa an ba su kuɗi sun zaɓi wani ɗan siyasa'', in ji shi.

Akan yi amfani da kuɗi ko abinci ko tufafi wajen yaudarar masu kaɗa ƙuri'a domin a sayi ƙuri'unsu.

Amfani da ƴandaba

wasu ƴandaba

Asalin hoton, Getty Images

Matsalar ƴandaba ko ƴanbangar siyasa ta kasance ɗaya daga cikin manyan matsalolin da zaɓukan Najeriya na baya suka fuskanta.

Haka kuma Shugaban ƙungiyar TMG ya ce matsalar tana nan kuma bisa ga dukkan alamu za ta yi ƙamari a 2027.

''Ai yanzu babbar matsalar da yankin arewacin Najeriya ke fuskanta baya ga ƴanbindiga, ita ce matsalar daba'', in ji shi.

Rafsanjani ya ce akwai jihohin da ke zargin ƴansiyasa na goyon bayan ƴandaba suna ta kashe-kashe.

''Akwai wasu jihohin arewa biyu da a baya-bayan nan aka samu ƙaruwar daba, har ma suka kashe mutane, amma babu wani ɗansiyasa ko jami'in gwamnatin jihohin da ya fito fili ya soki batun'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya yi zargin cewa matasa ne ƙananan da ƴansiyasa ke amfani da su, suna ba su ƙwayoyi domin cimma burinsu na siyasa.

Sabuwar dokar zaɓe

Awwal Musa Rafsanjani ya ce sabuwar dokar zaɓen ƙasar da aka yi wa gyara a 2026 na da nata matsalolin da za su iya zama ƙalubale ga zaɓen na 2027.

''Dokar kanta tana ɗauke da ruɗani, saboda har yanzu wasu ƴan ƙasar ba su fahimceta ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ci gaba da cewa rashin fahimtar sabuwar dokar ya sa wasu na ta kwakwanto game da iri abubuwan da ta ƙunsa.