Barcelona ta lashe La Liga bayan casa Madrid a El Clasico

,

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Barcelona ta lashe gasar La Liga ta 2025/26 bayan doke babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid da ta yi a wasan El Clasico.

Barcelona ta samu nasara ne a wasan da ci biyu babu ko ɗaya, abin da ya sa ta haɗa maki 91 kenan.

Real Madrid wadda ta ke matsayi na biyu tana da maki 77 a wasa 35 da aka yi na gasar La Ligar bana.

A mintina na 9 da fara wasan ɗan wasan gaban ƙungiyar Marco Rashford ya sa ƙungiyar a gaba.

Dan ƙasar Ingilar ya ci bugun tazara ne bayan ƙetar da aka yi wa Barcelona a minti na 8 da fara wasan.

Mintina 10 bayan nan ɗan wasan Sifaniya na gaba Ferran Torres ya ƙara ta biyu, wadda kuma har ƙarshen wasan ba ta ƙara ba, ko kuma an samu farke ko ɗaya daga cikin kwallayen nata.

Yanzu dai wasa uku ne ya ragewa Barcelona a gasar inda za ta je gidan Alaves da ke ta ukun ƙarshe a teburi.

,

Asalin hoton, BBC Sport

Sai ta ƙara wasanta na kusa da ƙarshe da Real Betis, sai ta kammala da Valencia.

Ita kuma Real Madrid wadda ke matsayi na biyu za ta fafata wasannin ta uku na ƙarshe ne da Oviedo ta ƙarshen teburi da Sevilla da ke matsayi na 13 sai kuma Bilbao a ranar 24 ga wannan wata.

Ƙungiyar da ke cikin ruɗani saboda rashin jituwar 'yan wasanta za ta ƙare wannan kakar ne ba tare da cin ko kofin shayi ba.

Wannan ita ce shekara ta biyu da Barcelona ta yi tana lashe gasar ta La Liga, kuma shekara ta biyu kenan ga abokiyar hamayyarta da ta yi ba tare da cin La Liga ba.

Yanzu kofi bakwai ne tsakanin Barcelona da Real Madrid a tarihi, wadda ta ci kofi sau biyu a jere.

Wannan ne wasa na 18 da Barcelona ta ci a gida waɗanda suka taimaka mata ta kai ga nasarar lashe gasar a gaban magoya bayanta.

Ƙoƙarin Rashford a Sifaniya, shi ko zai ci gaba da zama a Barcelona?

,

Asalin hoton, Getty Images

Har yanzu akwai shakku kan makomar Rashford a Barcelona wanda a yarjejeniyarsa akwai zaɓin sayansa daga United kan kuɗi fan miliyan 28, ko da yake zaman aron da yake zai ƙare ne a ƙarshen wannan kakar.

Ƙoƙarinsa na wannan wasan wata shaida ce ga ƙungiyar cewa ɗan wasan yana da rawar da zai iya ci gaba da takawa a ƙungiyar.

Bugun tazarar da ya ci abin burgewa ne, kuma ya ci kwallo 14 ya ba da 14 an ci, a wasan 47 da ya bugawa ƙungiyar.

Amma ganin cewa wasa 24 kacal aka fara da shi cikin duka wasannin da ya buga wata shaida ce da ke nuna cewa babu tabbas ko za a saye shi.

Barcelona ta ci kwallo a duka wasanni 35 da ta buga na wannan kakar kuma Rashford ya taka muhimmiyar rawa a wannan tafiya.

Yanzu ya samu sarƙar La Liga da ya lashe, babbar gasa da ya ci kenan a matsayinsa na ɗan wasa.