Carrick ya ci gaba da aiki, yayin da Man Utd ke duba yiwuwar maye gurbinsa

Manchester United head coach Michael Carrick
Bayanan hoto, Michael Carrick ya nemi afuwar magoya bayan Manchester United 700 da suka je Italy domin mara mata baya a wasan Champions League da Como ta ci 4-1
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da ake sa ran Michael Carrick zai jagoranci kungiyar a wasan Premier League ranar Lahadi da Bournemouth, Manchester United ta riga ta fara aikin nemo wanda zai iya maye gurbinsa.

An fahimci cewa Eddie Howe da Antonio Conte da Julian Naglesmann suna da sha'awar karbar aikin a Old Trafford.

Majiyoyi sun ce Carrick na ci gaba da aikinsa kamar yadda aka saba kuma ba a sanar da shi wani canji da ake son yi ba a kungiyar, kayan shan kashi a Como da ci 4-1 a Italiya ranar Laraba a Champions League.

Wannan shan kaye ya biyo bayan da kyaftin, Bruno Fernandes ya yi tambaya kan dabarun Carrick a wasan da suka yi rashin nasara a Gasar ta Zakarun Turai.

An bai wa 'yan wasan United hutu a ranar Alhamis, yayin da har yanzu United ba ta tabbatar da shirye-shiryen taron manema labarai na ranar Juma'a ba, domin shirye-shiryen fafatawa da Bournemouth.

Wasu manyan jami'ai a United na da ra'ayin cewa yawan sauya masu horarwa da aka yi a shekarun baya-bayan nan bai shawo durkushewar kungiyar ba, kuma ana cewa Carrick ya yi rashin nasara ne saboda 'yan wasansa da dama basu samu buga karawar ba, balle su yi abin kirki.

Sai dai hakan ba yana nufin Carrick ya bayar da wannan uzurin kan dalilin da United ta yi rashin nasara ba.

Har yanzu akwai babban rashin tabbas game da makomarsa. Amma kuma wasu na kwatanta kokarin da ya yi a bara a lokacin da kungiyar ke fuskantar mawuya cin hali da ta kai ya yi bajinta, saboda haka suna cewa a kara masa lokaci, domin ya gyara al'amura.

Tun a makonnin baya masu horarwa ko dai wadanda suke da kungiya ko kuma wadanda ke zaune, suka fara ganin alamun za a iya samun aikin horar da Manchester United.

Misali, United za ta iya samun Howe, wanda bai da kungiyar da yake aiki a yanzu haka, Majiyoyi sun nuna cewa tsohon kocin na Newcastle a shirye yake ya koma aikin horaswa tare da Manchester United, bayan barin St James' Park a karshen kakar wasan da ta gabata.

Tsohon kocin Chelsea, Conte da tsohon kocin Jamus Naglesmann, wadanda suma ba su da aiki a halin yanzu, suna sha'awar karbar aikin United.

Kocin Aston Villa Unai Emery da na Brighton Fabian Hurzeler suna da kima sosai a wajen mahukuntan United kan rawar da suke takawa, amma yanzu haka dauko su daga kungiyoyinsu abu ne me dan karen wahala.

Makomar Carrick na iya zama tamkar ta waɗanda suka gabace shi.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A karo na uku a jere, United ta nuna goyon baya ga koci a bainar jama'a, haka kuma ta fitar da kudi masu yawa a lokacin bazara ta dauko yan wasa, amma har yanzu ba ta samun sakamakon da ake bukata a wasanninta.

A lokacin da Ruben Amorin yake kocin United ya fuskanci irin wannan matsalar, kuma an barshi har zuwa watan Jaiaru, amma rashin nasara ta ban mamaki da yi yi a Gasar League Cup a hannun Grimsby, kungiyar da ke League Two a watan Agustan bara.

Haka kuma mummunan wasan da suka yi da Brentford kasa da wata guda sun kawar da kariyar da mahukuntan kungiyar da suke yi wa Amorin, wadanda suka yanke korar dan kasar Portugal.

Daga nan United ta yi nazari sosai kan wasu 'yan takara masu son karbar aikin horar da kungiyar ciki har da Thomas Tuchel da Roberto de Zerbi a lokacin bazarar shekarar 2024 kafin ta yanke shawarar ci gaba da zama tare da Erik ten Hag. Daga baya ta sallami dan kasar Holland a watan Oktoba.

Yanzu kuma ga halin da Carrick yake ciki na fuskantar dan karen kalubale.

Akwai masu adawa da nada shi kociyan kungiyar Old Tarfford a lokacin da aka ba shi aikin a watan Mayu, sai dai kuma ya cancanci ya jagoranci United bayan nasara 12 daga wasa 17 da ya yi a matsayin kocin rikon kwarya da kuma kai kungiyar Gasar Zakarun Turai bayan shekara biyu rabonta da buga wasannin.

Amma kamar yadda aka saba, samun sakamako mai kyau ne ke tsara komai.

Akwai dalilai masu yawa da suka haddasa rashin kokarin kungiyar a wannan kakar wasa, kuma za a iya raba laifi tsakanin sassa daban-daban da kuma har zuwa saman shugabancin kungiyar.

Sai dai gaskiya mai daci ita ce nasara biyu kacal cikin wasanni 11, kuma bata ci wasa ko daya ba daga bakwai a jere ba, wanda shi ne mafi muni tun kakar 2015-16 lokacin da yi karawa takwas ba tare da nasara ba, hakan ya sa aka kusan korar Louis van Gaal.

Saboda haka rashin nasarar kungiyar ya dogara a kan Carrick kuma idan abubuwa ba su canja da wuri ba, zai iya rasa aikinsa a kowanne lokaci mai zai zuwa, domin shi ne kofi shi ne ake sa ran zai fitar da kungiyar daga halin da take ciki.

Me zai faru yanzu a Manchester United?

Zarge-zargen rashin ƙwazo da ingantantun yan wasa da rashin kokarin kungiyar sun dabaibaye United a duk tsawon kakar wasan bana, inda ta yi nasara sau biyu kacal a dukkanin fafatawar da ta yi daga ciki ta yi nasara daya a Premier League da kuma a Champions League.

Har ila yau, ƙungiyar tana fuskantar matsalolin raunuka da yan wasanta kan yi lokaci-lokaci da kuma wasu 'yan wasa da basa kan ganiya, suna daga cikin abubuwan da suka kara durkusar da United.

United tana fuskantar kasa cin kwallaye a wasannin da take bugawa, haka kuma karawa daya ce kacal ta yi ba tare da an zura mata kwallo ba a raga, sannan kwazon kungiyar gabaki daya ya yi kasa, kuma tsaron bayanta ya yi rauni.

Irin wannan halin da United take ciki ne ya sa mai tsaron bayanta, Lisandro Martinez ya soki tsarin ɗaukar 'yan wasa da aka yi a bazara da rashin sa kwazo daga wasu yan kwallon.

A tsakanin waɗannan abubuwan kuma akwai hirar da Ten Hag ya yi da Athletic inda ya yi magana kan "alkawuran da aka karya" da kuma "al'adar aiki mai mara tsari".

Duk waɗannan abubuwan suna nuna alamar ƙungiyar ba ta kan turba kan yadda ake gudanar da ita, balle a yi tunanin yadda za a ciyar da ita gaba kan tsarin da ya dace.

Hakika akwai ra'ayi a tsakanin wasu manyan jami'ain ƙungiyar da ke cewa duk da ana tambayar ingancin ɗaukar 'yan wasa gaba ɗaya, musamman rashin sayo wanda zai taimaka wa Benjamin Sesko ko wanda zai kalubalanci gurbin Luke Shaw a matsayin mai tsaron baya daga hagu.

Amma dole ne 'yan wasan su ɗauki babban nauyin halin da ake ciki a yanzu haka a kungiyar, domin da suna yin abin da ya kamata da United ba ta fada wannan yanayin ba.

Bayan sallamar Amorim a watan Janairu, tsohon ɗan wasan United, Darren Fletcher ya karɓi ragamar ƙungiyar a matsayin riƙon ƙwarya a wasa biyu.

Daga baya Fletcher ya koma aikinsa na kocin 'yan ƙasa da shekara 18, amma biyu daga cikin masu horarwar da suka taimaka masa Jonny Evans da Travis Binnion, sun ci gaba da zama tare da babbar ƙungiyar a matsayin wani ɓangare a jagorancin Carrick.

A kakar nan ta bana United ta yi ban kwana da EFL Cup a hannun Brighton, kuma ta fara cin kwallo biyu daga baya aka zare su aka kuma doke ta 3-2 kuma a Old Trafford, tun daga lokacin take ta fuskantar koma baya.

United na bukar cin Bournemouth ko matsil lamba zai dan lafa a wasan Premier League da za su kara a karshen mako da kungiyar da take da sabon koci, Marco Rose.

Itama tana fuskantar koma baya, domin wasa daya ta ci daga bakwai a babbar gasar tamaula ta Ingila, sai dai ta tashi 4-4 a Old Trafford a kakar da ta gabata, kafin nan ta kuma doke United har 3-0, amma karkashin Andoni Iraola, wanda yanzu yake horar da Liverpool.

Sai dai halin da ake ciki har yanzu ba tabbas ko Carrick zai kai karshen mako a United - kenan United tana halin rashin tabbas bayan da kakar bana ba ta fara nisa ba.