Yadda aka rataye mutanen da suka aikata assha' a masallaci a Makka

.
Bayanan hoto, A cewar ƴanuwansa, mutumin yana aiki ne a matsayin mai goge goge a Saudiyya, kuma an kama shi kimanin watanni shida bayan isarsa ƙasar. (Hoto daga iyali).
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Dangin wata 'yar ƙasar Bangladesh da aka yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya saboda abin da hukumomi suka bayyana a matsayin "aikata alfasha" sun ce ba su da cikakken bayani ko 'yarsu ta aikata laifin da ya kai ga hukuncin kisa.

Haka kuma, sun ce sun samu labarin aiwatar da hukuncin ne ta hanyar kiran waya daga wata ƙawar 'yarsu da ke zaune a Saudiyya.

A ranar Laraba 14 ga Oktoba, kafafen yaɗa labaran gwamnatin Saudiyya sun ruwaito cewa an aiwatar da hukuncin kisa kan wasu 'yan Bangladesh biyu, mace da namiji.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA), ya ruwaito wata sanarwar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta ƙasar, wadda ta ce ana zargin mutanen biyu da aikata abin da aka bayyana a matsayin "ayyuka na rashin ɗa'a" a cikin wani masallaci da ke birnin Makka mai tsarki.

A cewar mahukuntan Saudiyya, jami'an tsaro sun kama waɗanda ake zargin, sannan kotu ta tabbatar da laifukan da ake tuhumarsu da su.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce an yanke musu hukuncin ne saboda girman laifin da ake zarginsu da aikatawa, da kuma cin mutuncin masallaci.

Mahukuntan ƙasar sun ce an yanke hukuncin ne ƙarƙashin tsarin ta'azir, wanda ke bai wa kotu damar yanke hukunci kan laifukan da ba a fayyace takamaiman hukuncinsu a shari'ar Musulunci ba.

An aiwatar da hukuncin kisan ne a ranar 14 ga watan Oktoban 2026 bayan kotunan ɗaukaka ƙara sun yi watsi da ƙorafinsu.

Duk da dai hukumomin Saudiyya ba su bayyana ranar da aka kama mutanen biyu ba, mataimakiyar ministar harkokin wajen Bangladesh, Shama Obaid, ta ce an kama su ne tun a shekarar 2023.

A yanzu, iyalan mutanen biyu sun tabbatar da rahoton, inda suka ce 'yan uwansu sun shafe kusan shekara uku a tsare a Saudiyya kafin a aiwatar da hukuncin kisan.

Sashen Bangladesh na BBC ya tattauna da dangin 'yan Bangladesh ɗin da aka yanke wa hukuncin. Sun ce ba su samu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin Saudiyya ko jami'an Bangladesh game da aiwatar da hukuncin ba.

"Ta tafi Saudiyya ne da bizar aiki"

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar 'yar uwarta, ''ƙawar ta ce ta kira ni ta tambaye ni ko mun samu wani bayani. Sai na ce mata ba mu da wani bayani. Daga nan sai ta ce mini ai ƙanwata ta rasu. Daga baya kuma ta turo mini da wani bidiyo, wanda daga bisani na gani yana yawo a kafafen sada zumunta."

Sai dai bayan samun rahotannin farko, iyalan sun ce sun yi shakkar gaskiyar labarin, saboda hoton da aka fara tura musu bai yi kama da 'yaruwarsu ba. Haka kuma ba su samu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ko hukumomin da abin ya shafa ba.

Mahaifin matar da aka rataye ya ce ya yi jinkirin gaskata labarin ne saboda matar da ya gani a hoton da abokiyar 'yarsa daga Saudiyya ta turo masa ba ta yi kama da 'yarsa ba.

A cewar iyalan, mamaciyar ita ce auta cikin 'yan mata huɗu a gidan. Ta tafi Saudiyya a shekarar 2023 da bizar yin aiki domin taimakawa wajen inganta rayuwar ƴanuwanta.

Mahaifinta ma'aikacin ƙwadago ne, kuma iyalan sun ce an kama 'yarsu ne kusan watanni shida da isarta Saudiyya.

'Yar uwarta ta kuma ce "Matsalar ta soma ne bayan wata shida da tafiyarta Saudiyya. Ta gaya mana cewa tana gidan yari, amma ba ta bayyana mana dalilin da ya sa aka tsare ta ba. Har ma ta hana mu yi mata tambayoyi, inda ta ce idan ta dawo gida za ta yi mana bayanin komai."

Iyalan sun ce duk tsawon lokacin da take tsare, tana tuntubar su kusan sau ɗaya a kowane wata. Sun ce karo na ƙarshe da suka yi magana da ita shi ne a ranar Talata, kwana ɗaya kafin hukumomin Saudiyya su sanar da aiwatar da hukuncin kisa kanta a ranar Laraba.

'Yar uwar ta ƙara da cewa "Mun yi magana da ita a ranar Talata. Ta sake kiranmu a ranar Laraba, amma ba mu samu damar ɗaga kiran nata ba."

"Ban san cewa za a rataye ɗana ba"

.
Bayanan hoto, A cewar kafafen yaɗa labaran gwamnatin Saudiyya, an aiwatar da hukuncin kisa da aka yanke wa wani namiji da wata mace 'yan ƙasar Bangladesh a ranar 14 ga Oktoban 2026.

Mahaifiyar ɗan Bangladesh ɗin da aka yanke wa hukuncin kisa ta shaida wa sashen Bangladesh na BBC cewa iyalan sun yi magana da shi daga gidan yari a Saudiyya a ranar Lahadin da ta gabata.

Tana magana cikin kuka, ta ce: "Mun san yana gidan yari, amma ba mu taɓa tunanin cewa hakan zai faru ba. Ko shi kansa ɗana bai gaya mana cewa za a yanke masa hukuncin kisa ba."

Mahaifinsa ma ya ce ya samu labarin aiwatar da hukuncin ne a ranar Larabar da ta gabata.

"Na yi magana da ɗana a ranar Lahadi. Ya tambaye ni lafiyata. Sai kuma ranar Laraba na samu labarin cewa an aiwatar da hukuncin kisa a kansa."

Mahaifin ya ce ɗansa ya yi kusan shekara uku a gidan yari a Saudiyya, amma a duk wannan lokaci bai samu wata sanarwa daga gwamnati dangane da halin da ɗansa ke ciki ba.

"A duk shekarun nan ina ta tambaya ko ofishin jakadancin Bangladesh ya bi diddigin lamarin, amma babu wanda ya ba ni wani bayani. Babu wani jami'in Bangladesh da ya taɓa ziyartarsa a gidan yari ko ya binciki halin da yake ciki."

Ya kuma buƙaci a dawo masa da gawar ɗansa Bangladesh cikin gaggawa tare da gudanar da bincike domin a tabbatar an yi adalci a lamarin.

"Shekara uku da wata uku kenan ban ga fuskar ɗana ba. Ina fatan in gan shi a karo na ƙarshe."

A cewar mahaifiyarsa, matashin ya kammala makarantar Islamiyya kafin ya tafi Saudiyya ta hannun wani jam'in kamfanin zarga zirga a ranar 10 ga Nuwamban 2022.

Shi ne babban ɗa a cikin yara huɗu, maza biyu da mata biyu. Ya yi aiki a matsayin mai tsaftace muhalli a Riyadh, kuma an ce yana aikin tsaftace wani masallaci lokacin da aka zarge shi da aikata abin da hukumomi suka kira "ayyuka na rashin ɗa'a".

Mahaifiyarsa ta ce: "An tsare shi ne bayan 'yan watanni kaɗan da isarsa Saudiyya. Bayan wata guda da aka tsare shi sai ya kira ni ya ce, 'Mama, wataƙila za su tsare ni na ɗan lokaci sannan su sake ni.'"

Da aka tambaye ta ko ɗanta ya taɓa bayyana dalilin kama shi, ta ce:

"A'a, bai taɓa gaya mana cikakken dalilin ba."

Sai dai wani ɗan uwansa ya ce daga baya matashin ya sanar da iyalan cewa yana da alaƙar soyayya da wata mata.

A cewar mahaifiyarsa, ɗanta ya gaya musu cewa wata rana yana wurin aiki ne sai jami'an 'yan sanda suka zo suka kama shi.

Iyalan sun ce bayan an tsare shi, yana tuntubar su ta hanyar kiran waya na gajeren lokaci kusan kowane mako, kuma a ɗaya daga cikin tattaunawar ya ambaci dangantakarsa da matar.

Karo na ƙarshe da suka yi magana da shi shi ne a ranar Lahadi, kwanaki uku kafin aiwatar da hukuncin kisa.

Mahaifiyarsa ta ƙara da cewa: "Da farko ɗana ya kasa kare kansa yadda ya kamata saboda matsalar saɓanin harshe. Lokacin da muka tuntuɓi wakilin da ya kai shi Saudiyya, sai ya gaya mana cewa bayan ya kai shi can ba shi da wani ƙarin alhaki a kansa."

Mazauna yankinsu sun shaida wa BBC cewa matashin yana da kusan shekara 22. Mahaifinsa ya kasance yana aikin noma a gonakin wasu mutane, amma saboda tsufansa yanzu ba ya iya yin irin wannan aiki.

Saboda mawuyacin halin da iyalin ke ciki ne aka tura matashin aiki ƙasashen waje ta hannun wani jami'i.

Sai dai an kama shi a shekarar 2023, kimanin wata shida bayan zuwansa Saudiyya.

Me hukumomin Bangladesh suka ce?

Dhaka pia ilimwita balozi wa Saudi Arabia kutokana na suala hilo.
Bayanan hoto, Dhaka ta gayyaci jakadan Saudiyya kan lamarin

A gefe guda kuma, Karamar Ministar Harkokin Wajen Bangladesh, Shamma Obaid Islam, ta ce bayan samun labarin aiwatar da hukuncin kisa kan 'yan ƙasar biyu, gwamnatin Bangladesh ta aika wa gwamnatin Saudiyya wasiƙa a hukumance kwanaki biyu da suka gabata, tana neman cikakken bayani kan lamarin da kuma shari'ar da ta shafi 'yan ƙasar Bangladesh ɗin da aka yanke wa hukuncin kisa.

Da take zantawa da manema labarai, ta ce gwamnati na jiran samun kwafin takardar hukuncin kotun da kuma bayanan yadda shari'ar ta gudana.

Bugu da ƙari, Ma'aikatar Harkokin Wajen Bangladesh da ke Dhaka ta gayyaci jakadan Saudiyya a Bangladesh, Abdullah Zafer bin Abiyah, domin ya yi ƙarin bayani kan lamarin da kuma yadda aka aiwatar da hukuncin.

A cewar Shamma Obaid Islam, Saudiyya na daga cikin muhimman ƙasashen da 'yan Bangladesh ke zuwa domin neman aiki, kuma kuɗaɗen da suke aikowa gida daga can na daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na ƙasashen waje ga Bangladesh.

Ta ce: "Akwai sama da 'yan Bangladesh 400,000 da ke zaune tare da aiki a Saudiyya, kuma haƙƙinmu ne mu tabbatar da tsaron lafiyarsu."

Ta kuma ƙara da cewa akwai 'yan Bangladesh da dama da ke zaman hukunci a gidajen yari daban-daban na Saudiyya, kuma hukumomin Saudiyya na aika wa gwamnatin Bangladesh jerin sunayen waɗanda aka kama, da lokacin da aka kama su, da kuma dalilan kamasu.

"Muna binciken ko sunayen mutanen nan biyu na cikin waɗannan jerin sunaye ko a'a. Haka kuma, ba mu samu wani bayani daga ƴanuwansu ba. Abin da muka sani shi ne lamarin ya faru ne a shekarar 2023, kuma an kama su a wannan shekarar."