Shawarwari uku ga masu tafiya a jirgi don kauce wa ɗaukar kayan laifi

Wasu mata matafiya
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Har yanzu mutane na ci gaba da muhawara bayan da jami'an NDLEA mai yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya suka kama wata mata a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano da birnin Kano da tabar wiwi a cikin jarkar manja a kan hanyarta ta zuwa Saudiyya.

Bayanan farko da hukumar ta fitar, ta ce wani ɗan'uwan matar ne ake zargi da sanya mata tabar cikin jarkar manja da nufin fataucinsa zuwa saudiyya ba tare da ta sani ba.

A lokuta da dama dai aka samu matsalar saka wa matafiya kayan laifi cikin jakankunansu ba tare da saninsa.

Ko a shekarun baya ma hukumomin saudiyya sun kama wata matashiya yar asalin jihar Kano, bayan da aka samu miyagun ƙwayoyi a cikin jakar da ke ɗauke da lambar takardun tafiyarta.

Lamarin da ya sa har sai da hukumomin Saudiyya suka yanke mata hukuncin kisa, kafin daga bisani aka gano gaskiya har aka sallameta.

'Hanyoyin da ke sa a saka wa mutum kayan laifi a jakarsa'

Masu tafiya

BBC ta zanta da wani babban jami'in da ke aikin kula da jakankunan matafiya a daya daga cikin filayen jiragen saman Najeriya, wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce akwai dalilai da dama da ke sa matafiya su tafi da kayan laifi ba tare da saninsu ba.

  • Karɓar Saƙo

Wannan ita ce hanya ta farko da mutum zai iya tafiya da kayan laifi ba tare da saninsa ba, a cewar ma'aikacin filin jirgin.

''A wasu lokuta masu aikata laifi, kan yi amfani da matafiya wajen aika kayan laifinsu ta hanyar ba su saƙo domin kai wa wasu a ƙasar da za su je'', in ji shi.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Ya ce za a ba ka saƙo a ƙulle cikin leda ko cikin jarka ba tare da ka san mene ne ba, shikenan daga nan ka ɗauki kayamn laifi ba ka sani ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

  • Sayar da kilon da aka wa matafiyi

Wani karin dalilin da kan sa mutum ya faɗa tarkon tafiya da kayan laifi shi ne sayar da kilon da aka ware masa domin ɗaukar kaya.

A cewar jami'in filin jirgin duk matafiyi a jirgi akan ware masa kilo 46 na babbar jaka, sannan yana da kilo 8.

''To wasu idan ba su da kayan da ya kai wannan nauyin, sai wasu su tambaye su ko za su sayar musu da nasu kilon, ta yadda za su saka nasu, kayan amma za a yi amfani da takardun bayanan asalin mai wurin wajen tantance kayan'', in ji shi.

  • Masu taimaka wa fasinjoji tantance kaya

Wata hanyar ita ce masu taimaka wa fasinjoji tantance sukan yi amfani da wannan damar wajen shigar da kayan laifi a jakar matafiyi.

''Irin waɗannan mutane, idan ba ka lura ba za su iya saka maka kayan laifi, su ɗauki lambar kayan naka, ta yadda za su tura wa masu tantance jakankuna na ƙasar da za su je domin su cire kayan'', in ji shi.

Me ya kamata matafiyi ya yi?

wata mai tafiya

Ma'aikacin filin jirgin ya lissafa wasu hanyoyi huɗu da ya ce mutum ya lura da su idan ya zo filin jirgi domin kauce wa faɗa wa tarkon tafiya da kayan laifi.

Tantance jakarku da kanku

Ma'aikacin filin jirgin ya ce abu na farko da mutum zai yi shi ne ya je ya tantance jakarsa da kansa a filin jirgin.

''Kada ka yarda wani ya ce zai taimaka maka wajen ɗaukar maka jaka a wurin tantance kaya, komai yawan kayanka kuwa. in ba haka ba za ka iya samun matsala'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa mutum ya kula sosai da kayansa, akwai mutane da ke cewa za su taimaka maka tantance kayan naka, domin ka ba su wani abu.

Kauce wa sayar da kilon kaya

Ma'aikacin na filin jirgi ya kuma shawarci matafiya kada su yarda su riƙa sayar da kilon da aka ware musu a jirgi.

''Idan ka zo ba ka da kaya, wani ya ce ka sayar masa da wurin saka kayanka, ka ce masa a'a ba za ka sayar ba, kuma ka tabbatar ka faɗa wa jami'an da ke bayar da tikitin shiga jirgi cewa ba ka da kaya, su tabbatar da haka'', in ji shi.

Kauce wa karɓar saƙo

Jami'in filin jirgin ya kuma shawarci matafiya su kauce wa karɓa saƙo daga wurin kowa idan za su yi tafiya.

''A duk lokacin da za ka yi tafiya ka kauce wa karɓar saƙo daga wurin mutane, koda yaya kuke da mutum kada ka yarda ka karɓi saƙonsa'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa in ma ta kama mutum zai karɓi saƙo to kada ya karɓi saƙon abin da bai sani ba, ya tabbatar an buɗe masa komai ya ganshi ido-da-ido.