Yadda bidiyon IS ya nuna mayaƙan ƙasar waje a Najeriya

Asalin hoton, AMAQ
Wani bidiyo da ƙungiyar Islamic State (IS) ta fitar baya-bayan nan kan harin da ƙungiyar ta kai kan dakarun Najeriya a jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya ya ƙara haske kan bayanin da ke nuna cewa akwai mayaƙa Larabawa cikin masu kai hare-hare a ƙasar.
Wasu daga cikin masu goyon bayan ƙungiyar wadanda suka yi tsokaci sun yi hasashen cewa mayaƙan sun fito ne daga ƙasashen arewacin Afirka, musamman Moroko da Algeria.
A watan Yuli, rundunar sojin Najeriya ta ce ta daƙile wani hari da ƙungiyar ISWAP ta yi yunƙurin kaiwa a jihar Borno wanda wasu mayaƙa Larabawa suka "jagoranta".
Bidiyon da ƙungiyar ta fitar ranar 15 ga watan Agusta na zuwa ne bayan wani gagarumin hari da dakarun Najeriya da hadin gwiwar na Amurka suka kai a manyan sansanonin ISWAP a jihar Borno, wanda rahotanni suka ce ya dagula wa ƙungiyar lissafi kuma ya yi ajalin ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Abu Musab am-Mki.
Ayyukan ƙungiyar ta ISWAP sun yi ƙasa tun bayan harin, sai dai ta riƙa farfaɗowa a hankali.
Wanda aka nuna a bidiyon yana magana cikin harshen Larabci ya ce mayaƙa na shiga ƙungiyar IS "daga ko ina", sannan ya riƙa tutiya da ci "ɓarnar" da ƙungiyar ke yi kan manyan sansanonin soji a Najeriya da kuma yankin Tafkin Chadi.
Bidiyo
An saki bidiyon ne mai tsawon minti 3:20 ranar 15 ga watan Agusta a shafin ƙungiyar IS na manhajar Telegram.
Kafar yaɗa labarai ta ƙungiyar Amaq ce ta haɗa bidiyon, wadda akai-akai take sakin bidiyoyin hare-haren da IS ke iƙirarin kaiwa, inda a wasu lokutan bidiyoyin kan nuna mayaƙa na jawabi na nuna turjiya.
Kafar yaɗa labaran ta IS ta ce bidiyon ya tattara bayani ne kan harin da ISWAP ta kai ranar 9 ga watan Agusta a kan wani "sansanin soji" a garin Gajiram na jihar Borno.
A iƙirarin da ta yi tun farko a ranar 12 ga watan Agusta, IS ta ce harin da ta kai ya "tursasa wa dakarun Najeriya tserewa", lamarin da ya bai wa mayaƙanta damar ƙwace sansanin na wani ɗan lokaci.
Haka nan ƙungiyar ta yi iƙirarin ƙwace makamai da kuma cinna wa wasu wuta.
A lokacin da bidiyon ya kai minti 2:31 sai aka sako wani mayaƙi wanda aka dusashe fuskarsa, duk da ana iya ganin cewa yana da hasken fata.
Mutumin ya yi magana cikin harshen Larabci na asali wanda hakan ya nuna cewa zai iya yiwuwa asalin balarabe ne.

Asalin hoton, AMAQ
Ya bayyana cewa "mayaƙan ƙungiyar sun fito daga ko ina domin yin faɗa har sai an tabbatar da dokar Allah", wanda hakan ke ƙara nuna cewa shi da wasu mutanen daban sun je Najeriya domin shiga ƙungiyar a ƙasar.
Ya kuma yi tutiya da harin ISWAP wanda ya yi iƙirarin cewa ya lalata sansanin sojojin na Najeriya, inda ya ce "jiragen Amurka ba za su taimaka muku ba", wanda hakan ke nuni da taimakon da Amurka ta bai wa Najeriya wajen yaƙi da ƙungiyar IS, musamman a samamen da suka kai kan mayaƙan ƙungiyar a ranar 6 ga watan Mayu.
A ƙarshen bidiyo an nuna wasu makamai da ƙungiyar ta yi zargin ƙwacewa a harin.
Yadda ISWAP ke amfani da mayaƙa daga waje

Asalin hoton, ISWAP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ƙarshen shekarar 2024 da kuma 2025, IS ta fito tana tutiya kan amfani da mayaƙan ƙasashen waje a ressanta na ISWAP da kuma a ƙasar Somalia, haka nan ta kuma yi iƙirarin kai hari da mayaƙan ƙasar waje a Jamhuriyar Nijar cikin watan Janairun 2026 ba tare da bayar da cikakken bayani ba.
A wani bidiyon farfaganda na ISWAP da aka saki a watan Disamban 2024, ya nuna wasu masu bayar da horo daga yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.
Duk da cewa an yi dushi-dushi da fuskarsu amma sunayensu na inkiya da aka bayyana su ne Abu Ishaq al-Maqdisi, Abu Juwayriya al-Maghribi da kuma Abu al-Yaman al-Maghribi- wani abu da ke nuna cewa akwai yiwuwar biyu daga cikinsu sun fito ne daga yankin Falasɗinawa da kuma Moroko.
A ranar 12 ga watan Yulin 2026 rundunar sojin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa ta daƙile wani yunƙuri na kai hari kan sansanin soji a jihar Borno.
Rundunar ta kafa hujja da wani faifan bidiyo da ta samu daga maharan, inda ta ce wasu ƴan ƙasar waje ne suka "jagoranci" harin.
Rundunar sojin bayyana su a matsayin "wani balarabe ɗan asalin yankin Falasɗinawa Abu Ishaq, wanda aka bayyana a matsayin babban mai bayar da horo na ISWAP, sai wani balarabe ɗan Moroko mai suna Abu Thaiba, wanda likita ne da ke tare da ƙungiyar, sai kuma wani balarabe na daban."
Haka nan rundunar sojin ta saki wasu hotuna inda ta bayyana mayaƙan da ta ce ƴan asalin ƙasashen wae ne.
Akwai yiwuwar cewa Abu ishaq ɗin da sojojin Najeriya suka ambata shi ne Abu Ishaq al-Maqdisi, inda "al-Maqdisi" ke nuna cewa ɗan Falasdinu - wanda aka gani a wani bidiyon ISWAP na watan Disamban 2024.











