Me ya bambanta aikin Nuhu Ribadu da sabon ofishin tsaron cikin gida na Najeriya?

Asalin hoton, BAYO/RIBADU/X
Tun bayan da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Manjo Janar Adeyinka Famadewa mai ritaya a matsayin babban mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tsaron cikin gida, ake ta samun ce-ce-ku-ce kan ko mene ne bambancin sabon ofishin da na ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro na ƙasa da Nuhu Ribadu ke jagoranta.
An sanar da wannan naɗi ne a ranar Litinin 11 ga watan Mayun 2026 ta cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya fitar.
A cewar sanarwar, naɗin Famadewa wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na ƙarfafa tsaron cikin gida da inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.
Sanarwar ta ce an zaɓi tsohon hafsan sojan ne saboda ƙwarewarsa, dabarunsa da kuma gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa tsarin tsaron Najeriya.
Wannan sabon naɗi na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fama da matsalolin tsaro da suka haɗa da hare-haren 'yan bindiga, ayyukan ta'addanci da kuma rahotannin yunƙurin juyin mulki.
To ko mene ne bambancin wannan sabon matsayi na babban mai bai wa shugaban ƙasa shawarwari kan tsaron cikin gida da na mai ba shi shawarwari kan harkokin tsaro?
Bambancin ofishin Famadewa da na Nuhu Ribadu

Asalin hoton, Ribaɗu/Facebook
Da yake bayani kan wannan batu, Kwamared Dr. Abdullahi Yelwa, masanin harkokin tsaro kuma babban malami a sashen nazarin muggan ɗabi'u da daƙile su na kwalejin kimiyyar ƙere-ƙere da ke Bauchi, ya ce akwai bambanci tsakanin sabon ofishin da kuma ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro na ƙasa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Shi wannan babban mai ba da shawara ga shugaba Tinubu kan harkokin tsaro na cikin gida wanda aka naɗa shi sabo, ayyukansa sun sha bamban da na mai ba da shawara kan harkokin tsaro duk da cewa akwai sarƙaƙiya daga sunayensu domin idan aka ɗauki sunan kaɗai ana iya rikirkita."
Ya bayyana cewa sabon ofishin zai fi mayar da hankali ne kan hukumomin da ke ƙarƙashin ma'aikatar harkokin cikin gida.
"Ayyukan da ake sa ran wannan sabon mai ba da shawwarwari zai mayar da hankali a kai suna da nasaba da ayyuka irin na kulawa da hukumomin shige da fice da na hukumar civil defense wato NSCDC. Wannan ofishin na da alaƙa da ministan cikin gida."
Ya kuma ƙara da cewa daga cikin ayyukan sabon ofishin akwai samar da dabarun kare muhimman kadarorin gwamnati da kuma hana shigo da makamai da miyagun ƙwayoyi da ke haddasa matsalar tsaro.
"Dalilin wannan sabon ofishi shi ne mayar da hankali kan dabaru da shawarwari na yadda za a tsare muhimman dukiyoyi na gwamnati sannan a daƙile shigo da abubuwa musamman makamai da kayan maye waɗanda suke kawo tasgaro ga tsaron ƙasa."
Ayyukan ofishin Nuhu Ribadu

Asalin hoton, Ribaɗu/Facebook
Dakta Yelwa ya ƙara da cewa babban aikin kula da hukumomin tsaro na kai tsaye, kamar soja da ƴansanda har yanzu yana ƙarƙashin ofishin Nuhu Ribadu.
"Shi kuma mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ayyukansa sun karkata ne wajen hukumomi irin su 'yansanda da soja wato ma'aikatar harkokin 'yansanda da na soji da DSS da NIA da dai sauransu," a cewar Yelwa.
"Wannan na nufin kenan asalin hidimar tsaro dai har yanzu na ƙarƙashin Nuhu Ribadu saboda sabon ofishin da Tinubu ya naɗa hidimomi ne waɗanda a kaikaice suke da nasaba da tsaro amma ba lallai hukumomin da suke fuskantar hidimar tsaro kai tsaye ba."
'Sarƙaƙiyar' da ke tsakanin ofisoshin biyu
Sai dai ya yi gargadin cewa rashin tsayayyen tsarin aiki a Najeriya na iya sa shugaban ƙasa ya bai wa sabon ofishin wasu ayyukan da ke ƙarƙashin ofishin NSA.
"Najeriya ba wata tsari take da shi tsayayye da ke aiki ba. Abin da muke da shi shi ne son ran shugaban ƙasa, don haka yana iya ɗibar abubuwan da suka shafi ofishin Nuhu Ribadu ya koma yi da sabon mai ba da shawarwarin da ya naɗa."
Dr. Yelwa ya ce akwai masu kallon ƙirƙirar sabon ofishin a matsayin wata kishiya ga ofishin Nuhu Ribadu, musamman idan aka yi la'akari da matsin lambar siyasa da ake ciki kafin zaɓe mai zuwa.
Shi ma Kyaftin Sadiq Garba mai ritaya wanda masanin tsaro ne ya ce "lallai idan ba a fito da haƙiƙanin aikin sabon ofis ɗin ba to za a rinƙa samun karo da arangama."
Dangane da ko an ƙirƙiri ofishin ne domin kishiyantar ofishin mai ba wa shugaba Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu sakamakon rashin jituwa da ake ta yadawa akwai tsakaninsu, sai mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Abdul'aziz Abdul'aziz ya ce "sam babu ƙanshin gaskiya."
Abdul'aziz ya ce "kowane ofis yana da ayyukansa daban da ɗayan kuma duka suna da goyon bayan tsarin dokar Najeriya."
Mece ce hikimar naɗin Adeyinka Famadewa ?

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Dakta Abdullahi Yelwa Masanin tsaron ya bayyana cewa sabon wanda aka naɗa, Manjo Janar Adeyinka Famadewa mai ritaya, na da gogewa da ƙwarewar da za su iya taimakawa wajen inganta tsaro idan aka ba shi cikakken goyon baya.
Masanin ya ce Famadewa ba sabon mutum ba ne a harkokin tsaro, domin ya taɓa aiki kai tsaye a irin wannan ofishi a baya tsakanin 2015 zuwa 2021 a matsayin babban jami'in kula da tsare-tsare a lokacin da Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro daban-daban.
Ya bayyana cewa a lokacin da Famadewa ke aiki a fannin, an fara samun matsalolin garkuwa da mutane da kuma wasu rikice-rikicen tsaro da suka addabi ƙasar.
An san shi da taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsarin haɗa bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro na Najeriya.
Shi ne ya jagoranci kafa cibiyar haɗa bayanan sirri ta Intelligence Fusion Centre (IFC), wadda ta haɗa hukumomi kamar DSS da NIA da DIA da 'yansanda da rundunar soji domin inganta musayar bayanai da martani ga barazanar tsaro.
Dr. Yelwa ya ƙara da cewa Famadewa ya taɓa taka rawa wajen ayyukan da suka shafi daƙile cin hanci da rashawa da kuma hana ayyukan da ke kawo cikas ga tattalin arzikin ƙasa.
Bayan ritayarsa daga aikin soja, Famadewa ya yi aiki a matsayin babban mai bincike a cibiyar bincike da nazarin rundunar sojin Najeriya da ke Abuja.
A cewarsa, idan gwamnatin tarayya ta bai wa Famadewa cikakken goyon baya tare da damar amfani da ilimi da gogewar da ya tara tsawon shekaru, akwai yiwuwar a samu canji a ɓangaren tsaro.






