Jam'iyyar ADC ta zargi Tinubu da 'kafa NDC don raunata' ƴan adawa

Asalin hoton, OTHERS
Mahawara ta sake ɓarkewa tsakanin jam'iyyar ADC da jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya kan zargin da ADCn ta yi cewa Shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyarsa ta APC da hannu wajen kafa jam'iyyar NDC.
A cewar jam'iyyar ta ADC, hakan wata dabara ce ta raba kan masu jefa ƙuri'a ga jam'iyyun hamayya gabanin zaɓukan da 2027 da ke ƙaratowa.
Sai dai, jam'iyyar APC ta mayar da martani inda ta yi ƙoƙarin wanke kanta daga waɗannan zarge-zarge.
Amma Jam'iyyar ta ADC ta yi zargin cewar an kafa NDC ne domin raunana haɗin kai da ke tsakanin ƴan adawa da jam'iyyun adawar masu ƙarfi da za su ƙalubalanci gwamnati mai ci, maimakon bunƙasa harkokin dimokaraɗiyya ta gaskiya.
A ƙarshen makon da ya gabata ne ƴan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin Labour da NNPP a zaɓen da ya gabata na 2023 Peter Obi da Rabi'u Musa Kwankwaso suka sanar da ficewa daga jam'iyyar ADC zuwa NDC.
Sai dai jam'iyyar ta ADC ta zargi APC da kitsa bi-ta-da-kulli domin haifar da koma-baya ga jam'iyyun siyasa kamar ta ADC, sakamakon ficewar Peter Obin da Kwankwaso.
Faisal Kabir ɗaya ne daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ta ADC a Najeriya, ya yi wa BBC bayani kan zargin da suka jima suna yi wa jam'iyyar ta APC na hana su rawar gaban hantsi na sake futowa fili ƙarar, musamman idan aka yi la'akari da yadda aka amince da jam'iyyar NDC aka yi mata rajista.
Haka kuma ya nanata cewar wannan kisisina ce ta neman raunata ADC da gwamnatin Bola Tinubu ta sa a gaba gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
"Ka ga ita wannan jam'iyya ta NDC, an nemi a yi mata rajista a 2017 amma INEC ta ce ba ta cika wasu ƙa'idoji ba.
''Yanzu kuma sai ga shi bayan shekara wajen tara, ba a sake neman wannan rajista ba, ba a je kotu ba, sai yanzu aka ce sun tafi kotu kuma kotu ta ce a ba su rajista," a cewar Faisal Kabir.
Haka kuma ya ce: ''Domin gwamnati tana da manufa a kansu ta ganin ta raba kan 'yan adawa, ta yi amfani da su ta jawo wasu daga cikin 'yan adawar da muke tare da su a jam'iyya daya ta saka su a ciki, wanda hakan ya saɓa da dokar zabe ta Electoral Act,' in ji shi.
Martanin APC kan zargin
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To sai dai, jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC ta nesanta kanta daga waɗannan zarge-zarge, inda ta ce da yan jam'iyyar ta ADC sun faɗa cikin ruɗani shi ya sa suke wannan fagamniya.
Malam Bala Ibrahim, shi ne Daraktan yaɗa labaran jam'iyyar ta APC a Najeriya ya ce 'babu wani abu da ke faruwa a Najeriya ba su dora alhakinsa a kan jam'iyyar APC ba'. in ji shi.
"Ni tsoron da nake ji ma shi ne, nan gaba idan kafofin yada labarai suna musu tambayoyi masu zafi, za su dora laifin a kan APC su ce APC ce ta kafa su"
"Babu wata alaka tsakanin jam'iyyar NDC da jam'iyyarmu ta APC, ya kamata su fuskanci matsalolin da ke damunsu, su yi kokari su magance su, su yi adawa da zafin jiki, ba adawa irin wannan ta zargi-zargi-zargi da ba su da tushe balle makama ba."
A ranar 30 ga watan Afirilu ne kotun ƙoli ta Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark.
Nigerian Democratic Congress (NDC) na ɗaya daga cikin jam'iyyun siyasa biyu da INEC ta yi wa rajista a baya-bayan nan.
Abin da hakan ke nufi shi ne an yi wa jam'iyyar rajista a 2026 a hukumance.
A watan Fabarairun 2026 ne INEC ta miƙa wa NDC takarkar shaidar zama jam'iyya.
Bayanan da ke shafin jam'iyyar na intanet, sun nuna cewa tana da rassa a ƙananan hukumomin Najeriya 774, yayin da fiye da mutum miliyan ɗaya ne suka yi rajista da jam'iyyar.
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Henry Seriake Dickson ne ya kafa jam'iyyar.
A cewarsa tun 2017 ya fara yunƙurin yi wa NDCn rajista, amma yunƙurin nasa ya gamu da cikas, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Sai dai daga bisani NDCn ta samu wasiƙa daga INEC cewa alamar jam'iyyar ta yatsu biyu, ta yi kama da ta da jam'iyyar APC mai alamar tsintsiya.
Nan take NDC ta shigar da INEC ƙara gaban kotu kan batun, inda kotu ta ce alamomin jam'iyyun biyu ba su yi kama ba, don haka INEC ta yi mata rajista.









