Yanayin baccin da ke iya jefa jariranku cikin haɗari

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Divya Talwar
- Marubuci, Marthe de Ferrer
- Marubuci, Amy Johnston
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Investigations
- Lokacin karatu: Minti 9
Wasu da suka kira kansu ƙwararru kan yanayin barcin jarirai na bayar da shawara da ka iya jefa jariran cikin gagarumin haɗari ko ma janyo mutuwarsu, kamar yadda ƙwararrun likitoci suka bayyana a wani bincike na BBC.
Mun naɗi ɗaya daga cikinsu a asirce yana bai wa wakilinmu shawarar guje wa kwantar da jariri rub-da-ciki, wani salon kwanciya da aka gano yana janyo mutuwar ba-zata a tsakanin jarirai - matasalar da a Turance ake kira (sudden infant death syndrome, Sids).
Hukumar Lafiya ta Birtaniya NHS tana yawan bayar da shawarar "kwantar da jarirai a bayansu" a kan gadonsu, daga haihuwarsu zuwa shekara ɗaya domin rage haɗarin matsalar Sids. Ya kamata katifar ta zama mai ƙarfi wadda ruwa ba ya ratsa ta.
Wata da ta yi iƙirarin ƙwararriya ce ta bayar da shawarar a rika shimfiɗa tawul a kan gadon jariran - wani tsari da wata ƙungiya mai ba da shawara kan yanayin barcin jarirai mai suna Lullaby Trust a Turance ta ce shi ma yana ƙara haɗarin Sids da kuma mutuwar fuju'a.

Ƙwararrun likitoci da suka kalli bidiyon sirrin sun ce abin da suka gani ya sa sun ji jikinsu ba daɗi kuma sun shiga tashin hankali.
Bayar da shawara kan tsarin barcin jarirai wata sana'a ce mara ƙa'ida da ke bunƙasa, in ji su, sakamakon ƙarancin shawarwarin da ake bai wa iyaye bayan haihuwa. Sannan sun ce duk da sun san mutane da yawa suna bayar da shawarwari masu muhimmanci kan barci ba tare da haɗari ba, sun yi gargaɗi cewa akwai wani ɓangare mai illa.
"Ƙwararru kan tsarin barcin jarirai" sun yi fice a shafukan sada zumunta sannan tawagar masu bincikenmu sun fahimci yadda masana'antar yake.
Iyaye da dama sun bayyana damuwarsu ga BBC.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da yawansu sun nuna wasu mata biyu da suka biya domin su ba su shawara - Alison Scott-Wright da Lisa Clegg. Suna da mabiya masu yawa a shafin Instagram, sun samu goyon bayan fitattun mutane sannan sun wallafa litattafai.
Shawarar da Scott-Wright ta bayar tsagwaron mugunta ce, wata uwa da shaida mana.
Wata uwa da ta gana da Clegg game da yaranta biyu masu tsiran shekaru tsakaninsu, ta ce ta yi da-na-sanin sanya jariranta cikin haɗari ta hanyar bin shawarar zuba ƙyallaye masu laushi da wasu ƙananan kaya a kan gadonsu.
Scott-Wright ta shaida wa BBC cewa shawarar da take bayarwa ta taimaka wa jarirai da yara da iyaye da iyalai da dama". Ta ce tana ɗaukan lamarin da ya shafi kulawar jarirai da iyalansu da muhimmancin gaske".
Clegg ta ce "ta shawarci dubban iyaye" game da barci kuma babu guda cikin shawarwarinta da suka jefa rayuwar jarirai cikin haɗari".
Mun tura wakiliyarmu don yin bincike a asirce inda ta nemi ta zauna don samun shawarar matan biyu inda ta bayyana kanta a matsayin uwa ga jariri ɗan mako tara da ke yawan tashi cikin dare.
Mako tara ya faɗa cikin lokacin da aka fi yawan samun matsalar Sids tsakanin wata ɗaya zuwa shida.
Sids na nufin mutuwar ba-zata ta lafiyayyen jariri da shekarunsa suka kai shekara ɗaya.
A shekarar 2022, shekarar baya-bayan nan da ke da cikakkun alƙaluma, an samu mace-macen yara ƴan ƙasa da shekara ɗaya har197 a Ingila da Wales, 16 a Scotland sai biyu a Arewacin Ireland.
Kowa na iya kiran kanshi masani kan barci matuƙar babu doka. Scott-Wright da Clegg suna kuma kiran kansu "malamar jinya" - wani matsayi da ya shafi jigila da jarirai ba tare da ƙa'ida ba.
Sakataren Lafiya na Birtaniya Wes Streeting ya ce gwamnati ta shirya magance matsalar ta hanyar taƙaita wa mutane amfani da sunan "malamar jinya" har sai sun cancanta.
Hakan ya faru ne sakamakon binciken da aka yi kan mutuwar jikan koci Steve Bruce ɗan wata huɗu mai suna Madison Bruce Smith. Mai bincike kan mutuwar fuju'a ya yanke cewa jaririn ya mutu, "yayin da yake barci a gadonsa kasancewar an kwantar da shi a yanayin da bai kamata ba" bayan da wata da ta kira kanta malamar jinya ta jarirai ta yi.
Streeting ya shaida wa BBC cewa "shawarwari marasa tushe daga wasu da ke kiran kansu ƙwararru na jefa rayuwar jarirai cikin haɗari - kuma dole a kawo ƙarshen hakan".
Iyalin Bruce Smith na neman a ƙara sa ido sannan a tilasta horar da duk mutanen da ke aikin kula da barcin jarirai da ƙananan yara.
"Bai kamata a samu iyaye da za su yi alamar tambaya kan ƙwarewar mutumin da suka amincewa ya kula da jaririnsu ba," suka shaida wa BBC.
'Mun shiga matsananciyar damuwa'
Lokacin da jaririn Emily wadda haihuwarta ta farko ke nan ya kai wata huɗu, ya soma farkawa cikin dare bayan kowace sa'a, abin da ya sanya ta cikin damuwa.
Bayan da ta yi ta duba shawarwari kan barci a shafin Instagram, ta yi ta ganin sunan Alison Scott-Wright, da aka fi sani da "Mai Sanya Barci cikin Sauƙi".
Scott-Wright wadda ke da dubban mabiya a shafin Instagram, ta fito a shirin This Morning da kafar yaɗa labarai ta ITV ke yi kuma tana da littafi da kamfanin buga litattafai na Penguin Random House ya buga, wanda kuma ya samu goyon bayan fitattu har da ƴar fim da ke gabatar da shiri kan tarbiyyar yara Giovanna Fletcher.
Cikin wata sanarwa, ITV ta ce Scott-Wright ta taɓa bayyana a matsayin baƙuwa a shirin This Morning a 2024 a matsayin ƙwararriya mai sanya jarirai da yara barci cikin sauƙi. Kamfanin Penguin Random House da Fletcher ba su ce komai ba kan buƙatar BBC ta neman su yi martani.
Emily, wadda ta biya sama da fam 500 domin samun shawara ta hanyar bidiyo, ta ce Scott-Wright ta faɗa mata cewa ɗanta yana fama da gagarumar matsalar dawowar abinci sannan yana fama da ciwon jiki.

Scott-Wright ta bayar da shawarar a yi masa kwanciyar rub da ciki, in ji Emily, sannan ta ba shi maganin yawan dawowar abincin da yake ci - duk da cewa Scott-Wright ba ta ga jaririn ba kafin bayar da shawarwarin.
"Abin tsoro ne wani ya gano yarona na da matsala sannan kuma ya ba ni shawarar yin abin da bai kamata ba."
Scott-Wright ta kuma ba ta shawarar bai wa jaririn madara a maimakon shayarwa - wani abu da ba ta tsara yi ba, kamar yadda Emily ta shaida. Ta ce babu wani lokaci da Scott-Wright ta nemi ta ga likita.
Scott-Wright ta faɗa wa BBC cewa "ba ta taɓa iƙirarin ita likita ba ce" sannan gudunmawar da take bai wa iyali ba madadi ba ne na shawarar ƙwararrrun likitoci.
Emily ba ta bi shawarwarin da Scott-Wright ta ba ta ba, amma wasu iyayen sun faɗa mana cewa sun bi shawarwarinta da suka saɓa wa hukumar lafiya ta Birtaniya saboda sun kasance masu zaƙuwa kuma masu rauni.
Binciken sirri
Mun biya domin samun shawarar Scott-Wright ta hanyar bidiyo.
Mun gabatar da buƙatarmu dangane da abubuwan da wakiliyarmu ta fuskanta kan ɗiyarta shekaru biyu da suka gabata.
Wakiliyarmu ta gabatar da batun da ya shafi lafiyayyen jariri da ake shayarwa wanda ke fama da barci.
Duk da cewa damuwar ta barci kaɗai, Scott-Wright ta faɗa wa wakiliyarmu cewa akwai matsala ta narkewar abinci inda kuma ta buƙaci a yi masa gwaje-gwaje har da na CMPA yanayin da jariri ke samun matsala idan ya sha madarar shanu da yawan dawowar abinci da matsalar nan ta tongue-tie da ake haifar yaro da nama a saman harshensa.
Ta kuma ba da shawarar cewa abu ne mai kyau idan wakiliyarmu ta daina bai wa jaririnta madara, ba tare da faɗa mata ta tuntuɓi likitoci ba.
Babu wani lokaci da aka nuna wa Scott-Wright jariri ba.
Lokacin da take ba da shawarar, Scott-Wright ta faɗa wakiliyarmu cewa ta daɗe tana uguwarzoma amma a yanzu ba ta da lasisin ci gaba da aikin, inda ta ƙara da cewa "babu ƙwarewar da mutum ke buƙata kan abin da nake yi".
Mun nuna wa wasu ƙwararrun likitoci bidiyon da aka naɗa a asirce - unguwarzoma a hukumar Lafiya ta Birtaniya da ƙwararriya kan shayarwa Olivia Hinge da likitar ƙananan yara a hukumar Lafiya ta Birtaniya Dr Lillie Parker.

Sun ce matsalolin da Scott-Wright ta gano ba su yi daidai da alamomin da wakiliyarmu ta yi bayani ba. Sun kuma gano lokuta da dama da Scott-Wright ta yi iƙirarin da ba daidai ba.
Hinge ta ce ta zaɓi ta ba da shawarwarin lafiyar da ba ta da ƙwarewa a kai.
Bayan kusan rabin sa'a muna tattaunawa da ita, Scott-Wright ta kawo batun yi wa jaririn wakliyarmu kwanciyar rub da ciki, abin da ta ce ya kawo "babban sauyi".
"Ba zan ce muku ku yi kaza ba, amma kowane jariri da nake kula da shi yana kwaniyar rub da ciki," in ji Scott-Wright. "Ban taɓa kwanciyar rub da ciki ba, ban yarda da shi ba."
Binciken da aka yi kan mutuwar bazata a faɗin duniya, tsawon shekaru, ya nuna cewa kwanciyar rub da ciki na ƙara haɗarin jarirai su yi mutuwar fuju'a, a waɗannan watanni na farko". a cewar Farfesa Helen Ball, daraktar cibiyar Durham da ke nazari kan jarirai da tsarin barcinsu.
'Abu ne mai matuƙar haɗari'
Likitar ƙananan yara a hukumar lafiya ta Birtaniya Lillie Parker ta faɗa mana: "Wannan shi ne abu mafi haɗari da ta faɗa. Ba wai muna magana kan ƙaramar matsala ba ce, muna magana ne kan jaririn da ya yi mutuwar ba zata."
Yayin zamanmu, Scott-Wright, lokuta da dama ta ce "ba zan tilasta muku yin haka ba" lokacin da take magana kan kwanciyar rub da ciki.
Sai dai Parker ta ce hakan bai wanke haɗarin da ke tattare cikin bayaninta ba.
"Ta yi ta nanata cewa ba za ta iya ba da wannan shawarar ba amma kuma ta wata fuskar tana nuna yanayi na tilastawa kan shawarar da take bayarwa.
Lokacin tattaunawar, Scott-Wright kwanciyar rub da ciki na iya sanya wakiliyarmu cikin tsoro amma ta ci gaba da ba da shawarar sanya na'urar da ke jin numfashi a ƙarƙashin katifa - tana iƙirarin cewa "babu damuwa kan yanayin da suka kwanta."
Lullaby Trust ya faɗa mana cewa babu wata hujja da ke nuna cewa sanya irin na'urorin suna rage afkuwar Sids kuma ba za a dogara da su ba don kare masu kwanciyar rub da ciki".
Parker ta ce bai wa uwa irin wannan shawarar abu ne mai haɗari. Na'urorin na ankararwa da zarar jariri ya daina numfashi, in ji ta, ma'ana na'urorin kawai suna ankararwa ne a lokacin da mummunan yanayi ya faru". A lokacin kuma uwa ta riga ta shiga yanayi na firgici.
Mun tuntuɓi Scott-Wright bayan da aka naɗi bidiyon a asirce. Ta shaida mana cewa iyaye da dama da suka nemi shawararta sun riga sun je hukumar lafiya ta Birtaniya da wurin ƙwararru amma ba a nusantar da su abubuwan da ya kamata su yi ba" game da damuwar da suka nuna kan jariransu.
Aikinta shi ne ta tallafa wa iyaye su magance ƙalubalensu "ba wai a madadin shawarar likita ba", in ji ta. Scott-Wright ba ta amsa tambayoyin da muka yi mata ba kan kwanciyar rub da ciki.

Bincikenmu ya kuma bankaɗo mummunar shawara daga Lisa Clegg, da mabiyanta 100,000 a shafin Instagram suka fi sani da "Ƙwararriya kan harkar jarirai".
Wakiliyarmu mai binciken sirrin ta gabatar da matsalolin da ta gabatar wa Scott-Wright.
Clegg ta karɓo fam 200 ga minti 50 na kiran waya da kuma tallafi na tsawon wata guda wanda a nan za a riƙa badawa ta imel da saƙon karta-kwana.
Duk da cewa ba ta tallata kwanciyar rub da ciki ba sannan kuma ba ta yi iƙirarin samun ƙwarewar likita ba, ta dai bayar da shawarwarin barci da suka ci karo da na hukumar NHS.
Ta ba da shawarar sanya ƙyallaye masu laushi da sanya tawul da aka nannaɗe a gadon jariri inda ta ce a guji sanya kaya kusa da fuskar jariri.
Sanya tawul da aka nannaɗe a kowane gefe na jariri yayin barci, a cewar Clegg, zai sa jariri ya ji kamar yana hannun mahaifiyarsa.
Daga bisa yayin tattaunawar, Clegg ta sake bayyana cewa tawul ɗin zai hana jaririn mirginawa.
Iyaye da dama sun tura mana hotuna da suka ce Clegg ta tura musu a matsayin dabaru na yadda za su yi hakan. Hotunan sun nuna jarirai da tawul da ƙyallaye kusa da fuskoki da kuma kawunan jariran.
A yi taka tsan-tsan
Farfess Ball ta nazarci duka bidiyon ina kuma ta bai wa Kamfanin Lullaby Trust shawara.
Ball da ƙwararrun likitoci sun shaida mana cewa abin da ke cikin hotunan abin kaɗuwa ne kuma mai haɗari.
"Akwai gagarumin haɗari a ajiye kaya da tawul a gadon jariri. Jarirai za su iya fizgo su su kuma rufe kansu da su... wanda haɗari ne ga numfashi." in ji Ball.
Clegg ta yi wa BBC martani inda ta ce ba ta san iyalan "da suka nuna damuwa game da shawarwarin da take bayarwa ba - sannan kuma iyaye suna zuwa wajenta saboda ba sa samun tallafi daga NHS.
Ta ƙara da cewa duk da cewa akwai shawarwari ga iyaye...kowa na da ikon ya zaɓi abin da ya fi kwanta musu a rai su kuma watsar da wanda bai yi musu ba."
Shugabar Lullaby Trust Jenny Ward ta ce ƙara sa ido zai tabbatar da an samu tsare-tsare maus aminci. Ya kamata a yi taka tsan-tsan da duk wata shawara da ta yi hannun riga da ƙa'ida", in ji ta.
Ɗan Emily a yanzu ya kai wata tara kuma yana cikin ƙoshin lafiya.











