KAI TSAYE, Sabbin ƴan wasa huɗu sun lashe La Liga a karon farko a Barcelona

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 11 zuwa 16 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

  • Barcelona ta ɗauki kofin La Liga a El Clasico karon farko a shekara 97
  • Arsenal na daf da lashe Premier League na farko tun bayan 2004
  • Premier League: Tottenham za ta karɓi bakuncin Leeds United
  • Saura wasa ɗaya a kammala Premier League ta Najeriya
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp

Rahoto kai-tsaye

  1. Marmoush zai kara yin fice a sauran wasan Man City a kakar nan, Manchester City

    Pep Guardiola ya bayyana cewa Omar Marmoush zai taka muhimmiyar rawa a wasannin da suka rage wa Manchester City a kakar nan

    City na da sauran wasa huɗu kafin kakar nan ta karkare, ciki har da wasan ƙarshe a FA Cup da Chelsea a Wembley - kenan cikin kwana 12, ƙungiyar za ta yi fatan lashe dukkan wasannin da suka rage mata.

    Ɗan wasan tawagar Masar, Marmoush bai samu damar taka leda sosai ba a wannan kakar, inda ya fara da karawa bakwai a Premier League. Sai dai ya nuna ƙwarewarsa lokacin da ya zura ƙwallo a raga a wasan da City ta doke Brentford 3-0, wanda ya shiga canjin ɗan wasa a ranar Asabar.

    Guardiola ya ce yana sa ran Marmoush da sauran ƴan wasan da ba sa fara wasa akai-akai, za su kasance cikin shiri idan aka nemi gudummawarsu a koda yaushe.

    Marmoush yana sha zama a benci ne saboda kasancewar Erling Haaland, wanda ya ci ƙwallonsa ta 50 a bana yana kan ganiya.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  2. , Daga Jaridu

    Yanzu dai ta tabbata cewa kungiyoyin Firimiya na - Arsenal, da Liverpool, da kuma Manchester United suna da damar samun dan bayan Italiya Andrea Cambiaso, bayan da Juventus ta ce za ta iya sakin dan wasan mai shekara 26 a bazaran na. (Teamtalk)

    Har yanzu Atletico Madrid tana son sayen dan wasan tsakiya na Wolves, Joao Gomes, amma kuma ta ce ba za ta biya sama da yuro miliyan 40 ba a kan dan Brazil din mai shekara 25.(Marca)

    Dan wasan tsakiya na Scotland Bailey Rice, mai shekara 19, na shirin barin Rangers a bazaran nan kuma Aston Villa na daga kungiyoyin Firmiya da suke son sayenshi. (Football Insider)

    Ipswich Town na tattara sunayen masu horarwa ko da kociyanta Kieran McKenna zai samu aikin horad da wata kungiya a gasar Firmiya a bazaran nan. (Sun)

    Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Sabbin ƴan wasa huɗu sun lashe La Liga a karon farko a Barcelona, La Liga

    Har yanzu Barcelona na ci gaba da murnar lashe kofin La Liga karo na biyu a jere, bayan nasarar da ta samu a El Clásico a filin Spotify Camp Nou a kan Real Madrid.

    Wannan ne karon farko da sababbin ƴan wasa huɗu — Joan Garcia da Marcus Rashford daJoão Cancelo da kuma Roony Bardghji — suka lashe gasar La Liga a rayuwarsu.

    Uku daga cikinsu sun shiga Barça kan fara kakar bana. Ta ɗauki Joan Garcia domin ƙarfafa matsayin mai tsaron raga, sannan ta sayi matashin ɗan wasa Roony Bardghji saboda bajintarsa. Haka kuma ta ɗauki aron Marcus Rashford daga Manchester United..

    A wannan kakar, matasa huɗu — Jofre Torrens, Toni Fernández, Xavi Espart da Tommy Marqués — sun fara bugawa Barcelona wasansu na farko, kuma sun taimaka wajen samun wannan nasara.

    Sauran matasan daga makarantar koyon tamaula taƙungiyar, wato Álvaro Cortés da Eder Aller, duk da cewa ba su fara bugawa ƙungiyar wasan farko ba, sun yi atisaye tare da manyan ƴan wasan a mafi yawan kakar nan, kuma ana ɗaukarsu cikin waɗanda suka taka rawa a wannan nasara.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  4. West Ham za ta bi bahasin dalilin soke ƙwallon da ta ci Arsenal, Premier League

    West Ham United na shirin tuntuɓar kwamitin alkalai na Professional Game Match Officials Limited (PGMO) kan jin dalilin soke ƙwallon da suka ci a ƙarshen lokaci a wasa da Arsenal.

    A ranar ta Lahadi West Ham ta ci ƙwallon da take tunanin za ta taimaka mata tsira daga faduwa a gasar bana, wanda Callum Wilson ya zura a raga.

    To sai dai an soke ƙwallon, bayan da alakalin wasa ya je yaduba lamarin ya kuma soke sakamakon, saboda Pablo Fornals na West Ham ya yi wa mai tsaron ragar Arsenal, David Raya keta.

    West Ham ta damu da aka soke ƙwallon, shi ya sa take son a fayyace mata daliln hakan, wadda take ta ukun karshen teburi a kakar bana.

    Haka kuma ƙungiyar za ta nemi saukin tattaunawa da aka yi tsakanin tsakanin alkalin wasa, Chris Kavanagh da jami’in da ya kula da VAR, Darren England.

    Daga ƙarshe Arsenal ta yi nasara da ci 1-0, wanda ya sa ta ƙara tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City mai biye da ita. Wannan sakamakon ya kuma ƙara sanya makomar West Ham cikin haɗari, domin tana matsayi na 18, yayin da Tottenham ke sama da ita da maki ɗaya kafin karawarsu da Leeds United ranar Litinin.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  5. , Daga Jaridu

    Manchester United ta yi watsi da maganganun da ake yi cewa za ta bar dan wasanta na gaba na gefe Amad Diallo, dan Ivory Coast, mai shekara 23 ya bar kungiyar a bazaran nan. (Teamtalk)

    Liverpool ta tattauna da Real Madrid a kan dan takaitaccen aikin da Xabi Alonso ya yi da kungiyar ta Sifaniya, a shirin da kungiyar ta Firimiya ke yi na duba yuwuwar bai wa tsohon dan wasan nata na tsakiya aikin kociya. (AS )

    Everton na tattaunawa da John Stones a kan yuwuwar komawar dan bayan na Ingila mai shekara 31, kungiyar idan ya bar Manchester City a bazaran nan. (Football Insider)

    Newcastle ta kusa rike matashin dan wasan tsakiya na Ingila Lewis Miley mai shekara 20 na tsawon lokaci inda take dab da cimma yarjejeniya da shi ta kwantiragi na tsawon shekaru. (Sun)

    Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Liverpool ta fitar da hoton wani abin da za ta gina don tunawa da marigayi ɗan wasanta Diogo Jota da ɗan’uwansa Andre Silva bayan rasuwarsu a lokacin bazarar da ta gabata.

    Jota mai shekara 28 da Andre Silva mai shekara 25, wanda ke buga wa Penafiel wasa a rukuni na biyu a Portugal, sun mutu ne a wani hatsarin mota a ranar 3 ga Yuli a yankin Zamora a ƙasar Spain.

    Abin tunawar yana ɗauke da siffar zuciya mai lankwasawa, wanda ke nuni da yadda Jota ke murnar cin ƙwallo. Haka kuma yana ɗauke da lambobin rigunansu 20 da 30, tare da kalmomin waƙar Jota da magoya bayan Liverpool ke rerawa a minti na 20 a kowane wasa.

    An sanya wa abin tunawar suna “Forever 20”, kuma Liverpool ta ce tana girmama rayuwar Jota da Andre Silva, dangantakarsu ta ƴan’uwa da kuma ƙauna da girmamawar da iyalai da abokan wasa da magoya baya a duniya.

    Za a kafa abin tunawar a filin Anfield a titin 97 Avenue. An kuma sake amfani da kayayyakin girmamawa da magoya baya suka ajiye a wajen Anfield, bayan mutuwar Jota, inda aka haɗa su cikin dutsen ginin abin tunawar.

    Liverpool ba ta sanar da ranar ƙaddamar da abin tunawar ba tukuna, amma ta ce za ta bayyana ranar nan gaba.

    Jota ya koma Liverpool daga Wolverhampton Wanderers a shekarar 2020, inda ya zura ƙwallo 65 a wasa 182 da ya buga wa ƙungiyar. Ya taimaka musu lashe Premier League da FA Cup da kuma kofunan EFL Cup guda biyu a lokacin da yake Merseyside.

    Jota

    Asalin hoton, Liverpool FC

  7. Dybala zai buga wa Roma wasan karshe a Serie A ranar Lahadi, Roma

    Ɗan wasan tawagar Argentina, Paulo Dybala ya ce karawar hamayya ta Serie A da za su buga da S.S. Lazio ranar Lahadi na iya zama na ƙarshe a gida da zai buga wa AS Roma, saboda har yanzu ƙungiyar ba ta tuntube shi domin tattauna makomarsa ba.

    Mai shekara 32, wanda ya shafe shekara bakwai a Juventus FC, ya koma Roma a shekarar 2022, kuma ya taimaka musu kai wa wasan ƙarshe a wasan karshe a Europa League a kakarsa ta farko.

    Sai dai Dybala ya sha fama da jinya a wannan kakar, sannan an yi masa tiyata a watan Maris, lamarin da ya sa ya rasa kusan watanni huɗu bai taka leda ba.

    Dybala ya bayar da ƙwallo aka zura a raga a wasan da Roma ta doke Parma Calcio 1913 da ci 3-2, wanda ya sa take maki iri ɗaya da AC Milan a mataki na huɗu a kan teburi, domin neman gurbin Champions League a baɗi.

    Dybala

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni

    Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu ke sanar da ku wainar da ake toyawa daga wannan ranar zuwa Asabar 18 ga watan Afirilu.

    Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.