Yadda batun tsayar da ɗan takarar haɗin gwiwa ya raba kan 'yan adawar Najeriya

.
Bayanan hoto, '
Lokacin karatu: Minti 3

Da alama sanarwar wasu jam'iyyun hamayyar Najeriya ta baya baya nan ta yiwuwar tsayar da dan takarar gamin gambiza a zaben 2027 ba ta samu shiga a wajen wasu daga cikin 'yan hamayyar kasar musamman wadanda suke ikirarin shugabantar wasu rassan jama'iyyun ba.

Idan ba ku manta ba dai a makon da ya gabata ne wasu jama'iyyun hamayyar kasar sama da goma suka bayyana wannan aniya, a wani kokari na kalubalantar shugaba Bola Ahmed Tinubu na APC a zaben mai zuwa.

Yayin wani gangamin jam'iyyun hamayya da aka gudanar a birnin Badun na jihar Oyo, jam'iyuun PDP da ADC, da Labour da kuma NNPP da sauransu, sun yi imaninn ba abu ne mai yiwuwa a iya kayar da shugaba Tinubu idan aka ki hada kai ba, saboda a cewarsu ''Yadda shugaba Tinubu ke amfani da karfin mulki wajen murkushe dimukradiyya''

Sai dai tun kafin a je ko ina, wasu bangarori biyu na jam'iyyar PDP da ADC da kuma jam'iyyar Labour sun sa kafa sun yi fatali da wannan taron da ya gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Bangarorin sun ce taron wani yanki ne kawai na 'yan siyasa ba wai na jam'iyyun adawa ba, don haka za su fito da nas tsari da zai tsayar da dan takarar da zai iya fafatawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Kwamitin gudanarwar PDP mai samun goyon bayan Wike ya yi bayyana cewa taron na a matsayin na yuyuyu, kuma sun wakilci kansu ne kawai ba wai jam'iyyun ba.

Bangaren na Wike sun ce wannan shure-shure ne da ba ya hana mutuwa, kuma taron na 'yan siyasa ne ba na jam'iyyun adawa ba.

Muhammad Jangudu, sakataren watsa labaran PDP na kasa, bangaren Wike ya shaida wa BBC Hausa cewa idan za a yi irin wannan taro kamata ya yi a duba su wanene halastattun shugabanni.

''Mu a wajenmu wannan taro ne na 'yan siyasa amma ba wai taro na jama'iyyun adawa ba, a wajen an ce Tanimu Turaki da Seyi Makinde su ne shugabannin PDP, shin a wajen hukumar zabe haka abun yake?'' inji shi.

Mahalarta taron 'yan adawa da aka yi a Ibadan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mahalarta taron 'yan adawa da aka yi a Ibadan

Ya kara da cewa ita kanta jama'iyyar ADC ba ta da shugabanci.

Ya ce ''Mu kiranmu shine jama'iyyun adawa su zo su shiga karkashin PDP a matsayinta na jama'iyya mafi karfi a Najerya don a samu nasara''

Kazalika, su ma a nasu martani, bangaren tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC a 2023 Dumebi Kachikwu da Nafi'u Bala Gombe ke jagoranta, sun nesanta kansu da wannan taron.

Honarabul Nafi'u Bala Gomben ya ce babu wani dan ADC da ya halarci taron face 'ya'yan jam'iyyar PDP.

Wadannan mutanen ba 'ya'yan jam'iyyar ADC bane, kuma muna sake tabbatarwa 'yan Najeriya cewa bamu je wajen wani taro na 'yan adawa ba, wasu 'yan PDP da suka wargaza jama'iyyarsu ne suke nema su bata mana suna, don haka mu a wajenmu wannan taron sharholiya ne kawai'' inji shi.

Hasalima dai baya ga bangaren na Wike da Nafi'u Bala, su ma bangaren Nenadi Usman na jam'iyyar Labour sun nesanta kansu da taron kolin jam'iyyun adawar a birnin na Badun. Haka ita ma jam'iyyar Accord ta ce zata dauki matakin kai karar wadanda suka kira kansu 'yan jam'iyyar da suka ce sun wakilce ta a taron kolin.

Mahalarta taron sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi da sauran wasu kusoshin hamayya.

Haka ma a cikin jam'iyyun da suka halarci taron akwai ADC, da PDP, da Labour, da NNPP, da PRP, da Accord, da APM, da (YP), da ADP, da sauransu.