Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nau'ikan cutar kansa 11 da ke bazuwa tsakanin matasa
Dalilan da ke haifar da ƙaruwar masu cutar kansa a cikin matasa masu shekara 20, 30 da kuma 40 sun jawo masana kimiyya kasa gane al'amarin tsawon shekaru.
Bradley Coombes, daga birnin Portsmouth, ya mutu yana da shekara 23 sakamakon kansar hanji. Mahaifiyarsa, Caroline Mousdale, ta ce duk da cewa ya fuskanci alamomin cutar kansar, hakan bai sa an mayar da hankali kan ɗan nata ba saboda an ce shekarunsa ba su kai ya kamu da ita ba.
Ya ce shi "matashi ne mai lafiya" wanda ke daf da sanya kwantiragin fara buga kwallo don more rayuwarsa. Babu wani abu da ya saka shi cikin haɗari, in ji ta.
Sai dai bayan shekararsa ta farko a makaranta, ya fara ramewa da kuma fuskantar ciwon ciki. Daga nan amai da gudawa ya biyo sai kuma jini a kashinsa.
Alamomin sun kasance na tsawon watanni 18 kafin a tabbatar yana ɗauke da cutar. Lokacin da ya je yin gwajin kashinsa, an faɗa masa cewa cutar ta girma sosai har tana hana na'urar gwaji shiga cikinsa.
Bradley Coombes ya mutu duk da tiyata da kuma magani da aka yi masa don shawo kan cutar.
Na'ukan cutar kansa 11 na ƙaruwa tsakanin matasa a Birtaniya, kamar yadda wani bincike ya nuna.
Har yanzu ba a kai ga gano dalilan da ke janyo haka ba. Sai dai, bincike ya nuna cewa ƙaruwar ƙiba na taka rawa sosai, duk da cewa ba shi kaɗai dalilin ba.
Masana kimiyya daga cibiyar binciken kansa a kwalejin Landan sun bayyana cewa har yanzu cutar kansa tsakanin matasa ba ta da yawa, kuma kowa zai iya rage barazanar kamuwa da cutar ta hanyar yin salon rayuwa mai lafiya.
"Ina jin kamar yadda iyaye da dama ke ji, cewa zai cika burinsa na kwallon kafa, cewa zai samu rayuwa mai inganci, sai dai hakan bai samu hakan ba sakamakon kasa gane cewa yana da cutar kansar hanji da wuri," in ji Caroline Mousdale.
Yana da wuya a gano dalilin da ya sa wani ke kamuwa da kansa. Sai dai, tawagar masana kimiyya sun yi nazari kan cutar kansa da kuma salon rayuwar mutane don ganin ko za su gano wani dalili.
Sun ce baya ga kansar hanji, kansa da ke shafar hanta, ƙoda, kansar mama, baki, su ma suna ƙaruwa.
Kansar hanji da na mama su ne suka fi kama matasa, inda mutum 11,500 ke kamuwa duk shekara, yayin da wadda ke kama ƙwayoyin jiki kuma ta kasance ba kasafai ake samunta ba.
An ga ƙaruwar kansar hanji da ta bakin mahaifa tsakanin matasa kaɗai, yayin da sauran tara kuma ke karuwa cikin manya.
Binciken, wanda cibiyar nazarin kansa a kwalejin Imperial da ke Landan ya yi, ya kuma duba ɗabi'u waɗanda a baya ke janyo ƙaruwar barazanar kamuwa da kansa.
Amma binciken ya nuna cewa ƙaruwar shan taba, shan giya, yana motsa jiki, cin jan nama mai yawa da kuma abincin gwan-gwani, da kuma raguwar cin abinci mai dusa na ƙaruwa ko kuma suna yanda suke.
Duka waɗannan ɗabi'u na taimaka wa wajen janyo cutar kansa, sai dai ba su yi cikakken bayani kan abin da ya sa kansa ke ƙaruwa ba.
Rahoton ya ce alkaluman da kaɗai suka nuna abin da ke jawo ƙaruwar kansa shi ne ƙiba mai yaw, wadda ke ƙaruwa tun shekarun 1990.
Ana tsammanin cewa yawan kitse yana shafar wasu sinadarai, kamar insulin, wanda zai iya ƙara haɗarin kamuwa da kansa.
Sai dai, shi ma wannan bayani ba cikakke bane.
Alal misali, masu bincike sun kiyasta cewa a cikin mutum 100 da suka kamu da kansar hanji, zai iya yiwuwa 20 sun kamu da shi ne sakamakon ƙiba, yayin da saura 80 kuma ba a san me ya janyo nasu ba.
Masu bincike sun ce yana da muhimmanci a kare kai daga kamuwa da duk wani na'ui na cutar kansa. Sun kiyasta cewaza a kare kashi 40 na masu kamuwa da kansa a duniya ta hanyar salon rayuwa mai lafiya, kamar daina shan taba.
Sun kuma ce duk da cewa ana samun ƙaruwar matasa da ke kamuwa da kansa, yana da muhimmanci a tuna cewa alkaluman ba su da yawa idan aka kwatanta da tsoffi masu ɗauke da kansa.
Har ila yau, masu binciken sun ce ana samun mutum ɗaya cikin matasa 1,000 (masu shekara daga 20, 30 zuwa 40) da ke kamuwa da kansa a duk shekara, idan aka kwatanta da mutum ɗaya cikin tsofaffi 100 (masu shekara 50, 60 zuwa 70) da ke kamuwa da cutar.