Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona na daf da kammala ɗaukar Silva, Juventus na zawarcin Reijnders
Barcelona ta kusa kammala cinikin ɗaukar ɗan wasan Manchester City Bernardo Silva, mai shekara 31, bayan da ɗan wasan na Portugal ya bayyana cewa zai bar Ingila a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Barca Universal)
Juventus ce ke kan gaba a jerin ƙungiyoyin Italiya da dama da ke zawarcin ɗan wasan tsakiya na Netherlands da Manchester City Tijjani Reijnders, mai shekara 27, wanda ya bar AC Milan zuwa Manchester kan farashin fam miliyan 46.3 a bara. (Football Insider)
Kocin Newcastle United Eddie Howe yana son Will Osula, mai shekara 22, ya ci gaba da zama a St James' Park, duk da ana sha'awar ɗan wasan ɗan ƙasar Denmark wanda aka ƙiyasta farashinsa kan fam miliyan 30, kuma kwantiraginsa zai ƙare har a watan Yunin 2029. (Shields Gazette)
Crystal Palace na kallon Andoni Iraola a matsayin wanda ke kan gaba wajen zama kocinta na gaba bayan ɗan ƙasar Sifaniyan ya bayyana cewa zai bar Bournemouth a ƙarshen kakar wasa ta bana - amma ita ma Chelsea ta nuna sha'awar ɗaukar kocin mai shekara 43. (Football Insider)
Real Madrid za ta yi ƙoƙarin riƙe ɗan wasan gaban Brazil, Endrick, mai shekara 19, a bazara, duk da sha'awar da Arsenal da Chelsea suka nuna kan ɗan wasan. (TeamTalk)
Kocin Coventry City Frank Lampard yana son tsohon ɗan wasan Ingila Ross Barkley ya zama ɗan wasa na farko da kulob ɗin zai ɗauka a bazara, inda kwantiragin ɗan wasan mai shekara 32 zai ƙare a Aston Villa a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Alan Nixon)
Real Sociedad na fatan dakatar da tafiyar Alex Remiro, mai shekara 31, zuwa Barcelona, ta hanyar bai wa golan ɗan ƙasar sifaniya sabon kwantiragi. (Football Espana)