Mece ce ranar ma'aikata ta duniya kuma yaushe ta samo asali?

    • Marubuci, Melissa Hogenboom
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journaliste spécialisée dans la santé et les sciences à la BBC
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ɗaya ga watan Mayu, rana ce da aka ware a duk shekara, a matsayin ranar ma'aikata ta duniya kuma ranar hutu ce. A Amurka, ana ɗaukar ranar a matsayin "Ranar Kwadago''.

An ƙirƙiro ranar ce domin yin waiwaye game da irin nasarorin da ma'aikata suka samu, da kuma matsaloli ko ƙalubalan da suke fuskanta a ƙasashe daban-daban.

Babu wata ƙasa da ta fara aiwatar da wannan rana. Sai dai ranar ta samo asali ne daga wata zanga-zanga da ma'aikata suka yi wata kasuwa a birnin Chicago a 1886.

Ma'aikata da dama sun shiga yajin aiki ranar 1 ga watan Mayun, 1886, inda suka yi zanga-zangar adawa da yawan sa'o'in aiki na awanni takwas a rana.

Kwanaki huɗu bayan haka, wasu da dama sun nuna goyon bayan zanga-zangar da ma'aikatan suka yi a kasuwar a Chicago.

Sai dai, ƴansanda sun yi harbi tare da kashe ma'aikata lokacin da zanga-zangar ta riƙide zuwa tarzoma.

Bayan faruwar lamarin, daga 1889 zuwa 1890, ma'aikata sun gudanar da zanga-zanga a ƙasashe da dama a faɗin duniya.

A ranar 1 ga watan Mayun 1890, ma'aikata kusan 3,000 sun halarci wata zanga-zanga da aka gudanar a dandalin Hyde da ke Ingila. Sun buƙaci a rage lokutan aiki daga sa'a 12 zuwa sa'a takwas a rana.

Haka kuma, an yi irin zanga-zangar a ƙasashen Turai da dama.

Daga baya, an cimma matsaya inda mutane suka yi murnar May Day a matsayin ranar ma'aikata tare da tuna wa da mutanen da aka kashe yayin maci a Chicago.

Daga nan ne ƙimar ranar ma'aikata ya sauya a faɗin duniya. Ba sabon abu bane yin zanga-zangar lumana don murnar ranar a ƙasashe da dama.

Daga shekara ta 1900 zuwa 1920, ma'aikata sun gudanar da zanga-zangar ranar Mayu karkashin karkashin inuwar jam'iyyun gurguzu don yaƙi da tatsar da ƙasashe ke yi musu da kuma 'yan kasuwa masu arziki a Turai.

An yi zanga-zangar adawa da yaƙi a ranar Mayu a lokacin Ƴaƙin Duniya na daya.

Bayan gomman shekaru, an yi bikin 1 ga Mayu a matsayin ranar kin ƴan Nazi. An yi bikin ranar a matsayin ranar ma'aikata ta ƙasa lokacin mulkin Hitler.

Mussolini a Italiya da Janar Franco a Sifaniya sun kakaba takunkumai da yawa a ranar Mayu.

Bayan Yaƙin Duniya II, ƙasashen Turai suka fara murnar bikin ranar ma'aikata a matsayin ranar hutu.

Daga baya, ƙasashe da dama a faɗin duniya sun bi sahu. An fara gudanar da shirye-shiryen walwalar ma'aikata a ƙasashe da dama a wannan rana.

Baya ga ɓullo da shirye-shiryen walwalar ma'aikata, ranar 1 ga watan Mayu, ya zama wani dandali na yin zanga-zanga.

A wannan rana ne aka fara gudanar da zanga-zangar kin ƴan jari-hujja a ƙasashe daban-daban. Wasu ƙungiyoyin ƙwadago da yawa su ma sun bayyana a wannan rana ta Mayu.

Ana murnar ranar Mayu a matsayin ranar hutu a wasu biranen Indiya. Ƙungiyoyin ƙwadago na gudanar da maci da kuma zanga-zangar lumana a ranar, da kuma taya murna ga hazikan ma'aikata.

A tsawon lokaci, buƙatun ƙungiyoyin ƙwadago shi ne ganin an inganta yanayin aiki da kuma albashin ma'aikata.