Yadda za a fara jigilar maniyatta Hajji a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya, ranar Lahadin nan ne ake sa ran jirgin farko na maniyyata aikin Hajjin bana (2026) na ƙasar zai tashi zuwa Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin.

Hukumar alhazan ƙasar NAHCON, ta ce an kammala dukkan shirye-shirye da suka kamata don gudanar da jigilar maniyyatan cikin nasara.

Hukumar ta ja hankalin maniyyatan ƙasar kan abubuwan da ya kamata su kiyaye, domin kauce wa matsala a ƙasar ta Saudiyya.

Fatima Sanda Usara, mataimakiyar darakta ce a sashen yada labaran hukumar, ta ce kawo yanzu hukumar na ci gaba da raba katin shaidar aikin Hajji ga maniyyatan, musamman a Abuja, da Legas.

"Jirgin farko zai tashi ne daga Abuja babban birnin Najeriya, ɗauke da alhazan jihohin Kogi da na Nasarawa, muna sa ran mahajjata dubu hamsin daga ɓangaren hukumomi sai na jirgin yawo su dubu kusan tara, in ji Fatima Sanda Usara,

Har ila yau ta ce abubuwan da suka rage wa maniyyatan su kammala kafin tafiya ƙasar mai tsarki, baya ga kammala karbar alluran rigakafinsu, sai kuma jaddada muhimamcin ƙarɓar katin shaidar aikin Hajji, wanda ta ce yana ɗaya daga cikin abu da a baya suke samun matsaloli a kai.

"Muna jaddada wa maniyyata da su kula sosai da guzurinsu, saboda yadda ake yi wa mahajjatan kudadensu a ce su kawo farar takardarsu, sai a chanja musu a ba su dala dai-dai, wanda hakan ya sa muka wayar da kawunan mahajjatan da su kauce wa hakan" a cewar mataimakiyar daraktar.

A baya dai ana yawan samun jinkiri a aikin jirgilar alhazan Najeriyar a duk shekara, wanda hakan kan sa wasu alhazan su gaza samun damar sauke faralin, sai dai Fatima, ta ce tuni suka ɗauki mataki kan lamarin.

"A baya matsalar dama ta katin nan ne na Yellow Card ( katin shaidar yin allurar cutar shawara ) da ake samun jinkirin fitowarsa, har zuwa lokacin da za a rufe tafiya aikin hajjin, mun yi magana da hukumomin alhazan jihohi, sun kuma tabbatar mana da cewar dukkan alhazan jihohin an samar musu" in ji jami'ar.

Ta ce kan batun fargabar da ake yi ta cewar ko matsatar da ake fama da ita a yaƙin Iran da ya haifar da tsadar man jirgi, ta ce shugaban hukumar ya dauki mataki a kai, wanda ya sanar da fadar shugaban ƙasa kuma ana tattaunawa wajen ganin an ɗauki matakan da suka kamata don ganin hakan bai shafi jigilar alhazan na Najeriya zuwa Saudiyya don sauke farali ba.

A kowace shekara, miliyoyin Musulmi ne kan je ƙasar ta Saudiyya domin aikin Hajji wanda yake wajibi ne ga wanda ya samu dama sau ɗaya a rayuwa kuma yana gudana a watan ƙarshe na jerin watannin Musulunci.

Rukunin ibada ne da ya haɗa da yin ɗawafi sau bakwai a Ka'aba, wadda ita ce mafi tsarkin wurin ibada a Musulunci.

Ga yawancin mutane, wannan tafiya tana cike da imani da farin ciki inda za a ji sautin kiran sallah a Masallacin Harami da na Annabi Muahmamad SAW da ke Madina, tare da sautin takun ƙafafu da damar yin adduo'i kuma addu'o'in dabban-daban na neman gafara ko duniya.