Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yara fiye da miliyan 18 ba sa zuwa makaranta a Najeriya
Asusun kula da yara na Majalisar ɗinkin duniya watau UNICEF ya bayyana jihohin Jigawa da Kano da Katsina a matsayin jihohin da suka fi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
Asusun ya jaddada buƙatar, saka hannun jarin gaggawa a fannin ilimin yara ƙanana a matsayin abin da ke da matuƙar muhimmanci wajen juya akalar lamarin.
Kwamshinan ilimi na makarantun firamare da sakandire a Jihar Katsina, Yusuf Sulaiman Jibiya ya yi wa BBC ƙarin bayani kan dalilan da suka sa Katsina ta kasance cikin jihohi masu yawan yaran da ba sa zuwa makaranta:
''Akwai maganar tsaro, wanda saboda da harkokin tsaro yara da ya kamata a ce sun gama makaranta, ba su gama ba''
''Harkar tsaro ta sa waɗanda suke zaune da iyayensu sun bar wurin, makarantun da ke a nan, an rufesu'', in ji shi.
Kwamishinan ya kuma bayyana matsala ta tattalin arziki da ta ƙarancin makarantu a inda al'umma suke zaune a matsayin wasu daga cikin abubuwan da suka haifar da matsalar.
Unicef ta jaddada buƙatar, saka hannun jarin gaggawa a fannin ilimin yara ƙanana a matsayin abin da ke da matuƙar muhimmanci wajen juya akalar lamarin.
Ita ma gwamnatin jihar Katsina ta ce ta na ɗaukar matakan da suka da ce domin samun zaman lafiya.
Ta ce ƙananan hukumomi da a da ake samun matsalolin tsaro masu yawa kamar Jibiya da Batsari da Safana da Kurfi da Ɗanmusa da sauransu a yanzu an samu sauƙi
''Waɗannan wurare a da duk an rufe makarantansu amma yanzu cikin ikon Allah kusan kashi 70 cikin 100 na waɗannan wurare an samu tsaro kuma an buɗe akasarin makaruntu ko ana kan buɗewa '', in ji shi
Dokta Usman Aliyu Tilde tsohon kwamishinan ilimi a jihar Bauchi kuma mai sharhi kan al'amuran da suka shafi ilimi a ƙasashen Afrika ya yi tsokaci kan matsalar
''Yara maza ba su cika bari ba saboda girmansu amma ƴan mata su kan bari saboda girmansu, da zarar sun kai shekara 13 ko 12 ƙarfinsu ya na koma wa kan ayyuka irinsu talla da sauransu''
''A da aure ne amma yanzu ana amfani da su ta fanin tattalin arziki kuma har da mazan su ma, sai su koma neman kuɗi saboda ciyar da iyali''
Sai dai masanin ya nuna shakku kan yiwuwar kawar da matsalar.
''Wallahi wannan lamari za a ci gaba da samunsa, saboda akwai wasu dalilan, waɗanda ita kanta gwamnati ba bu abin da za ta iya yi akansu, kuma sai tattalin arziki ya inganta'' in ji shi.