Dr. East: Baturen da ya fara assasa jaridar Hausa a Najeriya

Asalin hoton, Farfesa Aliyah Adamu Ahmad
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Dr. Rupert Moultrie East baturen Ingila ne da ya je Najeriya a zamanin mulkin mallaka, inda ya yi aikace-aikace a yankunan arewacin Najeriya, musamman a ɓangaren ilimi da adabi.
Farfesa Aliyah Adamu Ahmad, wanda ta yi bincike tare da nazari kan tarihin baturen, ta ce Moultrie ba sunan mahaifinsa ba ne, inda ta ce sunan mahaifin mahaifiyarsa ne.
Ta ce Baturen Ingila ne wane ya je Najeriya yana matashin shi a lokacin da yake ɗan shekara 23, inda ta ƙara da cewa ya je Najeriya a matsayin ɗan mulkin mallaka amma a ɓangaren ilimi wato Education Department. "Tunda a arewacin Najeriya ya yi aiki, sai in ce an kasa yan arewacin Najeriya, ya fara aiki ne a yankin Adamawa."
Ta ce bai yi aikin koyarwa a can ba sosai, duk da cewa hukumar ilimin yankin ta buƙaci a samar da abin koyarwa da karatu na matakin farko.
"To aikin da ya yi ke nan, ya samar musu da abin karantawa a cikin harshen Fulfulde, musamman a ɓangaren ƙirƙirar labari, wanda yake tafiya da irin hikayoyi da tatsuniyoyi da ƙirƙirarren labari."
Farfesa Aliyah ta ce daga Adamawa ne ya koma koma yankin Benuei, inda a can ya yi aiki a ɓangaren ilimi, suma ya jagoranci rubuta labarai, amma a cewarta ya ƙara aikin duba makarantu da yadda hada-hadar koyarwa ke tafiya.
Aliyah ta ce daga Benuwei ya koma Katsina, daga can kuma ya koma yankin Zaria na jihar Kaduna.
Assasa jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo
Ferfesa Aliyab ta ce daga Katsina ne Dr. East ya koma yankin Zaria, inda a shekarar 1929 ya jagoranci assasa cibiyar fassara ta Translation Bereau a 1929. ''Daga 1929 duk da yake ba shi ke jagorantar hukumar a wannan lokacin ba, yana da wanda suke gaban shi, yana matsayin mataimaki. Har kuma ya zo ya zama shi ne jagora bayan aikin fassara littattafai daga harsuna zuwa Hausa domin a samar da abin karatu a cikin harshen Hausa.''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta ce daga fassara ne suka koma irin harkar jarida, wanda a cewarta ya samar da Gaskiya Ta Fi Kwabo a 1939.
''Daga nan dai har aka kafa kamfanin gaskiya. Ya ɗan samu tallafi daga asusun ilimi a arewacin Najeriya. Da asusun aka gina kamfanin Gaskiya Ta Fi Kwabo kuma ake wallafa jaridu kuma ake fassara wasu manufofi na gwamnati,'' in ji ta.
Ta ce a kamfanin ne kuma ake shirya tambayoyin jarabawa ga Turawa masu son su zo Arewacin Najeriya domin a cewarta sai bature iya Hausa, ya iya Fulatanci sannan an masa jarabawa ta 1 da 2 kafin ya samu aikin.
Ta ƙara da cewa da fassara littattafai da sauran su ne har hukumar ta jagoranci shirya gasar ƙirƙirarrun labarai a 1936, inda aka samar da littattafai irin su Ruwan Bagaja da sauran su. ''Rupert East shi ne wanda ya jagoranci duk waɗannan ayyuka."
Aliyah ta ce a zamaninsa ne ƴan Tibi suka samu jarida ta kansu, Hausawa suka samu jarida ta kansu ba ma ɗaya ba, suka samu So Dangi da Jaruma a Sokoto da Gaskiya Ta Fi Kwabo da Ƴar Gaskiya da sauran su, sannan Fulani suka samu jaridar Arɗo.
Jigon adabin arewacin Najeriya
Farfesa Aliyah ta bayyana cewa idan ana maganar adabin Hausa da ma raya adabi a arewacin Najeriya, Dr. East ya ba da gudumawar da har yau ba a samu wanda ya ba da fiye da ita ba.
"Domin ina da wani misali da zan ba ka. Kamar lokacin da yake Adamawa, sai ya samar da wani littafi, sunan shi The Stories of Old Adamawa, inda suka tara hikayoyinsu na baka. Sai ya ɗauki littafin da suka rubuta a harshen Fulfulde, amma ya gyara musu aka buga," in ji ta, sannan ta ƙara da cewa ya koya magana da harshen.
Ta ce bayan ya gyara musu sai ya fassara zuwa Ingilishi. "To sai ya ce to yanzu kun ga waɗannan, kuna iya kai waɗannan littattafan guda biyu a makarantunku. Na farko, ana iya karanta shi da Fulfulde. Na biyu kuma ana iya karanta shi a cikin Ingilishi."
Farfesa ta ƙara da cewa da ya koma Binuwei, haka ya yi wa ƴan Tibi, inda can ma ya jagoranci rubuta littafai.
"Abin da wasu ba su sani ba, wancan labarin na cikin Fulatanci da ya taimaka aka yi a Fulatancin da Hausa da kuma wannan na Tibi, su ne ya ɗauko ya fassara da Hausa, inda aka fara samar fa littatafan, "Littafin Hausawa da Makwabtansu" na 1 da na 2."
Ta ƙara da cewa littafin 'Jiki Magayi' shi kuma labarin da wani Akiga ya rubuta ne a kan mutanensa na Tibi da al'adunsu da tsafe-tsafensu da sauransu.
Ta ce littafin Sauna Jack labari ne na gaskiya, inda ta ce labarin wani yaro ne da ya kasance yana yi wa ƙananan ma'aika aiki musamman wankin takalmi a lokacin da Dr. East yake Benewei.
"Matar East ɗin - akwai matarsa Baturiya Jacklin, ita kuma sai ta ƙirƙira labari Sauna Jack, Sauna na Jacklin. Sai take bin labarin Sauna Jack a cikin hotuna da kuma irin duk halayya da hidindimun da shi Sauna ɗin yake yi."
"To ka ga gaskiya dai a zuwa yanzu, Turawa sun ba wa Hausa gudumawa amma dai ba kamar yadda Rupert East ya bayar ba," in ji ta.
Farfesa ta nanata cewa East jigo ne faɗa a ji a adabin Hausa da arewacin Najeriya, inda ta ƙara da cewa an samu waɗanda suka ci gaba da irin tarbiyyar da ya musu kamar su Imam da Tinau Mafara da Sardauna da Malam Ahmadu Ingawa da sauran su.
"To yanzu ma sai ka ga cewa babu jaridun larduna kamar a lokacin shi. A wancan lokacin kowane lardin yana ƙoƙari da fitar da jarida duk mako biyu ko duka wata-wata, suna labarto abin da larduna suke ciki na gefen ilimi, na gefen lafiya, na gefen kasuwanci, na gefen shari'o'i da ake yi, ga sunan dai abubuwa da yawa."
Ta ƙara da cewa a lokacin shi aka samu ƴan jarida, su ma na larduna masu ɗauko rahotannin abubuwan da suke yi a lardunan su, "kowane lardi yana fitar da rahoto a tura ma Gaskiya Ta Fi Kwabo."
A cewartsa, a lokacin ne aka fara tura wakili zuwa kotu-kotu, wanda duk lokacin da za a yi zaman yanke hukunci to akwai wakilin da yake zuwa ya zauna ya ga yadda ake yi ya rubuta ya kai wa jarida a wallafa.










