Ba mu shirya wata tattaunawa da Amurka a Doha ba - Iran

Asalin hoton, Tasnim news agency
Iran ta musanta iƙirarin Trump cewa za a fara sabbin tattaunawa da Amurka a Doha, tana mai cewa ba ta shirya wata ganawa ko tattaunawa da Amurka ba a wannan lokaci ba.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce wakilan ƙasar da ke tafiya Doha ba don tattaunawa ba ne, sai dai domin bibiyar batun kuɗaɗen ƙasar da aka ƙwace a ƙasashen waje.
Wannan matsaya na Tehran ya zo ne duk da cewa Trump ya bayyana cewa za a gudanar da ganawa tsakanin wakilan ƙasashen biyu a babban birnin Qatar.
Sai dai jami’an Iran sun musanta wannan batu, suna jaddada cewa babu wani shiri na ganawa ko tattaunawa da suka shirya yi da Amurka a kwanaki masu zuwa.
A wani ɓangare, Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kimanin dala biliyan 6 daga cikin biliyan 12 na kuɗaɗen Iran da aka ƙwace za su sake dawowa da su hannun gwamnati nan ba da jimawa ba.
Ya ce ana ci gaba da bin matakan da suka dace domin ganin an saki kuɗaɗen, wanda ake ganin zai taimaka wajen karfafa tattalin arzikin ƙasar.
Haka kuma, Iran ta yi martani ga bayanan da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi, inda ta jaddada cewa ita kaɗai ce ke da ikon gudanar harkokin mashigin Hormuz.



















