Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan ƙwallon da za su nemi ƙungiya bayan gasar kofin duniya 2026
Gasar cin kofin duniya ta 2026 na kara zama abin ban sha'awa
Kawo yanzu gasar tana matakin ziri ɗaya ƙwale, an kusan kammala zagayen tawaga 16, an kuma shirin faɗawa wasannin ƴan 16 zuwa sauran matakan da za ta kai a buga karawar karshe ranar 19 ga watan Yuli.
Sai dai kuma ga wasu rukunin ƴan wasa suna da damar taka rawar gani da yin fice a wasannin da suke gabansu.
Tun daga ranar 2 ga watan Yulin 2026, ƴan wasa 14 da ke buga gasar cin kofin duniya ta bana, ba su da wata ƙungiyar da suke buga wa tamaula da zarar an karkare wasannin.
Daga cikinsu da akwai fitattu da suka yi suna a duniya suka tara arziki, kamar su Casemiro da James Rodriguez da kuma Mo Salah, waɗanda ba za su yi fargabar yaya tsadar rayuwa take a irin wannan matakin.
Sai dai duk da haka suna da rawar takawa, domin su samu ƙungiyoyin da za su yi zawarcinsu - kuma suna da damar ci gaba da gudanar da sana'ar tamaula, idan har rauni bai kawo musu cikas ba.
BBC ta yi duba kan makomar waɗan nan ƴan kwallon da ba su da wata yarjejeniya da ƙungiya, kuma suna fatan yin abin kirki a gasar kofin duniya.
John Stones, 32, England (Ƙungiyar da ya bari ta karshe: Manchester City)
Ya yanzu ya bar Manchester City bayan ya shafe shekara goma a kulob ɗin, inda ya lashe manyan kofuna 15.
Duk da matsalolin raunuka da ya fuskanta a baya-bayan nan, sabon kocin tawagar ƙasar Ingila Thomas Tuchel ya je da shi gasar cin kofin duniya.
Ana kuma alaƙanta John Stones da yiwuwar komawa tsohuwar ƙungiyarsa ta Everton, yayin da manyan ƙungiyoyin Italiya har da AC Milan ke nuna sha'awar ɗaukar shi.
Stones ɗaya ne daga cikin fitattun ƴan wasa masu tsaron bayan Manchester City a shekarun baya, inda ya taka muhimmiyar rawa a nasarorin da ta samu a ƙarƙashin jagorancin Pep Guardiola.
Casemiro, 34, Brazil (Ƙungiyar da ya bari ta karshe: Manchester United)
Ba a tsawata yarjejeniyar ɗan wasan ba a Manchester United saboda albashin da yake ɗauka kuɗin ya yi yawa, duk da cewa ya yi kaka mai kyau sosai a wasansa na ƙarshe a Old Trafford a kakar da aka kammala.
A gasar Kofin Duniya, rawar da Casemiro yake takawa ba yabo ko fallasa, inda wani lokaci ya yi fice, wani lokaci kuma bai kai yadda ake tsammani ba. Duk da haka, ya zura ƙwallo mai mahimmaci a raga da ta bai wa Brazil damar farke wadda Japan ta fara zura mata a wasan zagayen ƴan 32.
Ana sa ran ɗan wasan mai shekaru 34 zai koma ƙungiyar Inter Miami mai buga gasar Major League Soccer (MLS) da zarar gasar Kofin Duniya ta ƙare.
David Alaba, 33, Austria (Ƙungiyar da ya bari ta karshe: Real Madrid)
David Alaba ya bar Real Madrid bayan kammala kakar da ta wuce, bayan ya shafe shekara biyar a ƙungiyar.
Tsohon ɗan kwallon Bayern Munich ya yi nasarori masu yawa a ƙungiyar, inda ya lashe kofunan lig guda 12 da kuma na Champions League har sau huɗu.
Haka kuma, an zaɓe shi a matsayin Gwarzon Ɗan Ƙwallon Ƙafar Austria na Shekara har sau 10, abin da ke nuna irin tasirinsa a ƙwallon ƙafa tsawon shekaru.
Duk da jita-jitar da ke alaƙanta shi da ƙungiyoyi da dama bayan karewar kwantiraginsa da Real Madrid, har zuwa yanzu Alaba bai sanya hannu a wata ƙungiya ba.
Fabinho, 32, Brazil (Ƙungiyar da ya bari ta karshe: Al Ittihad)
Da yake magana da jaridar Marca a watan Janairu, Fabinho ya bayyana cewa ba ya gaggawar yanke hukunci kan makomarsa, yana mai cewa yana son komawa Turai da ci gaba da taka leda a wani lokaci nan gaba.
A gasar Kofin Duniya ta bana, kocin Brazil Carlo Ancelotti ya fi amfani da shi a matsayin ɗan wasan da yake yin canji. Duk da haka, Fabinho na ci gaba da kasancewa muhimmi a tawagar ta Brzil, saboda ƙwarewa da gogewarsa.
Yanzu da zarar ya kammala buga gasar ƙwallon ƙafar Saudiyya, ana sa ran za a ci gaba da hasashen inda zai koma da taka leda a kakar wasa mai zuwa, musamman ganin cewa ya nuna sha'awar komawa Turai.
Mohamed Salah, 33, Egypt Ƙungiyar da ya bari ta karshe: Liverpool)
Salah bai samu natsuwa da kwanciyar hankali ba a Anfield daga watannin karshe a kakar da aka kammala ba, saboda dangan taka da ta yi tsami tsakaninsa da koci, Arne Slot. Yanzu shi da kociyan kowa ya bar Liverpool. Ana kuma ta hasashen cewar Salah zai koma taka leda a babbar gasar tamaula ta Saudiyya da zarar an kammala gasar cin kofin duniya ta 2026, amma yanzu hankalinsa yana kan yadda zai kai Masar zagayen ƴan 16 a karon farko a gasar kofin duniya da za su kara da Australia ranar Juma'a.
James Rodriguez, 34, Colombia (Ƙungiyar da ya bari ta karshe: Minnesota United)
Ƙungiyar Minnesota mai buga MLS tana da zaɓin tsawaita masa ƙwantiragin wata shida, domin ya ci gaba da wasa a gasar babbar tamaula ta Amurka. Sai dai har yanzu ba labari kuma da ƙyar ne idan za ta yi hakan, domin wasa shida ya buga mata a farkon zangon kakar bana daga ciki biyu aka fara wasa da shi, sauran ya shiga canji. Kenan Rodriguez zai nemi ƙungiyar da zai koma buga wa tamaula ta biyar a kasa da shekara uku.
Luka Modric, 40, Croatia (Ƙungiyar da ya bari ta karshe: Real Madrid)
AC Milan tana da zaɓin tsawaita yarjejeniyar Modric zuwa kaka ɗaya, amma ba ta fayyace ko hakan zai yiwuba, ko kuma tsohon ɗan wasan zai kara yin gaba ba, ko kuma zai sanar da yin ritaya.
Modric bai taka rawar gani ba a wasa da Ingila a cikin rukuni daga baya ya kara sa kwazo a nasarar da Croatia ta yi a kan Panama da kuma Ghana daga nan kuma Portugal ta yi waje da su a zagaye na biyu.
Vozinha, 40, Cape Verde (Ƙungiyar da ya bari ta karshe: Chaves)
Mai tsaron ragar Cape Verde ya yi suna a gasar nan ta ci kofin duniya, saboda hana Sifaniya ta zura masa ƙwallaye a raga a wasan farko a cikin rukuni da suka tashi ba ci wato 0-0. Tun daga lokacin ya ci gaba da sa kwazo har sai da ya kai kasar zagayen ƴan 32, inda za su kece raini da Argentina ranar Juma'a.
Mai shekara 40 ya sanar cewar yarjejeniyarsa ta kare da ƙungiyar da ke buga gasa mai daraja ta biyu a Portugal, Chaves, amma ya sanar da cewar yana sun ya ci gaba da taka leda.
Ƴan wasan da ke buga gasar kofi duniya da kwantiraginsu ya kare a ƙungiyoyinsu
- David Alaba, 33, Austria (Last club: Real Madrid)
- Nabil Bentaleb, 31, Algeria (Last club: Lille)
- Casemiro, 34, Brazil (Last club: Manchester United)
- Fabinho, 32, Brazil (Last club: Al Ittihad)
- Gideon Mensah, 27, Ghana (Last club: Auxerre)
- Thomas Meunier, 34, Belgium (Last club: Lille)
- Luka Modric, 40, Croatia (Last club: AC Milan)
- Abdul Mumin, 27, Ghana (Last club: Rayo Vallecano)
- Orjan Nyland, 35, Norway (Last club: Sevilla)
- Thomas Partey, 32, Ghana (Last club: Villarreal)
- James Rodriguez, 34, Colombia (Last club: Minnesota United)
- Mohamed Salah, 33, Egypt (Last club: Liverpool)
- Xaver Schlager, 28, Austria (Last club: RB Leipzig)
- John Stones, 32, England (Last club: Manchester City)
- Vozinha, 40, Cape Verde (Last club: Chaves)