Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Adadin waɗanda suka mutu a harin da Rasha ta kai kan Ukraine ya kai 30

    Sojojin Rasha sun kai wani mummunan harin makami mai linzami kan Kyiv cikin daren Alhamis, inda suka kashe aƙalla mutum 30, abin da magajin garin ya bayyana a matsayin "hari mafi muni" da aka kai babban birnin Ukraine.

    Mutum 91 sun ji rauni, in ji shugaban gwamnatin sojin Kyiv, Timur Tkachenko.

    Magajin gari Vitaly Klitschko ya ce wata tashar motocin asibiti na daga cikin wuraren da abin ya shafa.

    Duk da cewa hare-haren da aka kai a baya sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, wannan harin shi ne wanda ke da mafi yawan bama-bamai da aka zazzaga a babban birnin ƙasar.

    An kwashe mutane daga unguwanni da dama yayin da aka kai hare-hare a birnin sa'o'i bayan shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya gargaɗin cewa Rasha na shirin kai hari.

    Moscow ta ce dakarunta sun kai hari kan abin da ta kira masana'antar soji a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da ake kai wa farar hula a Rasha.

    Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya shaidawa manema labarai jiya Alhamis cewa, Rasha za ta ci gaba da ƙara matsawa gwamnatin Kyiv lamba har sai ta cimma muradunta.

  2. Iran ta fara makokin Ayatollah yayin da ake shirye-shryen jana'izarsa

    Iran ta fara gudanar da zaman makoki na gama-gari yayin da ake shirin fara jana'izar tsohon Jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, bayan fiye da watanni huɗu da aka kashe shi a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai.

    Za a ajiye gawar tsohon Ayatollah din a babban ɗakin taro na 'Grand Mosalla' da ke birnin Tehran tun daga ranar Juma'a, kafin a kai shi garinsu na Mashhad domin binne shi a ranar Alhamis mai zuwa.

    Jami'ai sun ce jana'izar na iya samun halarcin masu makoki miliyan 20 daga sassan Iran, a cewar AFP.

    Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Iran da Amurka ke tsagaita wuta a tsakaninsu bayan sanya hannu kan yarjejeniyar farko ta dakatar da faɗan da suke yi a watan Yuni.

    Za a ajiye gawar Khamenei a Grand Mosalla na tsawon kwanaki uku, tare da gawarwakin sauran yan daginsa da aka kashe a harin da Amurka da Isra'ila suka kai a watan Fabrairu.

    Za a yi wani taron jana'iza a hukumance a birnin Tehran ranar Asabar.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa hukumomi sun umarci ofisoshin gwamnati da na masu zaman kansu da ke Tehran da su rufe daga Asabar zuwa Litinin, yayin da aka kafa dokar takaita zirga-zirga a sassan tsakiyar birnin.

  3. Harin bam ya kashe mutum shida a Syria

    Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Syria sun ce wani bam ya tashi a wani gidan shan shayi mai cike da jama'a a tsakiyar birnin Damascus, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum shida tare da jikkata wasu 22.

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce an dasa wani abu mai fashewa a cikin gidan shayin, wanda ke da nisan mita 100 kacal (ƙafa 330) daga ginin ma'aikatar Shari'a, wani babban ginin gwamnati a gundumar Hejaz da ke babban birnin ƙasar.

    Babu wata ƙungiya da ta yi ɗauki alhakin kai harin nan take. Wannan shi ne harin bam mafi muni da aka kai a birnin Damascus tun bayan harin ƙunar baƙin wake da aka kai a wani coci a watan Yunin 2025 wanda ya kashe mutane 25.

    Wata kungiyar masu iƙirarin jihadi mai suna Saraya Ansar al-Sunnah, ta ce ita ce ta kai harin, amma hukumomi sun dora alhakin harin kan ƙungiyar IS.

    Mohammed al-Dahabi, mamallakin wani shagon sayar da gilashi da ke kusa da gidan shayin, ya ce harin bam ɗin na ranar Alhamis ya yi kama da wanɗnada aka riƙa gani a Damascus a lokacin yaƙin basasar Syria.

    A yayin ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru, Gwamnan Damascus, Maher Marwan Idlibi, ya ce za a hukunta waɗanda ke da hannu a kitsa harin.

  4. Assalamu Alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'a daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.