Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Har an kammala shirin binne ni': Matar da ta yi shekara 30 da cutar HIV
- Marubuci, Beldeen Waliaula
- Aiko rahoto daga, Nairobi
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Margaret Lavonga, ƴar shekara 55, mai ƴaƴa biyu, ta kwashe sama da shekara 30 tana rayuwa da cutar HIV mai karya garkuwar jikin ɗan'adam.
"Na gano cewa ina ɗauke da ƙwayar cutar a lokacin da nake da juna-biyu bayan da na yi gwaji kuma na gano cewa sakamakon ya nuna akwai ƙwayar cutar."
A wancan lokacin, jinya ko kuma gano cewa ka na ɗauke da cutar HIV an ɗauke shi a matsayin wani abu mara kyau saboda ƙyama da ke tattare da cutar.
"Lokaci ne da ake za ka ga ko ina an manna hotunan mutane da suka ƙanjame, ga ƙaton kai da ƙasusuwa ɓaro-ɓaro a jikinsu. Da aka ce mun ina ɗauke da ƙwayar cutar, na yi tunanin kawai rayuta ta zo ƙarshe."
A lokacin da aka gano Margret tana ɗauke da cutar HIV, magungunan cutar ba su isa ƙasar Kenya ba, wanda hakan ya tilasta mata ɓoye halin da take ciki har sai da ta haihu a shekarar 1999, sai dai jaririn nata ya rasu bayan wata biyu da haihuwa.
"Haihuwa a asibiti ta kasance mai wahala, kowa na tsoron kusanta ta saboda tsoron kamuwa da cutar HIV."
Bayan wannan lokacin, lafiyar Margaret ta ci gaba da taɓarɓarewa. Ta yi mummunar jinya ta tsawon shekara biyu inda ta ke kwance ba ta iya zuwa ko ina, ƴar'uwarta ce ta riƙa kula da ita, wadda ita ce ta san halin da take ciki.
A lokuta da dama an kwantar da Margaret a asibiti, wanda hakan ya sanya ta zama cikin mutane na farko-farko da suka ci gajiyar maganin masu fama da cutar HIV a ƙasarta Kenya.
An ba da rahoton ɓullar kwayar cutar HIV karon farko a Kenya ne a shekarar 1984, kuma ga mutane da yawa da aka gano a lokacin, sun yi tunanin cewa ba za su daɗe a raye ba.
Mutane da yawa sun fuskanci ƙyama, da wariya daga iyali, da kuma tsangwama daga jama'a. Ɓarkewar cutar ta kuma sa an samu yara da dama da suka zama marayu.
Amma akwai mutanen da aka gano suna ɗauke da cutar tun a shekarar 1999, waɗanda har yanzu suna raye, inda suka kwashe shekaru 30 suna rayuwa da kwayar cutar har ma sun kama hanyar tsufa.
A nata ɓangaren, samun damar yin amfani da magungunan rage raɗaɗin cutar HIV (ARVs) ba abu ne mai sauƙi ba.
"Da farko, an rubuta mana magunguna daban-daban guda uku, suna da ƙarfin gaske kuma suna haifar da illoli da dama, bayan shan su, wani lokaci mukan yi wasu mafarke-mafarke masu ban tsoro ko kuma mu fara wasu gane-gane na abubuwan da babu su a zahiri, mukan fita daga hayyacinmu har ya kai ga ba mu iya tuƙin mota."
Ta ƙara da cewa: "Zan iya cewa mutanen da suka kamu da cutar a baya-bayan nan sun yi sa'a, saboda magungunan da ake da su yanzu ba su haifar da mummunar illa."
Margaret ta tuna cewa kafin ta fara jinya, ta yi tunanin cewa rayuwarta ta zo ƙarshe. Ta rame sosai, inda nauyinta ya ragu da kilo 34, lokacin da iyayenta suka fahimci halin da take ciki sai suka fara shirya sami labarin halin da take ciki, sai suka fara shirya jana'izarta.
Akwai lokacin da ta daina shan maganinta, ta ce ta warke kuma ta dogara da addu'a. Amma nan da nan lafiyarta ta taɓarɓare, lokacin da ta ga haka sai ta hanzari ta koma shan magungunan da aka ba ta, waɗanda ta ci gaba da amfani da su har yau.
HIV na kai hari ne kan garkuwa jiki. Wannan yana sa masu ɗauke da cutar su fi saurin kamuwa da cututtuka irin su tarin fuka, da sauran su.
To sai dai rayuwa ɗauke da cutar HIV yayin da tsufa ke kawo jiki abu ne mai cike da ƙalubale.
"Ko da yake yanzu ina da ƙarfin halin yin magana game da wannan ciwon, wani lokacin nakan kulle kaina a cikin ɗaki na yi kuka. Wani lokaci nakan yi tunanin cewa in da ban kamu da wannan cutar ba, da na samu ci gaba a rayuwa fiye da yadda nake a yanzu."
Ƙalubalen da take fuskanta a halin yanzu shi ne na cututtukan da suka shafi tsufa, wanɗanda suke ta'azzara kasancewar tana ɗauke da HIV.
"A halin yanzu ina fama da ciwon ƙashi, da hawan jini, da matsalolin ido. Cututtukan da suka shafi shekaru abu ne da aka saba gani, amma a wajenmu, sun fi tsanani."
Ta bayyana shan magungunanta a kowace rana, a matsayin abu mara sauƙi. "Wani lokaci nakan ji kamar na daina shan maganin, amma ina da mutanen da suke ƙarfafa min gwiwa kowace rana don in ci gaba da wannan yaƙin."
Duk da cewa ana ƙara inganta magungunan cutar HIV, matasa a wannan zamani suna fuskantar ƙalubale saboda rashin jure wa shan maganin a kaullum.
"Ina son in ƙarfafa wa al'ummar wannan zamanin gwiwa, ko sun kamu da cutar HIV, ko kuma an haife su da ƙwayar cutar: zama da cutar HIV ba abu ne mai sauƙi ba, amma ba mai saurin kisa ba ne. Cututtukan da ke da alaƙa da cutar HIV ne ke kisa. Don haka idan har ka kamu da cutar, ka sha magungunan ka, za ka daɗe ka na gudanar da rayuwarka."
Akasarin mutanen da ke rayuwa da cutar HIV a Kenya sun haura shekara 50 da haihuwa.
A cikin mutane sama da miliyan ɗaya da ke ɗauke da cutar a Kenya 27% daga cikin su sun haura shekara 50.
Burin Margaret shi ne ta rayu har sai ta kai shekara 120 duk da cewa ta na ɗauke da cutar HIV.
"Ga waɗanda suka girme ni, ina kira gare su da kada su saduda, kada su daina jinyar da suke yi, ya zama cewa tsufa ne ya yi ajalinsu ba rashin shan magani ba wanda zai haifar musu da kamuwa da cututtuka masu tsanani," in ji Margaret.