Kociyoyin da suka ajiye aiki da waɗanda aka kora a gasar kofin duniya 2026

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 8

A tarihin ƙwallon ƙafa, babu wata gasa da ta fi Kofin Duniya saurin korar koci ko kuma a ajiye aiki kamar yadda ake gani a yanzu.

Babbar gasar tamaula ta duniya da ake gudanarwa duk shekara huɗu kan ja hankalin dubban mutane a faɗin duniya, bayan buri da fata da ake sawa ga duk wanda yake aikin jagorantar duk wata tawaga da ke buga gasar.

Kuma kalubale kan fara tun daga wasannin neman shiga gasar, in banda masu masaukin baƙi da ba sa shiga zagayen neman tikitin shiga wasannin.

Tun daga lokacin ne masu horar da tamaula kan shiga matsi da fuskantar kalubale, wajen shirye-shiryen neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya.

Koda ka yi ƙoƙari ka kai tawaga babbar gasar tamaula ta duniya, nan ma ana sa ran ka taka rawar gani a idon duniya a ɗan kwanakin wasannin, idan ba haka ba makomarka za ta shiga rashin tabbas.

Saboda haka masu horas da tawagogi na fuskantar matsin lamba tun kafin fara gasa da kuma bayan kammalata, ba lallai sai gasar kofin duniya ba, amma sun fi cin karo da babban kalubale a kowane lokacin da ake buga gasar cin kofin duniya.

Kofin Duniya na FIFA 2026 ya sake nuna cewa nasara da rashin nasara na iya yanke makaomar mai horarwa. Domin cikin ƙasa da mako uku bayan fara gasar bana, koci bakwai sun riga sun rasa aikinsu ko kuma sun yi murabus daga tawaga 48 da aka fara wasannin bana da su. Wasu an kore su da gaggawa, wasu kuma sun zaɓi ajiye aiki bayan sun kasa cimma burin da aka ɗora musu.

Yawancin waɗannan kociyoyin ba sababbi ba ne a aikin. Wasu sun shafe shekaru suna gina tawagarsu, suna tsara hanyar da za ta kai ƙasarsu ga nasara. Sai dai kamar yadda tarihi ya nuna, Kofin Duniya ya fi karkata kan sakamakon da tawaga ta samu ba wai ƙokarin murza leda ba a wasanni.

Domin samun kyakkyawan sakamako ne zai kai ga lashe Kofin Duniya, wanda kowace ƙasa ke alfahari da shi tare da yin fice a idon duniya.

Sabri Lamouchi: Wanda ya fara rasa aiki a gasar kofin duniya ta 2026

Kocin Tunisia, Sabri Lamouchi shi ne mutum na farko da ya rasa aikinsa a wannan gasar ta Kofin Duniya. An naɗa shi aikin a ranar 14 ga Janairu, 2026 bayan da Hukumar Kwallon Tunisia ta raba gari da Sami Trabelsi.

An ba shi kwantiragin shekara biyu da rabi, tare da burin ya kai Tunisia wani matsayi mai ƙyau a gasar duniya.

Sai dai kuma an samu akasin haka. A wasan farko a cikin rukuni Sweden ta doke Tunisia da ci 5-1, sakamakon da ya girgiza magoya baya da jami'an tawagar ƙwallon ƙasar.

Washe gari ranar 16 ga watan Yuni, 2026, aka sallame shi daga aikin.

Masu sharhin tamaula sun ce korar Lamouchi ita ce mafi tsauri cikin dukkan matakan da aka ɗauka. A zahiri, bai samu damar gyara kuskurensa ba. An yanke masa hukunci ne bisa wasa ɗaya kacal. Wannan ya nuna yadda ƙasashe ke ɗaukar Kofin Duniya a matsayin gasa da ake dora burin nasara da kuma rashin uzuri.

Steve Clarke: Ya ajiye aikin bayan shekara bakwai yana horar da Scotland

Steve Clarke ya karɓi aikin kocin Scotland a ranar 20 ga Mayu, 2019, bayan da ya yi fice a ƙungiyar Kilmarnock. An ɗauke shi a matsayin mutumin da zai mayar da Scotland cikin manyan ƙasashen Turai a harkar taka leda.

Hakika ya yi abin a yaba masa. A tsawon shekara bakwai yana jan ragamar ƙasar, ya yi kokari wajen mayar da Scotland shiga babbar gasar tamaula ta duniya, bayan dogon lokaci na rashin halarta.

Sai dai kuma a wasannin cikin rukuni a gasar cin Kofin Duniya a 2026, Scotland ta kasa tsallakewa zagayen ƴan 32. Tawagar ta samu nasarar cin wasa ɗaya kacal, sannan ta sha kashi a hannun Morocco da Brazil. Bayan tabbatar da kasar ta kasa kaiwa zagaye na biyu ne, Clarke ya sanar da yin murabus a ranar 28 ga watan Yuni, 2026.

Sai dai wasu na cewa murabus din Clarke ba gazawa ba ce gaba ɗaya. Idan aka yi la'akari da inda ya tarar da Scotland da kuma matakin da ya kaita, za a iya cewa ya bar tarihi mai kyau. Sai dai matsalar Kofin Duniya ita ce ba a yi hangen rawar da ya taka a shekara shida baya ba, illa ana son samun sakamako mai kyau a dan ƙaramin lokaci.

Hong Myung-bo: Ƙyaftin ɗin da ya kasa bajinta a fannin horar da kasarsa

Hong Myung-bo ya zama kocin Koriya ta Kudu a ranar 8 ga watan Yuli, 2024 bayan da ya maye gurbin Jurgen Klinsmann. Lokacin da aka naɗa shi aikin, ana kallonsa a matsayin mutum mafi dacewa saboda matsayinsa na tsohon kyaftin ɗin da ya kai Koriya wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya a 2002.

An ba shi aikin gina tawaga mai cike da taurari ƴan ƙwallo irin su Son Heung-min da Kim Min-jae. An kuma sa ran Koriya za ta kai akalla zagayen kwata fainal.

Sai dai abubuwa sun lalace sun kasa tafiya yadda aka tsara. Tawagar ta yi nasara kan Jamhuriyar Czech a fafatawar cikin rukuni, amma ta sha kashi a hannun Mexico da Afirka ta Kudi. Bayan da aka tabbatar da kasar ba ta samu kai wa ko da zagaye na biyu ba, Hong ya yi murabus a ranar 29 ga watan Yuni, 2026.

Ya kuma ɗauki alhakin gazawar tawagar a kansa. Wannan shi ne jagoranci. Duk da haka, tambayar da ya kamata a yi ita ce ko matsalar ta Hong ce kawai ko kuma daga tsarin gudanar da harkokin ƙwallon kafar Koriya baki ɗaya ce?.

Miroslav Koubek: Kocin da aka ɗauka domin ceto tawagar Jamhuriyar Czech

A ranar 19 ga watan Disamba, 2025 ne Jamhuriyar Czech ta ba Miroslav Koubek aikin jagorantar tawagar ƙasar. An kawo shi ne a matsayin wanda zai ceto tawagar bayan korar Ivan Hasek.

Duk da shekarunsa 74, Koubek ya yi abin da ake buƙata a lokacin wasannin neman tikitin shiga gasar. Ya taimaka wajen kai Czech zuwa Kofin Duniya bayan dogon lokaci rabon da ta halarci wasannin.

Amma a gasar kanta da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico, Czech ta kasa samun nasara koda a wasa ɗaya daga ukun da ta yi a cikin rukuni, balle a sa ran za ta kai mataki na biyu na tawaga 32. Kasra ta samu maki daya kawai daga wasa uku. Saboda haka, Koubek ya yi murabus a ranar 29 ga watan Yuni, 2026 kuma hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ta amince da hakan.

Masu sharhi na ganin Koubek ya karɓi aikin da ya fi ƙarfin sa. Domin kai tawaga zuwa Kofin Duniya abu ne mai wahala, amma sai da ya kai Czech filin da'ga', kuma dalilin da ya sa ya haƙura da aikin shi ne kasa taka rawar gani a wasa uku kacal.

Marcelo Bielsa: Ɗan Dabarar Da Ya Gaza A Uruguay

Marcelo Bielsa ya fara aikinsa da Uruguay a ranar 15 ga Mayu, 2023. Lokacin da aka naɗa shi, an yi farin ciki ƙwarai saboda sunansa na ɗaya daga cikin manyan masu fasaha da gogewa a harkar horarwa a dunuya.

Bielsa mutum ne da ya shahara wajen canza yanayin tawagogi. Ya taɓa horar da Argentina da Chile da Leeds United cikin salon da ya sa ya yi suna a duniya a fannin horar da tamaula.

Sai dai Uruguay ta shiga Kofin Duniya da babban buri cewa za ta taka rawar da ba ta taba yi ba, amma sai ta kasa tsallake matakin rukuni. Sakamakon rashin nasara a hannun Sifaniya da kuma rashin samun sakamakon da ake bukata a sauran wasannin cikin rukuni, Bielsa ya sanar da murabus dinsa a ranar 30 ga watan Yuni, 2026.

Ya bayyana cewa yadda ya tafiyar da ƴan wasan da horar da su bai wadatar ba. Wannan furuci yana nuna irin mutuncin da Bielsa yake da shi, domin bai yi ƙoƙarin ɗora laifi kan kowa ba.

Masana harkokin tamaula sun ce Bielsa ya kasance ɗaya daga cikin kociyoyin da suka zo gasar da burin yin wani abu babba. To sai dai hakan bai samu ba duk da ƙwarewarsa da gogewarsa. Wannan ne ma ya sa Kofin Duniya ke da ban tsoro ga masu horarwa.

Ronald Koeman: Karo na biyu da ya kasa kai Netherlands matakin da take bukata

Ronald Koeman ya koma horar da Netherlands a karo na biyu a watan Janairu 2023 bayan da ya taɓa riƙe wannan mukamin tsakanin 2018 zuwa 2020.

An yi imanin cewa gogewarsa za ta taimaka wa Netherland wajen sake fafutukar lashe babban kofin. Tawagar ta yi rawar gani a wasu matakai kafin gasar nan ta kofin duniya.

Sai dai mafarkin ya kare ne bayan da Morocco ta fitar da Netherlands daga zagayen ƴan tawaga 32 a bugun fenariti. Washe gari, ranar 30 ga watan Yuni, 2026, Koeman ya sanar da cewa ba zai ci gaba da aiki ba, idan yarjejeniyarsa ta kare tsakaninsa da hukumar kwallon kafar kasar.

Ya bayyana cewa yana son ba iyalansa lokaci, amma ya kuma amince cewa sakamakon gasar bai kai inda ake fata ba.

Masu sharhi na ganin cewar Koeman ya fahimci cewa lokaci ya yi da zai yi gefe ya bai wa wasu dama. Wani lokaci babban koci ba lallai sai ya jira an kore shi ba; yana iya gane lokacin da ya kamata ya ajiye aikin.

Sebastián Beccacece: Kociyan da ya ajiye aikin ana girmama shi

Sebastián Beccacece ya karɓi aikin kociyan, Ecuador a ranar 1 ga watan Agusta, 2024. Babban burin da aka ba shi ya haɗa da ya kai ƙasar zuwa Kofin Duniya, kuma ya cimma wannan buri cikin nasara.

A gasarta 2026, Ecuador ta ba mutane mamaki ta hanyar kaiwa zagayen fitar da gwani. Wannan ya sa mutane suka fara kallon Beccacece a matsayin ɗaya daga cikin fitattun matasan kociyoyi a wasannin da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.

Sai dai Mexico ta kawo ƙarshen mafarkin Ecuador da doke ta 2-0. Bayan wasan, a ranar 30 ga watan Yuni, 2026, Beccacece ya sanar da cewa wa'adinsa ya zo ƙarshe kuma zai bar mukaminsa.

Ba kamar wasu kociyoyin ba, ba a kore shi ba kuma bai bar aiki cikin rigima ba. Ya yi bankwana cikin mutunci, yana gode wa wadanda suka bashi aikin ta tawagar da kuma magoya baya.

Ko da akwai karin kociyoyin da za a kora ko kuma su ajiye aikin nan gaba?

Idan aka duba waɗannan kociyoyi bakwai, za a ga cewa kowannensu yana da dalilinsa. Wasu sun yi aiki na shekara bakwai, wasu kuma watanni shida kacal. Wasu an kore su saboda wasa ɗaya, wasu kuma sun yi murabus bayan daɗewa a tawagar.

Shi dai aiki horas da tawaga a gasar Kofin Duniya ya fi kowane aiki girman suna. A wannan mataki, tarihin da ka gina a baya da kuma duk kwazon da ka yi ba zai hana a koreka ba, illa kawai ka samu sakamakon da ake bukata.

Wannan shi ne dalilin da ya sa ake cewa Kofin Duniya ba kawai gasa ce ta ƴan wasa ba; ita ce mafi girman da take yanke makomar mai horarwa nan take.

Yayin da gasar ke ci gaba, akwai yiwuwar jerin kociyoyin da za su rasa aikinsu ya ƙaru. Domin a duniyar ƙwallon ƙafa ta zamani, babban bambanci tsakanin jarumi da wanda ya gaza, banbancin minti 90 ne kacal tsakani.