Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
KAI TSAYE, Gasar kofin duniya 2026: Za a yi bugun fenariti Australia 1-1 Masar
Takaitaccen Bayanin Wasa
Key Events
Australiya
- Mohamed HanyOwn Goal 55 minutes
Masar
- Emam AshourGoal 13 minutes
Taƙaitattu
- Wannan ne karo na farko da Masar ta haura wasannin cikin rukuni a gasar kofin duniya a tarihinta
- Duk wadda ta yi nasara tsakanin Australia da Masar za ta kara da wadda ta kai zagayen gaba a wasan Argentina ko Cape Verde
- Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
- Nagelsmann ya ajiye aikin kociyan Jamus, bayan kasa yin abin kirki a gasar kofin duniya ta 2026
- Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook
- Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu tare da taimakon A1
, Penalties - Australia v Egypt
Kyaftin din Australia Harry Souttar ya dauki na farko ya buga ta yi sama sosai
, Australia 1-1 Masar
Australia ce za ta fara bugawa
An kammala wasan sai bugun fenariti, Australia 1-1 Masar
Za a fara da mutum biyar-biyar daga nan muga abin da zai faru.
, Australia 1-1 Masar
Australia ta yi bugun tazara daga gidan Masar, amma an yi karo tsakanin yan wasa biyu kowanne yana kwance. Alkalin wasa ya busa.
Ausralia ta yi canjin mai tsaron raga, Australia 1-1 Egypt
An saka dogon gola mai suna Mat Ryan ya maye gurbin Patrick Beach.
Kowa ya san me hakan yake nufi cewar Ryan ya gwanance a tare fenariti.
Bari mu gani an yi karin minti daya.
, Australia 1-1 Masar
An buga kwallon ba ta yi kyau ba, domin ta bugi masu tsaron baya ta je jifa, kenan kwallon ya bugi katanga.
, Australia 1-1 Masar
Hany na Masar ya yi keta an samu bugun tazara daga irin wajen da Australia ta farke kwallonta.
, Australia 1-1 Masar
, Australia 1-1 Masar
Kamar wani karin karfi ne ya karu a tawagar Masar sai kokarin cin kwallo take, ko tana tunanin bugun fenariti tana da matsala, gwara ta kammala wasan tun yanzu.
, Australia 1-1 Masar
Salah ne ya buga kwana ta shiga cikin gidan Australia, amma yan baya sun fitar da ita.
, Australia 1-1 Masar
Sai yanzu ne Masara ta buga kwallo mai kyau ta yi bani in baka har ta kai ga Ashour ya samu dama ya buga a cikin gidan Australia, amma ta taba masu tsaron baya ta yi waje zuwa kwana.
, Australia 1-1 Masar
Bangarorin biyu suna da ƙarin canji guda ɗaya. Yadda za a yi amfani da shi watakila idan ta kai ga bugun fenariti shi ne abin ji. Za a iya sa mai tsaron raga da ake ganin yana da gogewa a fannin tare fenariti ko kuma wani dan wasan da ya kware a cin bugun daga kai sai mai tsaron raga.
, Australia 1-1 Masar
An koma karin lokaci na biyu da za a buga minti 15, idan babu tawagar da ta zura kwallo a raga daga nan sai bugun fenariti da ake kira sai mai rabo.
, Australia 1-1 Masar
An kammala minti 15 za a dan huta sannan a koma fili a karasa minti 15 nan gaba.
, Australia 1-1 Egypt
Kawo yanzu yan wasa sun ci gida sau 13 a gasar cin kofin duniya ta 2026, Ita ce kan gaba da aka yi haka a tarihi. Koda yake da sauran wasanni a gaba, watakila su fi haka, domin za a kai ga zagayen yan 16 da kwata fainal da daf da karshe da wasan karshe.
Dan wasan Masar, Mohamed Hany ya zama na biyu da ya ci gida a wasa biyu a gasar kofin duniya guda, bayan dan Bulgaria, Ivan Vutsov a gasar 1966.
, Australia 1-1 Masar
Wannan shi ne karo na hudu a zagayen yan 32 da aka yi karin lokaci a gasar cin kofin duniya ta 2026.
Biyu an kai ga bugun fenariti, yayin da wasan Belgium da Senegal aka kammala shi daf a tashi inda Belgium ta kai zagayen yan 16.
Shin yaya wannan wasan zai kaya?
Katin gargadi, Australia 1-1 Egypt
An bai wa matakin kociya, Ibrahim Hassan katin gargadi na Masar saboda ya yi korafi ga alkalin wasa.
Kadan ya rage Salah ya ci kwallo, Australia 1-1 Egypt
Damar farko da Salah ya samu a wasan nan.
Kwallo ce a cikin gidan Australia daga gefen hagu ya yi kokarin bugata, amma ta yi fadi.
Shi kansa ya san cewar ya kamata kokarinsa ya fi haka.
An koma wasan, Australia 1-1 Masar
Za a fara yin minti 15 daga nan a juya zango na biyu a kara wani minti 15 daga nan a je bugun fenariti idan babu wadda ta kara cin kwallo.

