Me ya sa Iran ta amince Qalibaf ya jagoranci duk wani batu da ya shafi China?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Saeed Jafari
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
A lokacin da Mohammad Baqer Qalibaf ya samu ƙuri'u kusan miliyan uku kacal a zaɓen shugaban ƙasa a baya kuma ya kasa kai wa zagaye na biyu, da dama sun bayyana hakan a matsayin kawo ƙarshen mafarkin da ya daɗe na zama shugaban ƙasa.
Ɗansiyasar, wanda ya shafe kusan shekaru 20 yana ƙoƙarin zama shugaban ƙasa, da alama an wuce da yayinsa
To sai dai abubuwan da suka faru a Iran a cikin 'yan watannin nan, musamman yaƙi da rikicin da ke tsakanin Tehran da Washington, sun sa ya zama babban ɗan gaban goshi.
Qalibaf ya jagoranci tawagar Iran wajen tattaunawa da mataimakin shugaban Amurka, kuma shi ne kan gaba a tarukan tsaro da siyasa masu muhimmanci da aka yi, sannan kuma an naɗa shi a matsayin "Wakilin Iran na musamman a China".
Me ya sa aka amince wa Qalibaf?
An ɗauki wannan matakin ne a yayin da kasar China ta zama babbar abokiyar Iran wajen hulɗar kasuwanci a cikin 'yan shekarun nan, kuma tana taka rawa wajen batutuwa da suka shafi yaƙinta, Mashigar Hormuz da kuma tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.
Masu sharhi na ganin wannan naɗin nasa ba wai iya a baki ba ne, yana nuna yadda Iran ke ɗaukar wasu matakai masu muhimmanci game da harkokinta na ƙasa da ƙasa, musamman a irin wannan lokaci na tsamin dangantaka a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wasu kuma na ganin Qalibaf na taka muhimmiyar rawa wajen yanke wasu hukunce-hukunce da tattaunawar masu faɗa a ji a wannan yanayi na yaƙi.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa China ke da muhimmanci a yanzu?
Bayan ficewar Amurka daga JCPOA a shekarar 2018, alkiblar Iran ta karkata zuwa Gabas sosai. Sannu a hankali kasar China ta zama babbar abokiyar hada-hadar tattalin arziki ga Tehran; ƙasar da take sayen mafi yawan man fetur na Iran a tsawon shekarun da aka sanya mata takunkumi, inda ya zama ɗaya daga cikin hanyoyin da suka rage mata na samun kuɗaɗen shiga.
Yaƙin da aka fafata a baya-bayan nan ya sa matsayin China ga Iran ya wuce na kasuwanci kawai, domin baya ga zamanta babbar ƙasar da ke sayen manta, masu sharhi na ganin tana taka muhimmiyar rawa wajen tattaunawa game da yaƙin Iran da Amurka.
Yadda China ta shiga tsakanin yarjejeniyar Iran da Saudiyya da ci gaba da alaƙa tsakanin ƙasashen biyu ya sa ake ganin za ta iya irin hakan a wasu rikice-rikicen na wasu yankin.
Sai dai duk da haka, wasu na ganin China ba za ta taɓa bari zumuncinta da Iran ya lalace ba, kuma ba za ta so a ci gaba rikici a yankin Gulf ba, yankin da China ta dogara sosai a kai ta fannin makamashinta.
Wannan ya sa ake ganin Iran ɗin na son inganta alaƙarta da China fiye da ta kasuwanci.
Ina ma'aikatar harkokin waje take?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Naɗin kakakin majalisar a wannan sabon muƙamin zai iya zama kamar rage ƙarfin ikon ma'aikatar harkokin wajen Iran da kuma muhimman bayanai da suka shafi soji da harkokin tsaro.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta cika barin wasu tsare-tsare da suka shafi hulɗar ƙasashen waje kacokan ga ma'aikatar harkokin waje ba. Kama daga maganar nukiliya da tsaron yanki, rundunar juyin juya hali da majalisar ƙoli na taka muhimmiyar rawa wajen yanke hukunci.
Wasu masu sharhi na ganin hulɗar China ta wuce ta diflomasiyya. A irin yanayin da ake ciki na yaƙi da takunkumai, ga batun Mashigar Hormuz da kuma alaƙarta da Amurka, ya sa ake ganin ta ga dacewar miƙa wannan ragama zuwa ga wani mutum da ke da kusanci da hukumomin tsaro da kuma ƙarfin faɗa a ji a siyasance.
Qalibaf tsohon kwamandan dakarun juyin juya halin ne, kuma yana da kyakkyawar alaƙa da rundunar. Wannan ya sa ya fi dacewa da kula da batun da ya shafi ɓangarorin biyu; mutumin da zai iya tattaunawa da hukumomin soji da kuma ƴan siyasa da batun da ya shafi tattalin arziki da harkokin ƙasashen waje.

Asalin hoton, Getty Images
Qalibaf: Magajin Larijani a kaikaice
Wani abu mai muhimmanci shi ne yadda ayyukan sabon matsayin Qalibaf ke kamanceceniya da matsayin da Ali Larijani ya taɓa riƙewa.
A shekarun baya, ana ganin Larijani a matsayin mutumin da aka fi amincewa da shi a gwamnati, tun daga maganar nukiliya da kuma alaƙar Iran da China da Rasha; ɗansiyasa ne da ke sanya ido kan batutuwan da suka shafi tsaro da siyasa da harkar diflomasiyya.
A yanzu masana na ganin Qalibaf na gudanar da irin waɗannan ayyuka, inda ake ganin ma yana taka rawa a wasu batutuwan bayan wanda ake gani.
Yana da ta cewa kan batun da ya shafi yaƙi da kuma kulle mashigar ruwa, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani ga shi yanzu kuma shi ne babban jami'in da ke hulɗa kan abubuwan da suka shafi China. Wannan ya sa ake ganin an samar da wani tsarin shugabanci da zai ɗinke bakin zaren duk wani ƙalubale da za a iya samu a Iran.
Me China take so?
Duka waɗannan na faruwa ne a yayin da ake ɗiga ayar tambayar shin me China take nema daga Iran, kuma wane matakai za ta iya kaiwa domin goyon bayan Tehran da kuma fuskantar ƙalubalen da zai shafi alaƙarsu.
Take-taken China na nuna cewa ba ta son rikicin Gabas ta Tsakiya ya haifar da matsala ga harkar makamashi a duniya, saboda China ita ce babbar ƙasar da ke siyan manta da kuma wani sashe na makamashinta da ke bi ta yankin Gulf da Mashigar Hormuz.
Sai dai ga dukkan alamu, China ba ta shirya shiga wani rikici da Amurka kan Iran ba
Wannan ya sa masu sharhi suke ganin China na son daidaita komai yadda ya dace da kuma ci gaba da alaƙa tsakaninsu Iran da Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Shin wannan dama ce ko kuma rashin ƴanci?
Yayin da wasu a Iran ke sukar yawan dogaro kan Gabashin Duniya da China da Rasha, musamman bayan janyewar Amurka da JCPOA da kuma yaƙe-yaƙen da aka yi a baya-bayan nan, ya kamata a yi tsarin da zai rage dogaro kan wata ƙasa musamman kan tattalin arziki da hulɗar ƙasa da ƙasa.
Wasu masu sharhi na gargaɗin cewa yawan dogaro kan China zai iya zame mata matsala a nan gaba. Suna ganin Beijing na yanke hukunci na kan abin da take da ra'ayi kawai ba tare da duba wasu abubuwan da suka shafi siyasa da kuma alaƙarsu da Jamhuriyar Musuluncin ba.
Saboda wannan dalilin, wasu masu sharhi ke ganin idan rikicin Iran ya zama ɗaya daga cikin manyan batutuwan da za a hau teburin tattaunawa da su, Tehran za ta iya shiga tsaka mai wuya kuma ba lallai ta iya daidaita lamuran ba.











