Cibiyar nukiliyar Iran ta sirri da Trump ke barazanar kai wa hari

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Journalist Reza Sabeti, with additional reporting from BBC Verify
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
A barazanar da ya yi ta kwanan nan, Donald Trump ya bayyana wani waje da ba a sani ba sosai idan aka kwatanta da yadda sauran cibiyoyin nukiliyar ƙasar suka yi fice.
Da aka tambaye shi ko Iran ta mayar a kayayyakin sana'anta makamin nukiliyarta zuwa "Tsaunin Pickaxe" sai shugaban ƙasar ya yi alƙawarin cewa Amurka za ta ƙaddamar da hare-hare "da ƙarfin gaske" sannan ya ƙara da cewa, "wataƙila nan kusa ne."
Iran ta tanadi cibiyar, wadda har yanzu ake cigaba da ginawa domin maye gurbin manyan cibiyoyinta a Natanz da Isfahan.
Girmansa da kuma yanayin da ak tsara shi da kuma hana izini ga hukumomin duniya su je dubiya ne suka sa ake ganin tsaunin na da muhimmanci ga Iran.
A ranar 2 ga watan Yulin 2020, a ji ƙara a kusa da cibiyar Natanz, lamarin da Iran ta bayyana da "yunƙurin zagon-ƙasa," sannan ta zargi Isra'ila, duk da cewa ba ta taɓa amincewa da hannu a lamarin ba.
Watanni daga baya sai Ali Akbar Salehi, shugaban ƙungiyar nukiliya ta Iran ya bayyana shirin maye gurbin tsohuwar cibiyar makamashin ƙasar da "sabuwa ta zamani mai girma,"

Asalin hoton, Institute for Science and International Security
Tsaunin na da bisa sosai, ta yadda za a iy samun gine-gine da dama a ƙarƙahinsa, kamar yadda cibiyar masana ta Institute for Science and International Security (ISIS) da ke Amurka ta bayyana.
Sai dai zai yi wahalar gaske a iya taskance asalin girma da yanayin abubuwan da ke ƙunshe a cikin tsaunin.
Iran ta ƙara tsananta tsaro a cibiyar tun bayan yaƙin kwana 12 da Isra'ila a watan Yunin 2025.
A watan Fabrailun 2026, hotunan tauraron ɗan'adam da cibiyar ISIS ta ɗauka sun nuna akwai hanyoyin shiga ƙasan tsaunin na ƙarƙashin ƙasa, sannan wani hoton ya nuna wani sabon kankare da aka yi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma kuma nazarin ISIS ya bayyaa cewa cibiyar ba ta aiki sosai.
Hotuna da aka ɗauka a ranar 9 ga Yulin 2026 sun nuna ƙofar shiga cibiyar a buɗe suke, kuma fayau.
A ranar Talata 22 ga Yuli, ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce ba a gudanar da wani aikin nukiliya a cibiyar Pickaxe.
ISIS ta ƙiyasta cewa cibiyar na da girma, kuma za ta iya ɗaukar aikace-aikacen sana'anta nukiliya.
ISIS ta bankaɗo abubuwan da ta ce hujjoji ne da suka alamta aikin sana'anta uranium da ake amfani da shi wajen haɗa uranium.
Babban ƙalubalen tantance yanayin cibiyar a yanzu shi ne hana hukumar makamashi ziyarar dubiya a cibiyar a yanzu, sannan Iran ba ta yi bayanin ba.
A watan Maris, darakta hukumar Rafael Grossi ya ce akwai buƙatar masu dubiya su samu shiga domin ganin yadda take da abubuwan da ke gudana a ciki.
Ita kuma Iran babu buƙatar zuwan hukumar har sai an kai kayayyakin nukiliya, inda shi kuma Grossi ya sake mayar da martani a zantawarsa a BBC cewa, "tun da farko ya kamata a ce muna zuwa."
Binciken hukumar na ƙarshe ya nuna cewa Iran na da kilogram 440.9 na uranium da aka inganta zuwa kashi 60, wanda saura aiki kaɗan ya rage ya kai kashi 90 na zama makami. Kuma a haka lamarin yake har zuwa ranar 13 ga Yunin 2025, ranar da aka fara yaƙin kwana 12 na Iran da Isra'ila.
Yanzu dai Tsaunin Pickaxe ta zama cibiyar da ake hasashen ana ayyukan nukiliya, amma babu tabbaci daga hukumar.
Amurka ta ƙaddamar da hare-hare a cibiyar Fordow da makamanin GBU-57 da bam ɗin 13.6 da zai iya tarwatsa kankare mai girma.
Amma nasarar waɗannan hare-haren na ta'allaƙa ne da ƙarfin dutse da kankare da kuma daidai wajen da aka ƙaddamar da harin.
Wannan harin ya biyo bayan shekaru da Amurka da Isra'ila suka yi suna tattara bayanan sirri a kan cibiyar ta Fordow.
Idan har akwai kayayyakin makamin nukiliya da aka adana a ƙarƙashin cibiyar Pickaxe, babu tabbas ko hare-hare ta sama za su iya tarwatsa su.












