Matsaloli 5 da za ku iya fuskanta idan kuna cin abinci daf da kwanciya barci

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Cin abinci daf da kwanciya barci da dare wani abu ne da mutane da dama suka saba yi, musamman bayan kammala harkokin yau da kullum ko dawowa gida a makare.

Ga wasu, hanya ce ta rage yunwar da suke ji kafin su kwanta, yayin da wasu kuma ba sa ganin wata illa wajen yin hakan.

Sai dai masana lafiya sun ce lokacin cin abinci na iya taka muhimmiyar rawa wajen lafiyar jiki, domin abincin da aka ci kusa da lokacin barci na iya shafar yadda jiki ke narkar da shi da kuma ingancin hutun da mutum zai samu kamar yadda Dr. Farouk Mutsapha, wani likita mai kula da lafiyar jama'a a Abuja ya bayyana wa BBC.

Likitan ya ce cin abinci mai yawa ko mai nauyi kafin kwanciya na iya tilasta wa jiki ci gaba da aiki wajen narkar da abinci a lokacin da ya kamata ya kasance yana samun hutu da kuma haifar da matsaloli daban-daban, musamman idan mutum ya mayar da cin abinci daf da lokacin barci ɗabi'a.

Ga wasu daga cikin matsalolin da mutum zai iya fuskanta idan ya ci gaba da cin abinci kusa da lokacin kwanciya barci in ji Likitan.

Ƙara ƙiba saboda taruwar kitse a jiki

Likitan ya ce ɗaya daga cikin matsalolin da ake danganta wa da cin abinci da dare ko daf da kwanciya barci shi ne yiwuwar ƙara ƙiba ko nauyin jiki.

"Lokacin da mutum ya ci abinci mai yawan maiƙo sannan ya kwanta ba tare da ya motsa jiki ba, jiki na iya ajiye wani ɓangare na wannan maiƙon a matsayin kitse."

Likitan ya ce soyayyen abinci da abinci mai yawan maiƙo da abubuwan sha masu zaƙi na iya ƙara wannan matsalar idan ana cin su akai-akai kafin barci.

Jin zafi a ƙirji

Dr Farouk ya ce wata matsalar kuma da aka fi samu idan mutum ya ci abinci ya kwanta nan take shi ne zafin zuciya kamar maiƙo mai yaji na dawowa mutum zuwa maƙogaro.

"Wannan matsala na iya sa mutum ya ji wani zafi a ƙirjinsa ko kuma kaikayi a makogaro, musamman idan ya kwanta a shimfiɗe."

Likitan ya ba da shawarar a bar tazara tsakanin lokacin cin abinci da lokacin kwanciya domin ba wa ciki damar fara narkar da abinci.

Rashin samun ingantaccen barci

Barci mai kyau yana da matuƙar muhimmanci ga lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa in ji likitan.

Amma cin abinci mai nauyi kafin barci na iya hana mutum samun cikakken hutu saboda tsarin narkewar abinci yana ci gaba da aiki.

Wasu mutane za su kasance suna yawan jujjuyawa a gado ko suna farkawa akai-akai ko jin nauyi a jiki idan sun ci abinci daf da kwanciya.

Ƙara haɗarin kamuwa da matsalolin lafiya

Likitan ya ce cin abinci da dare musamman abinci mai yawan sukari ko maiƙo masu yawa na iya shafar yadda jiki ke sarrafa sukari a cikin jini.

"Ga mutanen da ke da matsalar sarrafa insulin ko waɗanda ke cikin haɗarin kamuwa da ciwon suga, yawan cin abinci daf da barci na iya zama wani abu da ke ƙara matsalar.

Matsalolin narkewar abinci

Baya ga jin zafi a ƙirji, cin abinci daf da kwanciya na iya haifar da wasu matsaloli kamar kumburin ciki, yawan iska a ciki, tashin zuciya ko jin nauyi a ciki.

Dalilin hakan shi ne jiki bai samu isasshen lokaci ba kafin mutum ya kwanta, wanda hakan zai iya rage jin daɗin barci.

Idan mutum ya ji yunwa kafin barci fa?
..

Asalin hoton, Getty Images

Dr. Farouk ya ce idan yunwar ta taso kafin kwanciya, mutum zai iya cin ɗan ƙaramin abu mai sauƙin narkewa kamar 'ya'yan itatuwa ko yoghurt mara sukari ko kuma ɗan ƙaramin kaso na abinci mai lafiya maimakon cin abinci mai nauyi kuma mai yawa.

Dangane kuma da tsawon lokacin da mutum ya kamata ya ci abinci kafin barci, likitan ya ƙara da cewa "mafi dacewa shi ne mutum ya bar aƙalla awa biyu zuwa uku tsakanin cin abinci da lokacin kwanciya."

Wannan in ji likitan na ba jiki damar fara narkar da abincin kafin ya shiga yanayin barci.

Likitan ya kuma lissafo jerin abincin da mutane za su iya ci idan yunwa ta taso musu kafin kwanciya kamar haka;

  • 'Ya'yan itatuwa: 'Ya'yan itatuwa kamar gwanda, ayaba, pear, tuffa ko berries na iya zama zaɓi mai kyau idan yunwa ta taso kafin kwanciya barci.
  • Yogot mara yawan sukari: Yogot na ɗauke da sinadarin protein da calcium, waɗanda ke taimakawa wajen gina jiki da kuma rage yunwa kafin barci.
  • Kayan lambu: Kokwamba, karas ko latas na daga cikin kayan lambun da za a iya ci da dare saboda suna da sauƙin narkewa kuma ba sa nauyaya ciki.
  • Dafaffen ƙwai: Ƙwai na ɗaya daga cikin abincin da ke cike da protein. Dafaffen ƙwai ɗaya ko biyu na iya rage yunwa ba tare da ƙarawa ciki nauyi ba.
  • Oats: Oats na ɗauke da fiber, wanda ke taimakawa wajen cika ciki na tsawon lokaci. Ana iya haɗa shi da madara ko yogot.

Nau'in abincin da ya kamata a gujewa da daddare

Likitan ya ce abincin da ya kamata mutane su gujewa da dare ko kafin barci sun haɗa da

  • Abinci mai kitse sosai
  • Abinci mai yaji
  • Abinci mai nauyi
  • Abubuwan sha masu caffaine
  • Kayan zaki.

Likitan ya ce waɗannan abubuwa na iya haddasa jin zafi a ƙirji ko kuma su hana mutum samun isasshen barci.