Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya jawo aka sanya dokar hana fita a wasu yankunan Filato
Gwamnatin jihar Filato da ke Arewa ta tsakiyar Najeriya, ta sanya dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari a ƙananan hukumomi uku na jihar, biyo bayan sake barkewar tashin hankali.
Ƙananan hukumomin da abin ya shafa su ne Barkin-Ladi, da Bokkos da Mangu.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce daukar wannan matakin ya zama dole don shawo kan tashe-tashen hankulan da ake samu tsakanin fulani makiyaya da kuma manoma 'yan kabilar Birom.
Dokar hana fitar kamar yadda sanarwar ta ce, zata fara aiki ne daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe a wadannan yankuna.
Gwamnatin jihar ta Filato ta sanya dokar ne bayan da aka kashe wani fasto a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa ziyara, hakan ne ya fusata 'yan kabilar Birom da ma wasu wasu kabilu da ke yankunan anan aka fara daukar matakin ramuwar gayya.
Wani mazaunin Barikin Ladi, wato daya daga cikin yankunan da wannan doka ta shafa, ya shaida wa BBC cewa, ana zargin fulani da aikata wannan ta'asa.
Mutumin ya ce, " A gaskiya abubuwan da ke faruwa a wadannan kananan hukumi ya tsananta, don haka muna kira da mahukunta da a dauki matakin kawo karshen irin wadannan tashe – tashen hankulan."
" A yanzu mu mutanen wadannan yankuna da aka sanyawa dokar hana fita muna cikin tsoro ga damuwa sannan kuma gashi an killace mu waje guda tun da an hana mu fita sai dai mu zauna a gida." In ji shi.
Wannan matsala ta rikicin kabilanci a jihar Filato dai matsala ce mai dogon tarihi da aka jima ana neman yadda za a shawo kanta.
A shekarun baya an sha samun rikici mai nasaba da ƙabilanci da kuma addini a garin na Jos, babban birnin jihar Filato.
Duk da ƙoƙarin da hukumomi suke yi wajen samar da zaman lafiya, a lokuta daban-daban an sha samun rikice-rikice da ke haifar da asara ɗimbin rayuka.
Amma da alama dai lamarin ya neman ya gagari kundila, saboda har yanzu ana ci gaba da samun fuskantarta.
Hare-hare a arewa ta tsakiyar Najeriya
Maris 2025 – A ƙarshe-ƙarshen watan Maris an kashe kimanin mutum 52 a wani harin da aka kai a ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato.
Lamarin ya sanya mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu ya kai ziyara yankin, inda ya yi alƙawarin cewa gwamnati za ta tabbatar an kawo ƙarshen matsalar.
Sai dai duk da haka an ci gaba da samun hare-hare a jihar.
Afrilu 2025 – An kai wani hari a ƙaramar hukumar Bassa da ke jihar Filato, kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar wa BBC.
An kai harin ne da asubahin ranar Litinin 14 ga watan Afrilu.
Gwamnatin jihar ta ce ta ɗauki ƴan jarida zuwa yankin domin ganin abin da ya faru. Wani jami'in gwamnatin jihar Yakubu Ventim ya ce ''kimanin mutum 38 zuwa 50 ne aka kashe a ƙauyen.
''Sun kai hari ne na ba-zata, inda suka kashe akasari mata da yara".
Mayu 2025 – An kashe aƙalla mutum 10 sanadiyyar rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Riyom da ke jihar Filato.
Kafofin yaɗa labarai sun ce lamarin ya faro ne daga lalata gonaki da kisan shanu, inda daga baya kuma abin ya koma rikici tsakanin ƙabilun Berom da Fulani.
Bayanin dakarun rundunar Safe Haven y ace rikicin y afara ne daga ranar Litinin 12 ga watan Mayun 2025, sa'ilin da aka zargi wasu matasa da sacewa da kashe shanun da suka shiga wata gona a ƙauyen Dayan da ke ƙaramar hukumar Riyom.
An yi zargin cewa a matakin ramuwar gayya, makiyaya sun kai hari kan ƙauyen Danchindo da yammacin ranar 13 ga watan Mayu inda suka kashe kimanin mutum hudu.