Wani sabon rahoto ya yi zargin cewa wasu manyan ‘yan siyasar
Najeriya da dama sun karkatar da ɗaruruwan miliyoyin daloli daga kuɗin gwamnati a cikin shekaru 30 da suka gabata wajen sayen kadarori a Amurka.
Binciken da Cibiyar kare masu kwarmata bayanai a Afirka da gamayyar ƙungiyar yaƙi da rashawa suka gudanar ya gano wasu manyan jami'an gwamnati na yanzu da na baya 61 da ke da alaƙa da wasu kadarori 284 a Amurka da darajarsu ta kai kusan naira biliyan 370.
Sanarwar ta kuma ce 39 daga cikinsu an taɓa zargin su, wasu kuma an gurfanar da su a kotu, wasu ma an yanke musu hukunci kan cin hanci da rashawa.
Rahoton mai taken 'Dirty Deeds - Yadda manyan jami'an gwamnatin Najeriya suka sayi kadarori a Amurka', ya yi nazari kan kadarorin da aka saya tun daga 1991 tare da gano kadarori 152 da darajarsu ta kai kusan dala miliyan 177 da aka saya a lokacin da jami'an ke kan mulki, lokacin da rahoton ya ce suke da iko kan kuɗin gwamnati.
PPLAAF ta ce kusan kashi 81 na kadarorin an saye su ba tare
da wata bayyananniyar hanyar samar da kuɗin sayen ba, kamar rancen sayen gida.
Ƙungiyar ta bayyana hakan a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ka iya zama
alamun almundahana.
Sai dai rahoton bai tabbatar da cewa an sayi dukkan
kadarorin da kuɗaɗen sata ba, kuma ya buƙaci hukumomin Najeriya da Amurka su
gudanar da bincike don gano ta ina kuɗaɗen suka fito.
Babban Daraktan PPLAAF, Jimmy Kande, ya ce binciken ya
fallasa gazawar wasu jami’ai da kuma giɓin da ke bayar da damar zurarewar dukiyar jama’a da aka sata zuwa ƙasashen waje tare da
zuba ta a kadarori.
Jami'an da ke ɓangaren tsaro a Najeriya sune masu kaso mafi tsoka na kadarorin da rahoton ya gano.
Ƙasar na fama da matsalolin tsaro inda ake samun ƙaruwar garkuwa da mutane da matsalar ƴanbindiga da rikicin masu iƙirarin Jihadi cikin shekaru goma da suka gabata.
BBC ta tuntuɓi Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa domin jin ta bakinta kan bankaɗar da rahoton ya yi.